kaddamar da sabon filin wasa: Super Eagles ta kara da Sportlight a Katsina
A yammacin Talatar da ta wuce ne aka yi wasan kaddamar da filin wasa na Karkanda wanda gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna mai barin gado Barista Ibrahim Shehu Shema ta kammala aikin ginin filin wanda ya ci miliyoyin naira. Wasan kaddamar da filin wanda shi ne filin wasa na biyu a jihar, an gudanar […]
A yammacin Talatar da ta wuce ne aka yi wasan kaddamar da filin wasa na Karkanda wanda gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna mai barin gado Barista Ibrahim Shehu Shema ta kammala aikin ginin filin wanda ya ci miliyoyin naira.
Wasan kaddamar da filin wanda shi ne filin wasa na biyu a jihar, an gudanar da wasan kwallon kafa ne a tsakanin kungiyar wasan kwallon kafa ta kasa watau,’Super Eagle’da kuma kungiyar wasan kwallo ta ‘Sportlight FC’ da ke cikin garin Katsina. An tashi wasan ne babu ci a tsakanin kungiyoyin biyu.
Shi dai wannan filin wasa wanda zai rika daukar ‘yan kwallo har mutun dubu talatin da biyar (35.000) gwamna mai barin gado ne Barista Shema ya kammala aikinsa. An fitar da filin kwallo da sauran wuraren wasannin motsa jiki, da wajen canza kayan ‘yan wasa da wuraren yin tarurruka 2 da wajen hutawar manyan baki da sauransu.
Mataimakin Gwamnan jahar mai barin gado Barista Abdullahi Faskari, Kwamishinan kula da sha’anin wasanni da Shugaban Majalisar dokoki na jihar da wasu daga cikin mukarraban gwamnati mai barin gado ne suka halarci bikin kaddamarwar. Shi ma zababben gwamna mai jiran gado, tsohon Shugaban majalisar dokoki na Tarayya Alhaji Aminu Bello Masari yahalarci bikin. Sai dai babu wani bayani da bangarorin biyu watau na gwamnati mai barin gado da kuma mai jiran suyka yi a wajen bikin kaddamarwar..