Kafa daula ta hanyar zubar da jini barna ce -Dokta Gumi

Da yake tsokaci a kan wannan yunkuri na Boko Haram, Dokta Ahmad Gumi ya bayyana wa wakilinmu a Kaduna cewa, “Da farko dai Annabi ya ce babu abin da zai halakar sai kananan shugabanni, saboda ba a son yara su zama shugabanni, su ke halaka al’umma. Saboda haka ba a kafa daula sai da jama’a […]

Kafa daula ta hanyar zubar da jini barna ce -Dokta Gumi

Da yake tsokaci a kan wannan yunkuri na Boko Haram, Dokta Ahmad Gumi ya bayyana wa wakilinmu a Kaduna cewa, “Da farko dai Annabi ya ce babu abin da zai halakar sai kananan shugabanni, saboda ba a son yara su zama shugabanni, su ke halaka al’umma. Saboda haka ba a kafa daula sai da jama’a da dattijai. Kuma ya zama daular ta kafu da kanta, tana da komai, sannan daula ba mai korar mutane tana kashe al’umma ba. Kuma wadda mutanen da aka cuta suke kokarin samun mafakar taimako. A cikin irin wannan hali da muke ciki idan wani ya ce zai kafa daula ta Musulunci yana amfani ne da sunan Musulunci domin yin tasa barna.
“Duk inda ake kashe musulmi da wanda ba musulmi ba da nufin kafa daular Musulunci, to Allah ba Ya son musuluncinka, domin rai Allah yake so a tsare. Idan kuwa har sai ka yi kisa, to Allah ba Ya son musuluncinka. Kamar karuwa ce ta ce sai ta yi zina kafin ta ba da sadaka, Allah ba Ya son sadakarki, kar  ki yi zina. Zubar da jinin da za ka yi domin kafa daularsa shi da kansa ya rusa ta.”
Sannan ya ce, “An yi bayani da daular Musulunci za ta zo ta yi canji, za ta kuma yi  mulkin kama-karya, har kuma ta zo ta rushe. Yanzu ta rigaya ta rushe, kuma duk wanda ya ce zai kafa ta kuma ta hanyar zubar da jini, to barnar da yake yi ta fi a kafa ta, domin Allah da kanSa Ya rusa ta. Me ya sa kuma Allah Ya rusa ta, shugabanin musulmin ne da kansu suke barna. Bari ka ji, tun lokacin su Malik, halifofi suke dukan malamai. Malik an buge shi, Ibn Taimiyya ma an buge shi, malami babba irinsa an kulle shi har ya mutu. Su wa suke aikata hakan?  -Daulolin musuluncin ne suke azabtar da malamai, kuma malamai su ne magadan Annabawa.
“Allah Ya gaji da daular musuluncin gaba daya sai Ya tsayar da su, saboda ba musuluncin suke yi ba, illa yaudara da cutar jama’a. Idan har wadanda suka yi shekara 200, 300, 400 har zuwa 700 suna barna, kai ne a yau za ka yi ta gaskiya? Kana dai yin amfani da sunan Allah ne ka cuci jama’a, kuma Allah zai bayyana ka.” Inji shi.
Shi ma a nasa tsokacin, Limamin masallacin Usman Bin Affan da ke Baneks a Abuja, Malam Abduljalil Dabo Madaka, cewa ya yi, “Wannan al’amarin akwai daure kai, sai dai mu dukufa da addu’a ita ce mafita. Mu dai ’yan kasar nan ne, mun san yadda wannan al’amari ya faro, an samu sauyi irin daban-daban. Tambaya ta farko ita ce, shin su waye ne ma Boko Haram. Allah shi Ya halicce mu, Shi Ya
san sirrin wannan abun. Sai dai mu yi ta neman gafara tare da roqon Ya sama mana mafita. Ita kanta hukuma an rasa inda ta sa gaba. Sai dai ala kulli halin, Allah na jarabtan bayinSa da matsaloli iri-iri, kuma da neman gafara tare da addu’a, Zai yaye mana komi.’’
Gwamnatin tarayya ta yi watsi da shelar da shugaban qungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya yi cewa garin Gwoza da ke hannun qungiyarsa ya koma qarqashin daular musulunci.
Gwamnatin ta mayar da martanin ne kwana guda bayan shugaban Boko Haram ya fitar da wani hoton bidiyo inda a ciki ya yi iqirarin cewa garin Gwoza ya zama wani vangare na daular musulunci.
Ministan yaxa labarai, Mista. Labaran Maku ya ce babu wani vangare na qasar nan da zai zama cibiyar gwaji ta kafa daular ‘yan ta’adda a Afirka ta yamma, ya ce gwamnati tana da qwarin gwiwa a kan qarfin sojan qasar nan wajen tsarewa da kare martabar iyakokin Nijeriya.