Kafafen labarai su daina nuna son kai wajen yayata matsalolin al’umma
Muhimmin aikin kafafen watsa labarai shi ne ilimantarwa da wayar da kan al’umma da tabbatar da cewa gwamnatoci a dukkan matakai sun yi abin ya dace wajen kyautata wa jama’ar da ake mulka. Abu ne da ya dace kafafen watsa labarai su yi aiki ba tare da nuna bambancin addini, kabila ko bangaranci ba, koda […]
Muhimmin aikin kafafen watsa labarai shi ne ilimantarwa da wayar da kan al’umma da tabbatar da cewa gwamnatoci a dukkan matakai sun yi abin ya dace wajen kyautata wa jama’ar da ake mulka. Abu ne da ya dace kafafen watsa labarai su yi aiki ba tare da nuna bambancin addini, kabila ko bangaranci ba, koda matsalar da kafar labaran za ta tabo ko maida hankali kai, bai shafi al’ummar bangaren da take ba, Kudu ko Arewa.
Al’ummar Jihar Kano da Arewa da duk mai zuciyar tausayi sun wayi gari cikin watan da ya gabata da labari mai tada hankali na gano yara 9 ’yan asalin jihar da wadansu mutane suka sace tare da sauya musu sunaye da kuma addininsu na Musulunci tare da sayar da su a Jihar Anambra. Shekaru da dama iyaye a Jihar Kano ke korafin batar da ’ya’yansu ke yi a lamari mai kama da almara.
Bayan gano yara tara da Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta yi, abin mamaki da takaici, wanda ba shi ne karo na farko ba shi ne yadda wasu kafafen watsa labarai musamman na Kudu ancin suka kawar da kansu daga abin da ya faru da abubuwa makamantan lamarin na Kano da suke faruwa a Arewacin Najeriya.
A shekarar 2016 kafafen watsa labarai galibi na Kudu sun yi ta yayata labaran wata yarinya mai shekara 15 mai suna Ese Oruru, wadda ta yi soyayya da wani dan asalin Jihar Kano har ta kai ga yarinyar ta biyo shi jihar daga Jihar Bayelsa inda suka zauna.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wannan yarinya ba garkuwa saurayin ya yi da ita ba, bisa radin kanta ta biyo shi har Jihar Kano, amma kungiyoyi masu zaman kansu da kafafen watsa labarai na Kudu suka yi ta yayata sabanin ainihin abu da ya faru a tsakaninsu.
Batun gano yaran Jihar Kano a Anambra ya samu halin-ko-in-kula daga shugabanni da kafafen watsa labarai na Kudu, wanda ba shi ne na farko ba an sha yin irin wannan hali a baya.
A duk lokacin da matsala ta kunno kai a Arewa abu ne mai wuya ka ga kafar watsa labarai ta Kudancin Najeriya ta yayata domin samar da mafita. Irin wannan abu kan dasa ayar tambaya ko kasar guda ce mai al’umma daya?
Irin bambancin addini da kabilanci da ke zukatan ’yan Najeriya na bayyanuwa a tsarin aiki da kafafen watsa labarai ke yi wajen tunkarar lamuran da suka shafi kasa wadanda ya kyautu kafafen watsa labarai su tunkare su yadda ya dace domin neman mafita.
’Yan magana na cewa ‘wanda ya riga ka barci, dole ya riga ka tashi’ ma’ana Kudancin Najeriya ya sha gaban Arewa wajen samar da kafafen watsa labarai wanda hakan ya sanya kafafen ke ruruta batutuwan da suka shafi al’ummar shiyyar. Magana ta gaskiya lokaci ya yi har ma yana neman wucewa da ’yan kasuwa da ’yan bokon Arewa za su tashi tsaye wajen samar da kafofin watsa labarai da za su rika bayyana wa duniya matsalolin da ke ci wa al’ummominsu tuwo a kwarya ciki har da irin batun satar yara ’yan Jihar Kano.
Dole ne kafafen watsa labarai a Najeriya su rika gudanar da aikinsu ba tare da nuna bangaranci ba, saboda in mutum ba ya zaune a Najeriya kuma yana karanta wasu daga cikin jaridun Kudu, zai dauka kasar a rabe take, saboda yadda kafafen watsa labaran ke aiki da son kai.
Domin ciyar da kasa gaba da kuma kasancewarta tsintsiya madaurinki daya, dole kafafen watsa labarai su rika daukar matsala a dukkan sassan kasa wajen neman mafita. Sabanin haka ke faruwa a halin yanzu kuma babu abin da zai haifar face dasa gaba da kiyayya a tsakanin ’yan Najeriya.
Umar Ahmad Abubakar, dan jarida ne a Gombe. 08080831633