Kaduna garin Gwamna

Kaduna garin Gwamna, inda babu Sarkin Yanka. Kaduna Namijin gari, kafin Turawa, tushen mulki, garin ‘yan Boko. Wannan shi ne kirarin da ake yi wa Kaduna ‘Capital Territory,’ wasu kuma na cewa Kapital Tare-tare, domin garin ya tattara dukkan yaren Arewacin kasar nan da kuma na kudanci a wuri guda, suna huldar arziki ba tare […]

Kaduna garin Gwamna

Kaduna garin Gwamna, inda babu Sarkin Yanka. Kaduna Namijin gari, kafin Turawa, tushen mulki, garin ‘yan Boko. Wannan shi ne kirarin da ake yi wa Kaduna ‘Capital Territory,’ wasu kuma na cewa Kapital Tare-tare, domin garin ya tattara dukkan yaren Arewacin kasar nan da kuma na kudanci a wuri guda, suna huldar arziki ba tare da yamutsi ko kyamar kowa ba. Wannan ne ma ya sa ake cewa  garin Kaduna  ya yi kama da dan mitsilin Najeriya, kuma idan har al’ummar cikin garin Kaduna suka yi atishawa, to daukacin al’ummomin Najeriya za su tashi da mura. A garin Kaduna ne ake kulla duk wasu abubuwan alheri da za su shafi Arewa, kuma a nan ne ake yi wa sauran al’amuranta  wankan tsarki.

Daga Kaduna ne aka yaye dukkan manyan ma’aikatan  gwamnatin da suka kakkafa sababbin jihohi, sa’ilin da aka fara yanyanka  tsohuwar jihar zuwa gida shida; daga Kaduna ne kuma ake gudanar da wasu harkokin da suka shafi tsaron yankin Arewa da sarrafa al’amuran tattalin arzikin sauran jihohin da aka yi ta kirkirowa daga bisani har suka kai goma sha tara. Amma duk da haka nan idan wasu al’amuran da suka shafi daukacin wadancan jihohin sun taso a garin Kaduna ne ake hallara don  magancewa ko aiwatar da su. Haka nan kuma dukkan sauran gwamnatocin jihohin Arewa guda goma sha takwas suna da ofisoshin hulda da jama’a da kuma gidajen garari da gwamnoninsu ko wasu manyan jami’an gwamnatinsu ke sauka idan sun zo Kaduna, don gudanar da wasu ayyukan zumunta ko na alheri ga jama’ansu.

Kai hatta ma Turawan mulkin mallaka ma da suka yi zamani a Kaduna sun san da muhimmancin wannan gari a tsare-tsarensu na gina kasa da kuma ciyar da ita gaba, shi ya sa suke alfahari da garin, musamman ma saboda tsarin da suka yi masa, daidai da na birnin Landan, wanda wani kwararren kamfanin  tsara birane da ake kira Mad Locks ya yi. Baicin haka nan sun kayata garin da wuraren hutawa da aka shusshuka korayen ciyayi a ciki aka kuma sanya masu fararen bencunan zama don shakatawa a tsakiyar furanni da shuke-shuke masu ban sha’awa. Sun kuma samar da wuraren  shakatawa da wasanni kamar filayen sukuwa da kwallon doki da kuma na golf, sa’anan suka  samar da wani randabawut (shatale-tale) mai fitar da ruwa a daidai inda za a fara shiga tsakiyar garin Kaduna. Haka nan kuma Turawan sun tanadi wuraren saukar baki na alfarma da otal-otal irin na zamani da kuma gidajen saukar da manyan baki.

A irin wadancan gidajen  alfarma ne aka sauke Sarauniyar Ingila, kueen Elizabeth a ranar 6 ga watan Fabrairun shekarar 1956 sa’ilin da ta zo Arewacin Najeriya  ziyarar gani da ido a garuruwan Kaduna da Kano. Saboda muhimancin waccan ziyarar ce Turawan suka umurci sarakunan Arewacin kasar nan su shirya wata gagarumar hawan durbar dawakai don a kayatar da Sarauniya tare da mijinta, Prince Phlips. Waccan durbar ta yi armashi ainun, har  ma an yi ta  nuna ta a  nahiyoyin Turai da Amurka, kuma hakan ya kara fadakar da mutanen wadancan wuraren game da irin kyawawan al’adun mutanen Arewacin Najeriya, kuma daga bisani da yawa daga cikinsu sun yi ta zuwa don su gane wa idanunsu abubuwan da ba su gani ba a hotunan waccan durbar da aka yi.

Bayan shekaru uku kuma sai aka sake shirya wata gagarumar durbar a garin Kaduna a ranar 15 g watan Maris na shekarar 1959 don murnar samun ‘yanci na gwaji na Jihar Arewa kafin samun ‘yancin kasar gaba daya a 1960. 

A waccan durbar dukkan sarakunan Jihar Arewa, ciki har da Sarkin Musulmi Abubakar Siddik na uku da kuma Shehun Barno, Umar el-Kanemi sun yi  hawa a Kaduna da ta kayatar, wacce kuma ta kara kwarzanta martabar Arewacin Najeriya a idanun duniya. Kafin a yi waccan durbar kuwa a Kaduna  sai da aka yi bukin amsar mulkin kai a  gindin Giginya a  garin Sakkwato da sassafe, inda Turawa suka kwace shi a shekarar 1903.  Daga waccan durbar kuma ba a kara yin wata ba sai a  watan bakwai ga watan  Nuwambar shekarar 1971 sa’ilin da aka yi wata ‘yar kwarya-kwaryar durbar don marhaban da Shugaban kasar Habasha Haile Selassie a nan Kaduna. It ma ta kayatar ainun, ta kuma janyo hankulan shugabannin Afirka ga Najeria.  

Bayan shekaru shida ne kuma, watau a watan Janairun shekarar 1977, sai aka zo aka yi durbar da ta ta fi kowacce kayatarwa a nahiyoyin Afirka da kuma Asiya, inda a can ne aka tsiri hawan durbar, kuma sarakunansu hara fararen giwaye suke hawa. Ita waccan durbar tana daga cikin abubuwan da aka tsara za a yi a nan Arewa don bukukuwan  nuna al’adun gargajiya na daukacin bakaken fatan kasashen duniya da nahiyar Africa, watau World Black Festibal of Arts and Culture, FESTAC 77. 

Wannan bukin durbar  ya haifar wa garin Kaduna da alherai masu dimbin yawa, domin kuwa a sabili da haka ne aka giggina manya-manayan wuraren zaman jama’a guda uku don kallon bukukuwa a dandalin Murtala, aka kuma gina wani otal na garari don saukar da shugabannin kasashen da za su kalli durbar a Kaduna. Baicin haka nan kuma an giggina rukunonin gidaje masu saukin kudi da ake kira ‘Low Cost Estates’ a unguwannin Barnawa da Malali da kuma Unguwar Rimi aka kayata su da gadaje da kujeru da labule da kayayyakin girki don amfanin baki daga kasashen bakar  fatar da aka saukar a wuraren sa’ilin da suka hallara kallon durbar.

Saboda haka ana iya cewa bikin hawan durbar  a garin Kaduna ya zame dabi’ar da ake alfahari da ita wacce kuma gwamnatoci da yawa ke kokarin kiyayewa da inganta yanyin da ake yin ta. Wacce Gwamnatin Jihar Kaduna ta tsara a ranar 16 ga watan nan don bukin cika shekaru dari da kafuwar Kaduna ta kayatar ainun, jama’a da yawa kuma sun halarci Dandalin Murtala don kallon mahaya dawakai, tare da sarakunansu, suna gwada bajinta da kwarewarsu  a al’amuran da suka shafi  hawa da sukuwa da dawakai.  Babu shakka mutane da yawa za su koma garuruwansu suna mamakin abubuwan da suka kalla a wajen hawan durbar. Amma wadanda za su  fi mamaki su ne wadanda suka kwana  cikin bakin duhun da ya hana su zirga-zirga da daddare a cikin gari. 

Wasu kuma da suka nace lallai sai sun zagaya cikin gari bisa ababen hawansu don ba ido abincinsa sun yi ta afkawa cikin ramukan bisa tituna, sa’annan kuma suka yi   fama da karancin man fetur don komawa nisan duniyan da suka firfito.

Taron durbar dai ya yi taro, jama’a da yawa daga jihohin Arewa  sun taru, sun kuma ga Kadunar da suke jin labarinta, wacce Turawa suka assasa, amma a ‘yan shekarun da suka wuce  sai ta zame dandalin ‘yan sara-suka da barayin shanu da na  bil-adama. To wannan ne halin da garin Kaduna, kafin Gwamna Gwalangwan, ya kasance a wannan marrar, har bakin da aka gayyato don hawa ko kuma kallon bukin durbar suke cewa jin  labarin Kaduna ya fi ganinta, domin sun tabbatar da cewa garuruwansu sun dara Kadunar da suka gani armashi ta kowane fanni ne kuwa  a halin yanzu.

 

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara