Kadarorin da suka jefa Akanta Janar a komar EFCC
Hukumar na zargin sa da karakatar da N80bn wajen sayen filaye da gidaje da sauran kadarori.
A yanzu da Akanta Janar na Najeirya Ahmed Idris ke tsare a hannun Hukumar Yaki Da Yi Wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta yi bisa zargin karkatar da Naira biliyan 80 daga lalitar gwamnati, mutane na ci gaba da fadin albarkacin bakinsu kan lamarin.
A ranar Litinin din makon jiya ne jami’an Hukumar EFCC suka kama Akanta Janar din a Kano bayan sun ce ya ki amsa gayyatar da hukumar ta yi masa a baya.
- DAGA LARABA: Jikoki A Hannun Kakanni: Tausayi Ko Cutarwa?
- Tsadar rayuwa ta kai matakin intaha a Jamus
Har zuwa wannan lokaci Babban Akantan Kasar yana hannun hukumar inda yake amsa tambayoyi a kan abin da ya shafi karkatar da kudin jama’a.
Hukumar na zargin sa da karakatar da kudaden wajen sayen filaye da gidaje da sauran kadarori.
EFCC ta yi zargin cewa babban jami’in ya mallaki manyan gine-gine a jiharsa ta haihuwa Kano da kuma biranen Legas da Abuja da Dubai da kuma Landan.
Daya daga cikin kadarorin da ake zargin mallakar Idris ne shi ne tsohon ginin rukunin kantunan zamani na Alkhlas da ke Unguwar Daneji wanda yanzu aka kara masa girma da wasu gidaje da ke makwabtaka da shi.
Bincike ya ce Babban Akantan ya mallaki kadarori da yawa a Kano inda yanzu yake kokarin mayar da su makarantu masu zaman kansu da kuma asibitoci.
Wani mazaunin Unguwar Daneji da ya nemi a boye sunansa ya shaida wa Aminiya cewa idan aka zo batun sayen fili a wannan yanki to koyaushe Akantan ne yake saya saboda shi ne mai yin gwaggwaban tayin da mai sayarwa ba zai iya juya baya ba.
Wasu majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa Idris ya mallaki wasu gidaje na miliyoyin Naira a Unguwar Gandu da ke Kano.
Haka Aminiya ta gano cewa iri gidajen da Babban Akantan ya mallaka na miliyoyin Naira a Unguwar Ladanai da ke Kano sun sa shakku a zukatan al’ummar jihar inda suke zargin halaccin kudin da yake da shi da kuma yadda yake kashe su.
Daya daga kadarorin da ake zargin Akanta Janar din ya mallaka shi ne kasuwar nan ta Gezawa Commodity and Edchange Market da ke garin Gezawa wacce aka kiyasta ta kai Naira biliyan hudu da rabi.
Tun a shekarar 2021 Hukumar Kula da Harkar Hannun Jari ta Kasa (SEC) ta ba kasuwar lasisin fara gudanarwa.
A ziyarar da Aminiya ta kai kasuwar ta samu labarin cewa an tsara kasuwar kashi uku inda a yanzu aka kammala kashi na farko da ya kunshi kadada takwas. Kuma tuni ka fara gudaanr da hada-hadar kasuwanci a kasuwar.
A wani lokaci an ce Idris ya taba cewa ya mallaki filin kasuwar ne ta hanyar gado daga bangaren mahaifiyarsa wacce ’yar garin Gezawa ce inda daga bisani ya sayi wasu filayen ya kara a kai.
Da farko an dauka kasuwar wani shiri ne na masu zaman kansu da irinta ce ta farko a Najeriya. Kuma an ce kasuwar ita ce mafi girma da ta kunshi komai ta hanyar saye da sayar da kayan amfanin gona kaitsaye tare da samar da wurin da za a gudanar da kasuwanci a fadin duniya ba tare da je ka ka dawo ba.
A shekarar 2020 lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin Kungiyar Dattawa ta Jihar Kano Akanta Janar din ya shaida musu cewa ya dauki tsawon lokaci tun a shekarar 2014 yake burin ya samar da kasuwar don kara bunkasa harkokin noma da kasuwanci a jihar.
Ya ce “Wannan shi ne wuri mafi girma da ya hada komai don fito da ainihin manufar dogaro da kai wajen canza alkiblar kaswuanci tare da samar da ci gaban tattalin arziki.”
Ra’ayoyin mutane
Wadansu ’yan Najeriya da suka yi magana a kafafen labarai da na sada zumunta na zamani sun nuna kaduwarsu kan yadda ake zargin dakataccen Babban Akantan da kwashe wadannan makudan kudi har Naira biliyan 80 daga lalaitar gwamnati.
Sun nuna damuwarsu game da yajin aikin da malaman jami’o’i na kasa da malaman kwalejojin ilimi wadanda ba su shiri da Babban Akantan saboda fito da sabon tsarin biyan albashi na IPPIS. Wani malami a tsangayar Koyar da Aikin Jarida a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, Malam Kabiru Danladi ya shaida wa Aminiya cewa mambobin Kungiyar Malaman Jami’o’in ba su yi mamakin jin wanann labarin ba domin dama tuni suka bankado shi.
Ya ce, “Watakila ’yan Najeriya su kadu, amma ban damu ba, domin mun dade da sanin hakan inda yake amfani da tsarin IPPIS yana kwashe kudin kasa wanda kuma tuni muka sanar wa al’umma.”
Shugaban Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), Farfesa Emmanuel Osodeke a tattaunawa da Aminiya ya ce baya ga batun tsarin IPPIS da malaman jami’a ke rigima a kansa, yanzu haka wadansu malaman suna bin albashin wata 8 zuwa 13.
Ya ce “Mun sha fadi cewa IPPIS cuta ce kawai. Mun kuma bayyana cewa ofishin Akanta Janar cuta ne inda suke amfani da tsarin IPPIS su juyar da akalar duk wata cutarsu ga ofishin Akanta Janar. Kuma ba za mu yarda ba, wannan ne matsayarmu. Zan iya gaya maka cewa a yanzu mambobinmu da yawa ba a biya su albashin wata 13, wadansu 9, wadansu 8. Mun fada wa gwamanti cewa tana amfani da IPPIS ne domin ta kara habaka harkar cin hanci.”
A ranar Larabar makon jiya Gwamantin Tarayya ta bakin Ministan Kudi, Hajiya Zainab Shamsuna Ahmed ta bayar da sanarwar dakatar da Akanta Janar din domin a samu damar gudanar da cikakaken bincike.
A cikin takardar da Ministar ta aike wa Babban Akantan ta gargade shi da kada ya je ofishinsa a kowane lokaci.
Ta kuma ce dakatarwar da aka yi wa Akanta Janar din tana bisa tsarin dokar aiki ta kasa.
“Bayan kama ka da jami’an EFCC suka yi kan zargin karkatar da kudin gwamnati. Ina rubuta wannan takarda don sanar da kai cewa an dakatar da kai daga aiki ba tare da biyan albashi ba. Kuma wannan dakatarwa ta fara daga ranar 18 ga Mayun, 2022.”
Tuni Hukumar EFCC ta samu amincewar kotu na ta ci gaba da tsare Akanta Janar din na wasu kwanaki don ci gaga da gudanar da bincike a kan lamarin.
Daga: Ibrahim Musa Giginyu da Lubabatu I. Garba, Kano da Idowu Isamotu, Abuja.