Kaduna za ta karfafa dangantakar kasuwanci da Habasha

kungiyar ’yan kasuwa da masu masana’antu ta Jihar Kaduna (KADCCIMA) za ta karfafa dangantakar kasuwanci tsakaninta da kasar Habasha (Ethiopia). Shugaban kungiyar Dokta Abdul-Alimi Bello ya bayyana haka ne a lokacin da Jakadan Habasha a Najeriya Alemu Ayele Gesuma ya ziyarce su a Kaduna a ranar Lahadi.Shugaban ya bayyana ya kamata bangarorin biyu su samar […]

Kaduna za ta karfafa dangantakar kasuwanci da Habasha
Kaduna za ta karfafa dangantakar kasuwanci da Habasha

kungiyar ’yan kasuwa da masu masana’antu ta Jihar Kaduna (KADCCIMA) za ta karfafa dangantakar kasuwanci tsakaninta da kasar Habasha (Ethiopia).

Shugaban kungiyar Dokta Abdul-Alimi Bello ya bayyana haka ne a lokacin da Jakadan Habasha a Najeriya Alemu Ayele Gesuma ya ziyarce su a Kaduna a ranar Lahadi.
Shugaban ya bayyana ya kamata bangarorin biyu su samar da dangatakar kasuwanci mai karfi tsakaninsu.
“A nan Kaduna babu wata dangataka ko huldar kasuwanci mai karfi tsakanin Jihar Kaduna da kuma kasar Habasha. Abin da zan iya cewa shi ne mambobinmu suna shiga jiragen kasar Habasha idan za su yi tafiye-tafiye don gudanar da kasuwancinsu. Ina fata ziyarar da jakadan Habasha a Najeriya ya kawo mana za ta zama wata hanya ta karfafa dangantaka tsakaninmu.” Inji shi.