Kafa dokoki masu tsauri kadai ba zai magance cin hanci ba – Sheikh Kabir Gombe
Babban Magatakardan kungiyar Izala ta kasa Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe ya bukaci gwamnatoci a matakai daban-daban su sanya tsarin fadakarwar addini a yayin ba da horo ko sanin makamar aiki ga sababbin jami’an da suka dauka don cusa musu tsoron Allah da magance barna a dukiyar gwamnati. Sheikh Kabiru Gombe wanda ya yi kiran […]
Babban Magatakardan kungiyar Izala ta kasa Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe ya bukaci gwamnatoci a matakai daban-daban su sanya tsarin fadakarwar addini a yayin ba da horo ko sanin makamar aiki ga sababbin jami’an da suka dauka don cusa musu tsoron Allah da magance barna a dukiyar gwamnati.
Sheikh Kabiru Gombe wanda ya yi kiran a yayin taron lacca na musamman da addu’a ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari karo na biyar da Alhaji Shu’abu Ahmad Gara Gombe ke shiryawa duk bayan kwana dari tun hawan karagar mulki na gwamnatin, idan ya kasance babban mai jawabi, ya ce kafa dokoki masu tsauri kadai da tarin matakai ba za su magance matsalar ba.
Sheikh Kabir Gombe ya ce cin hanci da rashawa ya yi wa kasar nan illa a kusan dukkan bangarori da suka hada da rashin cikakken kula da kiwon lafiya da tituna da wutar lantarki, kuma ga matsalar sace jama’a, da tsare masu gaskiya da kuma sake masu laifi.
Malamin ya lisafto wasu matakai da ya ce dole sai gwamnati ta aiwatar da su sannan ta samu cikakkiyar nasarar dakile matsalar cin hanci wanda shi ne taken taron na wannan karo da ya gudana a Hedikwatar Izala ta kasa da ke Abuja.
Matakan inji Shehin Malamin, sun hada da daukar jami’ai da suka cancanta a matsayin ma’aikata kuma a wadace domin magance cinkoso da ke bude kafar ba da cin hanci ga masu gaggawa da kyautata albashi, da dora mutane nagari a matsayin masu kafa doka da masu tilasta bin dokar da kuma masu aiwatar da hukunci a kan wandanda suka bijere wa dokar. Haka nan ya ce dole ne shugaba ya kasance ya yi adalci ga duk dan kasa wajen ba da hakki.
“Sai dai shari’a ta ba shi damar yin ihsani ga wadanda suka taimaka masa ya samu nasara ta hanyar sadaukar da dukiya ko kusancinsu da al’umma inda bayan ya bai wa kowane dan kasa hakkinsa, su kuma zai iya kara musu da wasu takaitattun mukamai, ko yi musu hanya ta kwangila a matsayin sakayya ga dukiyar da suka batar a lokacin gwagwarmayar kawo shi.
A tsokacin Shugaban kungiyar Izala ta kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya bukaci ’yan Najeriya kan su kara hakuri da gwamnatin Buhari tare da yi mata addu’a. Ya ce “Kada mu manta da halin ukuba da fargaba da tsangwama da cin fuska da al’umma ta fuskanta amma duk wannan yanzu ya kau. Idan muka gode wa Allah a kan wannan ni’ima, sai Ya yi mana kari a kan abubuwan da muka rasa.”
Ya ce, “Sai dai akwai bukatar gwamnati ta kara kula da abubuwan da za su kara jawo mata kaunar jama’a da suka hada da saukaka musu rayuwa don rage wa kanta abokan gaba. Sannan ba laifi ba ne idan gwamnati na shakkar wadansu, sai ta kyautata musu don jawo kaunarsu gare ta, ba lallai sai wadanda ta wahala da su ba. Annabi Muhammad (SAW) ya yi kyautar rakuma dari-dari ga wadansu manyan Makka da ba su jima tare da shi ba, bayan wata nasara a wajen yaki, sannan ya bar wadanda ke tare da shi haka nan. Ya yi hakan ne don dadada musu da kara kusantar da zuciyarsu gare shi.”