Kafafen sadarwar zamani na taimakawa wajen kawo rarrabuwar kai – Kukan-Daka

Tsohon Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Gombe, kuma malami a Kwalejin Ilimin Qere-Qere ta Tarayya (FCE-T) da ke Gombe, Alhaji Kabiru Usman Kukan-Daka, ya ce kafafen sadarwa na zamani suna taimakawa wajen kawo rarrabuwar kai a duniya. Tsohon Kwamishinan wanda dan siyasa ne ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyin Aminiya, bayan kammala […]

Kafafen sadarwar zamani na taimakawa wajen kawo rarrabuwar kai – Kukan-Daka

Tsohon Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Gombe, kuma malami a Kwalejin Ilimin Qere-Qere ta Tarayya (FCE-T) da ke Gombe, Alhaji Kabiru Usman Kukan-Daka, ya ce kafafen sadarwa na zamani suna taimakawa wajen kawo rarrabuwar kai a duniya.

Tsohon Kwamishinan wanda dan siyasa ne ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyin Aminiya, bayan kammala wani taron da daliban kimiyyar siyasa na jami’o’in qasar nan suka gudanar kan muhimmanci kafafen sadarwa na  zamani da aka gudanar a Jami’ar Jihar Gombe.

Alhaji Kabiru Kukan-Daka, ya ce an qirqiro kafafen sadarwa na zamani ne domin amfanin jama’a amma a nan Najeriya da wasu qasashen ba a amfani da kafafen yadda suka dace, inda duk wanda ya leqa Facebook zai ga cewa matasa suna amfani da shi a baibai.

Alhaji Kukan-Daka ya ce wannan ne ya sa aka shirya wannan taro domin jawo hankalin matasa musamman daliban jami’o’i domin su riqa yin hattara kan yadda ake amfani da addini da siyasa a  kafafen sadarwar don kawo rarrabuwar kai. “Duk wanda yake amfani da wannan kafa zai ga abin baqin ciki kan yadda wadansu suke amfani da kafar suna kawo rashin fahimta da cusa qiyayya a tsakanin jama’a, kuma babu abin da hakan yake haifarwa sai koma baya. Misali tashin hankalin da ya faru a qasar Rwanda da irin wannan kafa aka yi amfani aka jawo matsalar da ta haifar da kashe-kashen rayuka, kuma ba mu son irin haka ya faru a Najeriya. Shi ya sa aka shirya taron fadakarwar domin idan haka ya faru a Najeriya abin zai yi muni fiye da yadda ake tsammani,” inji shi.

Malamin ya ce ba ’yan siyasa ne suke sanya matasan suna yin rubuce-rubucen jawo fitina ta kafafen sadarwa ba, matasan ne suke rubuntu su tura a qashin kansu, inda ya ce babu dan siyasar da zai ce wani ya rubuta abin da zai ta da hankali. Ya ce amma ya yarda a wasu lokuta da wurare kadan wadansu kan iya amfani da matasan wajen nuna qabilanci ko addini domin cimma wasu muradunsu na siyasa. “Amma dan siyasa na qwarai mai neman quri’a ne a wajen Musulmi da wanda ba Musulmi ba, mai neman mutane ba zai zamo mai watsa su ba, fiye da kashi 70 na masu amfani da kafafen su suka saka kansu ba wani ya saka su ba, amma ana iya samun qananan fitinu nan da can da ’yan siyasan kan haddasa saboda biyan buqatar kansu,” inji shi.

Sai ya yi kira ga matasa da ’yan siyasa su ji tsoron Allah kada su yi abin da zai jawo wargajewar Najeriya, don haka kada su bari bambancin siyasa ya sa su jefa qasar a cikin fitina ta hanyar rubuce-rubuce marasa tushe a kafafen sada zumuntar.