Kadoji za su rika gadin kurkuku a Indonesiya
Kadoji za su rika gadin kurkuku a IndonesiyaShugaban Hukumar Yaki da fatauci da shan miyagun kwayoyi na kasar Indonesiya, y3a bijiro da bukatar gina wani gidan kurkuku a kan tsiri da masu gadinsa za su kasance kadoji.Budi Waseso ya ce kadoji sun fi mutane iya gadi, saboda ba za a iya bas u cin hanci […]
Kadoji za su rika gadin kurkuku a IndonesiyaShugaban Hukumar Yaki da fatauci da shan miyagun kwayoyi na kasar Indonesiya, y3a bijiro da bukatar gina wani gidan kurkuku a kan tsiri da masu gadinsa za su kasance kadoji.
Budi Waseso ya ce kadoji sun fi mutane iya gadi, saboda ba za a iya bas u cin hanci ba.
Ya ce zai ziyarci tsibiran da ke sassa daban-daban na kasar Indonesiya, don gano kadoji masu karfi da kaushionh hali. kasar Indonesiya na da tsauraran dokoki kan al’amarin fatauci da shan miyagun kwayoyi a duniya, kuma shekara hudu ke nan da wa’adin hukuncin kisa ya kare tun daga shekarar 2013.
“Za mu sanya kadoji da dama gwargwadon yadda za mu iya a wurin,” inji Mista Waseso, a tattaunawarsa da weani shafin sadarwa na cikin gida da ake kira Tempo.
“Ba za ka iya bai wa kadoji cin hanci ba,” inji shi.
Har yanzu shirin share fage ake yi, don hba tantance wuri ba, ko ranar da za a saka daurarru a kurkukun, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito.