Kaduna ta kafa kwamitin binciken zaluncin ‘yan sanda

Biyo bayan matsayar da Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa (NEC) ta cimma, gwamnatin jihar Kaduna ta kafa wani kwamitin bincike domin duba zargin cin zarafin al’umma daga jami’an ‘yan sanda a jihar. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da fadar gwamnatin jihar ta fitar mai dauke da sa hannun Mai Ba Gwamnan Jihar […]

Kaduna ta kafa kwamitin binciken zaluncin ‘yan sanda

Nasir El-Rufai, Gwamnan Jihar Kaduna

Biyo bayan matsayar da Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa (NEC) ta cimma, gwamnatin jihar Kaduna ta kafa wani kwamitin bincike domin duba zargin cin zarafin al’umma daga jami’an ‘yan sanda a jihar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da fadar gwamnatin jihar ta fitar mai dauke da sa hannun Mai Ba Gwamnan Jihar Shawara kan Harkokin Watsa Labarai, Muyiwa Adekeye a ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce a ranar Litinin, 19 ga watan Oktoba za a rantsar da kwamitin mai mutane bakwai wanda zai kasance karkashin jagorancin tsohon mai shari’a David Shiri Wyom, sai AIG Lawal Tanko mai ritaya a matsayin mamba yayin da Rebecca Sako-John da kuma Mustapha Jumare za su wakilci kungiyoyi masu zaman kansu.

Idan dai za a iya tunawa NEC ta umarci dukkan gwamnonin jihohi da su kafa kwamitocin a matsayin matakin farko na tsaftace aikin ‘yan sanda a jihohinsu.

Muyiwa ya kuma ce Yakubu Umar Ibrahim zai wakilci kungiyoyin dalibai a kwamitin, sai Nathaniel Sheyi Bagudu da Inna Bintu Audu da za su wakilci kungiyoyin matasa da na Hukumar Kare Hakkin Bil’Adama.

Sanarwar ta kara da cewa mai rikon mukamin darakta a sashen kalu da hakkokin ‘yan kasa na Ma’aikatar Shari’a ta jihar, Hajara Abubakar za ta wakilci Babban Lauyan Gwamnatin jihar a kwamitin.

Muyiwa ya kuma ce, “Za a kuma nada wakilan kwamitin kungiyoyi masu zaman kansu da na matasa domin su yi aiki kafada da kafada da gwaman jihar da sauran shugabannin tsaron jihar da zai sa ido kan ayyukansu.

“Hakan kuma zai biyo bayan nadin mambobin kwamitin kare hakkin Bil’Adama da kuma tura wadannan jami’an zuwa ofisoshin karbar korafe-korafe domin a ba jama’a damar su mika koke-kokensu kan jami’an ‘yan sandan domin a magance, su’’ inji shi.

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu