Kafin a fara koyarwa a cikin harshen uwa
Bayan da a kwanakin baya aka ruwaito Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu yana shaida wa manema labarai cewa kasar nan za ta duba yiwuwar koyar da daliban makarantun firamare ’yan aji daya zuwa uku a cikin harshen uwa, ake ta samun cece-ku-ce a kan cancanta da rashin cancantar yin hakan a tsakanin ’yan kasa, shugabanni […]
Bayan da a kwanakin baya aka ruwaito Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu yana shaida wa manema labarai cewa kasar nan za ta duba yiwuwar koyar da daliban makarantun firamare ’yan aji daya zuwa uku a cikin harshen uwa, ake ta samun cece-ku-ce a kan cancanta da rashin cancantar yin hakan a tsakanin ’yan kasa, shugabanni da masu ruwa-da-tsaki a kan fanni ilimi da wadanda suke tofa albarkacin bakinsu kawai suna yi ne bisa ga ’yancin fadin albarkacin baki da kundin tsarin mulki ya tanadar musu. Ministan, ya fadi haka ne lokacin da yake bikin kaddamar da rahoton ci gaban duniya na bana (2018), da rukunnan Bankin Duniya ya gabatar, kasancewar rahoton na bana ya mayar da hankali ne a kan fannin ilimi.
Rahoton ya tabbatar da cewa kasashe za su samu ci gaban ilimi, muddin suka kula da abubuwa uku wato, damar koyarwa da nuna himma da kuma daidaito a kan abubuwan da ake so a koyar. Tun bayan da Ministan ya yi wancan tsokaci, wadansu masu fada-a-ji da masu ruwa-da-tsaki a fannin ilimi suke ta tofa albarkacin bakinsu a kan alfanu da rashin alfanun jarraba hakan. Daga cikin irin wadannan shugabanni da suka yi kiran har da Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi II wanda ya nanata cewa lallai lokaci ya yi da za a koma koyar da ilimin boko a cikin harshen uwa har ma ya kara da cewa a harshen Hausa.
Dama can sashi na 55, na kundin tsarin mulkin kasar nan na 1999 da aka yi ma kwaskwarima a shekarar 2011, ya yi tanadin yin amfani da manyan harsunan kasar nan uku, bayan harshen Ingilishi wajen gudanar da harkokin zaman Majalisun Dokokin kasar nan. Sashen ya yi bayani kamar haka: Za a gudanar da harkokin zaman Majalisun Dokoki na kasa cikin harsunan Ingilishi da Hausa da Ibo da Yarabanci idan an yi kyakkyawan tanadin yin haka. Sashen, bai yi bayanin wani irin kyakkyawan tanadi za a yi kafin yin amfani da sauran manyan harsunan kasar nan uku ba. Amma a tawa gajerar fahimtar, tanadin ba na jin zai wuce samar da na’urori da masu tafinta da za su rika fassara gudummawar kowane dan majalisa kai-tsaye a daidai lokacin da yake ba da gudunmawa a daya daga cikin wadannan harsuna uku.
Ina ganin rashin son yin amfani da wadannan manyan harsunan kasar nan uku ga masu girma ’yan majalisun dokokinmu na kasa ya sanya yau ana kusan shekara 20, ana mulkin dimokuradiyya ba kakkautawa a kasar nan ya sanya majalisun dokokin suka kasa yin wata hobbasa wajen ganin tabbatuwar hakan, al’amarin da za a iya dora shi kacokan kan rashin kishin kasa, amma ba wai don rashin kudi ko masu ilimin da za su tabbatar da fara aiki da harsunan kasar nan uku ba. Ai ka ga a majalisun dokoki na jihohi, suna yin amfani da harshen da yake mafi rinjaye a jihohinsu, kuma duk da cewa akwai harsuna sama da 400 a kasar nan, amma dai wadancan ukun na kasa da Ingilishi su ake amfani da su a irin wadancan jihohi ba tare da jin wani ka-ce-na-ce ba, amma a kasa, hakan ya gagara.
Mai karatu, kada ka manta cewa shekaru aru-aru tun bayan samun ’yancin kan kasar nan daga Turawan mulkin mallaka na Birtaniya a 1960, daga lokaci zuwa lokaci a kan tayar da muhawara irin wannan, walau ta zabar wa kasar nan harshen kasa daga cikin manyan harsunan kasar uku, wato Hausa da Ibo da Yarabanci, kai na san ma har a lokutan rubuta kundin tsarin mulkin kasar nan muhawara irin wannan kan bijiro cikin taron amma sai ta kare a kan yin amfani da wadannan manyan harsuna uku a cikin zaurukan majalisun dokoki na kasa da na jihohi ko a taron Majalisar Zartaswa ta kasa (ta ministoci) ba ka jin ana gudanar da tarurrukanta a daya daga cikin wadannan manyan harsuna uku na kasar nan, ko mai dai sai a harshen Ingilshi.
Wannan ba wani abu yake nuni da shi ba illa kasashe irin namu na Nahiyar Afirka da suka samu ’yancin kai daga Turawan mulkin mallaka har yanzu suna cikin kangin bauta ta yin amfani da harshe. Tunda dai tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasar nan ba su yi hani a kan yin amfani da daya daga cikin manyan harsunan kasar nan cikin harkokin mu na yau da kullum ba, sannan kuma kasancewar kundin tsarin mulkin ya tanadi fannin bayar da ilimi tsakanin gwamnatocin kasar nan uku, har ma da kungiyoyi da jama’a daidaiku a zamansu na iya shiga cikin harkokin bayar da ilimi tun daga kan ilmin firamare zuwa sakandare da gaba da sakandare, wato kwalejoji da jami’o’i, to kuwa babu dalilin da zai sanya zuwa wannan lokaci gwamnatocin jihohin Arewa inda nan fannin ilimi ya fi tabarbarewa kuma kullum yake kara samun koma-baya su zauna a kan sai a cikin harshen Ingilishi za a rika koyar da dalibansu karatun boko.
Babban abin la’akari a kan koyar da ilimin boko a cikin harshen uwa shi ne irin yadda a yau kasashen da suka ci gaba a duniya irin su Jamus da Faransa da Sin (China) da Japan da makamantansu, duk ba su kai ga nasara ba, sai da suka rungumi karantar da ilimi a harshen uwa. Don haka ina ganin mu ma a zaman kasa a dunkule ko jihohi a daidaiku ba mu makara ba, za mu iya yunkurawa wajen fara koyar da ’ya’yanmu ilimin boko a cikin harshen uwa mu ga ko irin wannan mummunar koma baya da muke samu duk shekara da mafi yawan dalibanmu ba sa iya cin Ingiishi da Lissafi a jarrabawar kammala sakandare kamar yadda Kudancin kasarmu suke yi. Amma kafin a kai ga haka ya kamata gwamnonin jihohinmu su hada kai a karkashin kungiyarsu ta Gwamnonin Jihohin Arewa su sa a fassara musu littatafan karatu tun daga na firamare har zuwa sakandare da ake koyar da dukan darussa a irin wadannan makarantu (na kimiya ne ko fasaha da sauransu), a cikin harshen Hausa da kuma harshe daya ko biyu da ke biye da harshen Hausa a wadannan jihohi. Haka ma gwamnonin jihohin Kudancin kasar nan da suke da sha’awa za su yi a kan harsunan da suka fi amfani da su a jihohinsu.
Na tabbata cewa batun malamai da za su yi aikin fassara ko koyarwa a makarantun ba zai zama wata matsala ba, babban dai abin da ake bukata musamman daga mahukunta da Allah Ya ba su jan ragamar mulkin jama’arsu a yau bai wuce kyakkyawan kudiri na siyasa da za su iya aiwatarwa ba. Ga sauran ’yan kasa, shugabanni da mabiya, su kuma hadin kai da goyon baya, amma dai na yi imanin cewa ya kamata a jarraba kuma yanzu.