Kafa wuraren kiwo zai magance rikicin manoma da makiyaya – Sarkin Dukku
Mai martaba Sarkin Dukku da ke Jihar Gombe, Alhaji Haruna Rashid ya ce, kudirin da Gwamnatin Tarayya ta dauka na kafa wuraren kiwo na zamani a wasu jihohin kasar nan, zai kawo zaman lafiya a tsakanin manoma da Fulani makiyaya. Sarkin ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da ’yan jarida a garin Wase […]
Mai martaba Sarkin Dukku da ke Jihar Gombe, Alhaji Haruna Rashid ya ce, kudirin da Gwamnatin Tarayya ta dauka na kafa wuraren kiwo na zamani a wasu jihohin kasar nan, zai kawo zaman lafiya a tsakanin manoma da Fulani makiyaya.
Sarkin ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da ’yan jarida a garin Wase a Jihar Filato.
Ya ce, suna goyon bayan wannan kudiri na Gwamnati Tarayya na kafa wuraren kiwo na zamani.
Sarkin ya ce kamar a Jihar Gombe tuni an tanadi fili mai fadin sama da eka 200 da za a yi wuraren kiwon, kuma tuni Ministan Gona ya ziyarci wuraren don ganin an fara aikin kafa wuraren kiwon.
Ya ce, kudirin kafa wuraren kiwo na zamani, ya nuna cewa Gwamnatin Tarayya tana kokarin ganin an samu zaman lafiya a tsakanin Fulani makiyaya da manoma a kasar nan.
Ya yi kira ga Fulani makiyaya da manoma kan kowa ya bai wa kowa hakkinsa a zauna lafiya. Domin dole ne a yi noma, kuma dole ne a yi kiwo.
Sarkin ya bukaci a samar wa sarakuna ayyukan da za su rika yi, a kundin tsarin mulkin kasar nan.
“Ya kamata a tsara wa sarakuna abubuwan da za su yi a kundin tsarin mulkin Najeriya. Idan ma ba zai yiwu a tarayya ba, to jihohi su yi irin wannan a jihohinsu. Yin haka zai kara wa sarakunan daraja, kuma zai dada karfafa musu gwiwa kan ayyukan da suke yi,” inji Sarkin.