Kafafen labarai mallakin al’umma ne ba na wata jam’iyya ba – Masari

Sabon Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya ce gidajen rediyo da talabijin na jihar mallakin al’umma ne ba na wata jam’iyar siyasa ba.  Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana a haka a wajen walimar da aka shirya a gidan gwamnatin jihar don karrama shi a ranar Juma’ar da ta gabata bayan karbar ragamar […]

Kafafen labarai mallakin al’umma ne ba na wata jam’iyya ba – Masari
Kafafen labarai mallakin al’umma ne ba na wata jam’iyya ba – Masari

Sabon Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya ce gidajen rediyo da talabijin na jihar mallakin al’umma ne ba na wata jam’iyar siyasa ba. 

Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana a haka a wajen walimar da aka shirya a gidan gwamnatin jihar don karrama shi a ranar Juma’ar da ta gabata bayan karbar ragamar mulkin jihar.
Gwamna Masari ya ce, wadannan kafofin watsa labarai biyu mallakar al’ummar Jihar Katsina ne da kowa ke da damar ya fadi albarkacin bakinsa kamar yadda doka ta bayar, ba kafofi ne na wata jam’iyya don takamar ita ke da mulki ba.
Gwamnan ya kara da cewa, “Daga yau Juma’a, gidan rediyo da gidan talabijin na Jihar Katsina mallakar al’ummar jihar ne ba wani ba. Saboda haka, kowa na da ikon ya je ya fadi albarkacin bakinsa kuma ko daga kowace jam’iyya ya fito walau APC ko PDP ko APGA da sauransu. In dan APC ya zo aka ba shi dama ta minti 30 shi ma dan wata jam’iyyar a ba shi irin wannan dama ba tare da nuna bambanci ba.”
Gwamna Masari ya ce, ta wannan hanya ce kadai za su iya gane inda suka samu wasu kura-kurai domin yin gyara. Sai ya kara da cewa,”Saboda haka ina shaida wa shugabannin wadannan gidajen watsa labarai su ba kowa dama ba kowane lokaci aka rika jin muryoyin jami’an gwamnati kawai ba.”
Gwamnan ya nanata manufofin sabuwar gwamnatinsa wajen bayar da fifiko ga batun ilimi da noma.
Aminiya ta tuntubi wasu jama’a a kan wannan mataki da Gwamnan ya dauka, inda suka ce matakin ya yi daidai.
Alhaji Adamu Abdullahi ya ce, “Yanzu ne za mu fara kallo da kuma sauraren wadannan kafofin watsa labarai, saboda yanzu ne suka zama na jama’a ba na Gwamna ko matar Gwamna ko wata jam’iyya ba.”
Shi kuwa Muntari Allah Wahid cewa ya yi, “Yanzu ne muka fita daga takumkumin fadin albarkacin bakinmu. Kuma yanzu ne muka san muna da kafofin watsa labarai namu. Sai dai yana da kyau jama’a su sani ba wai kada bayar da wannan dama ta sanya su wuce gona da iri wajen adawar siyasa. “Mu zamo in ma za mu yi suka ga gwamnati don kawo gyara, mu rika yin masu ma’ana ba na batanci ko cin zarafi ba.” Sai ya yi kira ga gwamnatin ta kafa gidan rediyo mai karamin zango (FM) kamar yadda ake da su a wasu jihohin.
Wani da ya nemi a sakaya sunansa cewa ya yi, neman suna da fadanci ne daga shugabannin kafofin watsa labaran ya sa suka mayar da su ’yan amshin Shata. Ya ce, a lokacin mulkin marigayi Umaru kafofin suna aikinsu bisa ka’ida. A lokacin mulkin Shema da farko ana barin jama’a na fadin albarkacin bakinsu, amma daga baya sai ya zamo ko talla aka kai in dai har aka fahimci mai tallar ba dan PDP ba ne ko tallarsa ba a sawa.