…Kafa Ma’aikatar Kula da Kiwo zai magance rikicin manoma da makiyaya – Bodejo
Ana zargin kungiyarku ta Miyetti Allah Kautal Hore da kai hare-hare a Benuwai me za ka ce? kungiyar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore muna Allah wadai da kai hare-hare a wasu kauyukan da suke kananan hukumomin Logo da Guma a Jihar Benuwai inda aka ce an kashe mutum 20 tare da raunata wadansu a […]

Ana zargin kungiyarku ta Miyetti Allah Kautal Hore da kai hare-hare a Benuwai me za ka ce?
kungiyar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore muna Allah wadai da kai hare-hare a wasu kauyukan da suke kananan hukumomin Logo da Guma a Jihar Benuwai inda aka ce an kashe mutum 20 tare da raunata wadansu a makon jiya. kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore kungiya ce ta zaman lafiya da hadin kan kasa da ke daukar matakan neman hakki ta hanyar tattaunawa ko zuwa kotu idan matakin sulhu ya ci tura. Muna jajanta wa gwamnati da al’ummar Jihar Benuwai tare da yaba wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan daukar matakin gaggawa bayan faruwar lamarin ta hanyar aikewa da Ministan Al’amuran Cikin Gida Janar Abdurrahman Dambazau (mai ritaya) zuwa jihar. Za mu ci gaba da kiyaye tsarin zaman lafiya kuma ba ma goyon bayan duk wanda zai aikata wani abu akasin haka, saboda haka muna kira ga jami’an tsaro su kama duk wanda ake zargi da hannu a lamarin tare da gudanar da bincike don zartar da hukunci a kansa.
Kuma muna kira ga Fulani makiyaya da ke Jihar Benuwai da sauran jihohin kasar nan su kasance masu bin doka da oda tare da jiran hukunci kan karar da muka shigar a kotu game da batun hana kiwo a wasu jihohin kasar nan, kuma muna fata Gwamnatin Tarayya za ta yi nazari a kan dalilan da suke jawo rikice-rikice a jihohi irin su Adamawa da Taraba da Kaduna da Zamfara da Nasarawa da Filato da Benuwai musamman wadanda suke da nasaba da takaddama a kan wuraren kiwo da nufin samar wa lamarin maslaha da magance ci gaba da aukuwar rigingimun.
Fulani suna fuskantar matsaloli iri-iri kama daga na yi musu satar shanu zuwa na hana su wurin kiwo, wane shiri kungiyarku ke yi na fuskantar wannan a bana?
Matakin da muke dauka bai wuce na wayar da kan jama’armu ba da kuma ci gaba da nema musu hakkokinsu a wajen hukuma kasancewar gwamnati ta gaza yin abin da ya wajaba a kanta. Lamarin har ya kai ana amfani da hakan a jawo rigingimu a kan makiyaya don sama wa gwamnati suna ko a bata mata. Zan ba ka misali da jihohi biyu, wato Benuwai da Ekiti, kowa ya san yadda ma’aikata ke fuskantar matsalar rashin biyan albashi a jihohin nan biyu da gwanoninsu suka gaza biya. To babbar damuwarsu ita ce me za su yi da zai karkatar da jama’a daga wannan matsalar. Sannan idan ka koma jihohin Arewa maso Yamma irin su Zamfara da Katsina da ma Kaduna kafin a baya-bayan nan a samu sauki bayan zuwan Gwamna Nasiru El-Rufa’i, matsalolin da ke damunsu su ne na masu satar shanu wadanda sakamakon hakan makiyaya da dama sun yi kaura zuwa jihohin Kudu da zama. Mun san Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kokari bakin gwargwado wajen magance matsalar satar shanu, an samu sauki sosai ta wannan fuska idan a ka kamanta da baya, sai dai kuma ana fuskantar wata sabuwar matsalar, ita ce ta hana kiwo irin wadda aka saba yi tare da neman a killace shanu a waje guda da sunan gidan gona wanda Bafulatanin da na sani da kuma irin dabbobin da yake kiwo ba zai iya ba.
To me kake ganin ya kamata a yi?
Mafita kawai ita ce gwamnati ta ware Ma’aikatar Kiwo daga ta Noma kasancewar tsarin da ake bi a yanzu bai bai wa makiyaya wata kulawa, gara ma masu kiwon kaji da kifi muna jin yadda su ake ba su tallafi a yayin da mu kuma a kullum sai dai matsaloli da ke kara gurgunta sana’armu kadai a ke kirkiro mana. Kiwo sana’a ce da ke bukatar kulawa ta musamman da idan gwamnati ta maida hankali a kai zai samar mata da kudin shiga ba kadan ba, sannan ya raya sana’ar dimbin jama’a saboda hatta fata da ake jakunkuna ko takalma masu daraja da fatun dabbobin ake yi, ga madara. Sannan dole ne gwamnati ta dubi wanda ya dace da shugabancin ma’aikatar. Shugaban kasa Buhari yana iya kokarinsa wajen inganta rayuwar makiyaya, sai dai matsalar da ake samu ita ce wanda ke rike da mukamin ma’aikatar noma bai da sha’awar haka, kamar yadda ya nuna a lokacin da Majalisar Tarayya ta nemi jin ta bakin ma’aikatar a kan shirin kafa dokar da kafa Hukumar Kula da Al’amuran Kiwo, ba ma kafa ma’aikata ba wanda Shugaban kasa yana da ikon kafawa a kashin kansa.
Wane hali kake jin kasar nan za ta samu kanta idan aka ci gaba da takura wa makiyaya ta hanyar kirkiro dokoki da ke dabaibayi ga sana’arsu?
Ina kira ga Shugaban kasa da ya kau da batun kawaici ya dubi abin da ma’abota wannan sana’ar suke bukata ya yi musu irin yadda ya yi ga manoma saboda muhimmancinsu ga rayuwar al’umma da kuma tattalin arzikin kasa. A yanzu haka makiyayan kasar nan a kullum fita suke yi, wadansu na tafiya kasar Ghana wadansu Afirka ta Tsakiya da sauransu. Ke nan idan ba a dauki matakin gaggawa ba, kasar nan za ta koma shigo da nama bayan ta magance na shigo da abinci. A yanzu yawancin sarakunanmu na Arewa Fulani ne haka nan su ma gwamnonin har ya kai ga shi kansa Shugaban kasa, kamar yadda wadansu da suka gabace shi Fulani ne, amma saboda kara irin tamu ta Fulani ba a jin wani nuna fifiko a tsakanin jama’a.
Wadansu gwamnoni na neman mayar kiwo ta zama a wuri guda maimakon yawo me za ka ce?
A farkon lokacin da gwamnatin Jihar Benuwai ta fara magana a kan wannan doka na tattauna da wadansu masana harkar kiwo na gidan gona kamar 5, inda a karshe muka gamsu cewa tsarin ba zai yiwu ba a yanayi irin na kasarmu da kuma na irin dabbobin da muke kiwo, saboda na farko ba mu da wadatar ruwa irin na kasashen da ke irin wannan kiwo da kuma fili da za a bukata. Su ma wadanda suka fara irin wannan kiwo bayan sun sayo irin nau’in shanun daga kasar waje wanda guda daya kawai ake sayar da shi kamar Naira dubu 700, ina shanunsu ke a yanzu, duk gidajen gonar sun zama kango. Illa iyaka idan sun dage a kan sai mun yi kiwon gidan gona sai su saye shanun da muke da su a yanzu wadanda a kullum ana yanka kamar dubu 6 a mayankan Legas kadai, amma ba su kare ba, in ya so mu sai mu kama wata sana’ar daban mu huta daga wannan tsangwama ta yau daban, ta gobe daban.
Ana kama Fulani a lokuta da dama a harkar garkuwa da mutane, me kake jin ya jawo haka?
A gaskiya nakan ji takaici a duk lokacin da na ji ko kuma na ga ana nuna al’ummata da hannu a wannan lamari. Sai dai abu guda da na fahimta shi ne; wadanda ake samunsu da hannu a lamarin nan ba Fulanin asali ba ne. A al’adarmu ta Fulani akwai masu shanu akwai masu kiwo wadanda a Fulatanci ake kiransu “Gainako” wato mai kiwo. Ko a tsakanin Fulani alakarsu da su ba ta wuce ta kiwo ba, amma idan ta shafi na sha’anin auratayya ba ma ba su aure, to ina jin daga cikin ire-iren wadancan mutanen ne da suka rasa sana’arsu sakamakon sace-sacen shanu da Fulani suka fuskanta a baya, ga kuma sanin daji sosai suka fada wannan harka. Ba zan yi mamaki ba idan aka ce an kama irin wadannan mutane a cikin masu garkuwa da mutane ko masu fashi. Amma a zuriya ta Fulanin asali a ce an samu irin wadannan, har yau ban ji ba. Sannan matsalar satar shanu ko garkuwa da mutane ta yi wa Fulani illa sosai, su ne suka fara fuskantar wannan matsalar kafin ta karaso zuwa gari. An sace mana mutanenmu da dama wadansu ma yara ne kanana har yau babu su babu labarinsu, hakan ya faru ne musamman a lokacin rigingmu a jihohin Fulato da Benuwai da kuma Kaduna. Duk abin da wadanda suka sace su din nan suka dora su a kai babu shakka suna iya bi. Kowa ya san makiyayi da sanin daji, to sana’arsa ta kiwo da ita kadai ya sani an raba shi da ita, shi kuma bai san ko’ina ba idan ba wannan dajin ba, ka ga ke nan sai abin da hali ya yi. Tushen fashi da makami kusan kowa ya san daga yankin da ya faro bayan an yi fama da Yakin Basasa a kasar nan, inda matasansu suka rasa sana’o’insu ga kuma sanin makami. Saboda haka shawarar da zan bayar ita ce; idan an tashi magana a kan irin wadancan masu laifi a kira su da aikin da suke yi shi ne masu garkuwa da mutane ko ’yan fashi kamar yadda ake yi wa sauran kabilu ba yadda jaridun kasar nan ke bayyanasu da Fulani ko makiyaya masu garkuwa da mutane ko masu kashe mutane ba. Kuma idan wata kabila ce ta yi irin hakan ba za ka ji ana danganta ta da kabilarta ba. A fuskanci mai laifi a matsayin mai laifi, idan kuma afuwa za a yi musu kamar yadda aka yi wa saura, a yi musu tare da ba su jarin sana’a bayan an horar da su.