Kadinal Okogie ga Buhari: ’Yan Najeriya suna fama da yunwa

Akibishop na cocin Katolika da ke Legas Kadinal Anthony Okogie ya shaida wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa ’yan Najeriya suna fama da yunwa kuma suna so ya samar musu da sauki tare da gaggauta cika alkawuran da ya yi musu lokacin kamfe na samar da kyakkyawan shugabanci da zai magance talauci a kasar nan.Kadinal […]

Kadinal Okogie ga Buhari: ’Yan Najeriya suna fama da yunwa
Kadinal Okogie ga Buhari: ’Yan Najeriya suna fama da yunwa

Akibishop na cocin Katolika da ke Legas Kadinal Anthony Okogie ya shaida wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa ’yan Najeriya suna fama da yunwa kuma suna so ya samar musu da sauki tare da gaggauta cika alkawuran da ya yi musu lokacin kamfe na samar da kyakkyawan shugabanci da zai magance talauci a kasar nan.
Kadinal Anthony Okogie, ya bayyana haka ne a wata wasika da ya rubuta zuwa ga Shugaba Buhari, inda ya tunatar da shi cewa, jam’iyyarsa ta APC ta yi alkawarin kawo canjin da kasar nan za ta ji dadi amma har yanzu ba a ga hakan ba. “Har yanzu ’yan Najeriya suna jiran a cika musu wadannan alkawura. Babu wani canji idan aka kasa kawar da tsofaffin al’amura,” inji limamin Kiristan.
Ya bukaci Shugaba Buhari ya sake waiwayar ministocinsa da kuma tsare-tsaren gwamnatinsa ciki har da masu taimaka masa wajen aiwatar da tsare-tsarensa domin yi musu garambawul da za su taimaka masa wajen cika alkawuran da ya dauka.
A ranar Litinin ce wasika ta bayyana a kafofin watsa labarai na Intanet kuma Daraktan Sadarwa na cocin Katolika na Legas Rabaran Monsignor Gabriel Osu ya tabbatar wa manema labarai ta waya cewa lallai wasikar daga Kadinal Okogie ta fito.
A cikin wasikar Kadinal Okogie wanda yana sahun gaba wajen ganin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan bai koma gadon mulki ba a zaben bara ya shaida wa Buhari cewa: “A bara lokacin da ka karbi mulki, taken ‘Canji’ ne ya yi maka rakiya zuwa  fadar Shugaban kasa. A yau kuka ‘yunwa’ ake ji a kowane sako da lungun kasar nan. Wannan wasika roko ne a gare ka kan ka yi wani abu cikin gaggawa, kuma idan kana yin wani abu to ka ninka kokarin da kake yi. Allah Ya sa kada a rubuta a tarihi cewa ’yan Najeriya sun mutu saboda da yunwa a zamanin mulkinka. A matsayinka na Shugaban kasa kai ne babban mai hidima ga kasar nana. Don haka ina kira gare ka ka tashi tsaye don share wa miliyoyin ’yan Najeriya hawaye tun kafin lokaci ya kure.”
Kadinal Okogie ya ce ba abu ne mai sauki cika alkawuran da Shugaba Buhari da jam’iyyarsa suka yi ba, amma duk da haka wajibi ne Shugaban ya tunkari wannan babban kalubale da aka dora masa. Ya ce ’yan Najeriya sun zabe shi ne saboda wadannan alkawura. “bullo da shirin ganawa da jama’a abu ne mai kyau. Amma a aikace kada ministoci kadai ke iya ganawa da kai, ka rika ganawa da ’yan Najeriya. Kai ne Shugaban kasa, wajibi ne ka rika yi wa jama’a bayani. Komai yana wuyanka ne. Koda gwamnatinka ba za ta iya dabo ba, amma akalla ka rika fadin kalmomin karfafa gwiwa. Kuma ka umarci ministocinka su rika fadin gaskiya da kuma nuna sanin ya kamata a yayin ganawarsu da jama’a. Amma romon bakan da suke yi ba zai amfane ka ba balle ’yan Najeriya,” inji shi.
Kuma ya nemi Shugaban kasar ya duba batun nada mukarrabansa don gyara kura-kuran nada mutanen bangare daya a gwamnatinsa.