Kafin Buhari ya hau!

A cikin ’yan watannin da suka wuce babu wata haja da take da farin jini da sayuwa a cikin kowace kasuwa a cikin kasar nan irin Buhari! Haja ce da kila ba sai an sha fama ana tallarta ba, domin kuwa haja ce ba irin ta makahon doki ba, wato sha wuyar talla. kila kuma […]

Kafin Buhari ya hau!
Kafin Buhari ya hau!

A cikin ’yan watannin da suka wuce babu wata haja da take da farin jini da sayuwa a cikin kowace kasuwa a cikin kasar nan irin Buhari! Haja ce da kila ba sai an sha fama ana tallarta ba, domin kuwa haja ce ba irin ta makahon doki ba, wato sha wuyar talla. kila kuma wannan karbuwa da wannan haja ta samu shi ya sa ta zama abin nema da tarairaya a kodayaushe, tamkar amarya a wajen angonta.

Irin wannan farin jini da daukaka da zarra da Buhari ya samu a cikin wadannan watanni, duk da cewa ya dade da samun kwatankwacin haka a tsakanin wasu al’ummar kasar nan, ita ta sa yanzu ake ganin da zarar ya hau karagar mulkin kasar nan, nan da ’yan watanni, al’amurran kasar nan za su gyaru, za su inganta, za su kuma daidaitu, su hau bisa saitin da ya dace. Ba ni da haufin hakan zai faru, domin ina da yakinin cewa halin ni-’ya-su da al’ummar kasar nan suka samu kansu na tsawon shekaru da addu’o’in da al’ummar nan ke yi na Allah Ya kawo dauki da alama Allah, Ya amshe su, shi ya sa abubuwa suka canza ta yadda a yau inda a da Buhari ke a matsayin mujiya a cikin kasar nan, yanzu ya zama dawisu. Inda a da ake ganin cewa Buhari ba zai iya shiga ba, bare ya fito ba, yanzu ya zame masa dakin kwana da arerewa. Wannan abu ne mai sanyaya zuciya, mai sa annuashuwa na nuni da cewa lallai Aljanna ta kusa sauka a cikin kasar nan.
Wannan zai iya zama gaskiya idan mu kuma muka amince cewa canjin nan shi muke bukata ba ci gaba da wahala da mulkin zalunci ba. Ke nan mu da ke jiran Allah Ya kai mu nan da ranar 28 ga watan Maris ko kuma ranar 11 ga watan Afrilu mu yi jihadin kawo canji, mu ne canji, domin mu ne masu samar da shi, mu kuma tabbatar da shi. Sai dai kamar yadda na sha fada, nan ke gizo ke yin sakar!
kila wasu su ce, to, wace irin sakar ce gizo yake yi, kuma yaya za a warware ta? Akwai alamun ganewa da matakan bi don gyara. Idan saboda farin jinin Buhari da karbuwa da ya yi a tsakanin al’ummar Najeriya take sa ’yan fashi da makami da ke tsare hanya za su rika fada wa wadanda za su yi wa fashi, “Ku ba mu rabonmu kafin Buhari ya hau,” (kamar yadda wasu kafafen watsa labarai a Intanet suka bayyana) ko kuma masu tukin ganganci a bisa hanya suna cewa “Ai muna yin na karshe ne, kafin Buhari ya hau.” Ko kuma direban bas da ke ajiye mota ba bisa ka’ida ba a kan titi, a yi masa magana ya daina, ya ce “Ai ba komai, nan da watan Mayu ba zan kara ba, domin lokacin Buhari ya hau.” Ko kuma karuwai su rika fadar “Mu tamu ta same mu idan Buhari ya hau.” Ko ma’aikacin gwamnatin da ke fadar “Bari mu ja kaya, kafin Buhari ya hau.”Duk alamu ne da ke nuni da cewa mun san inda ya dace mu gyara, mun kuma san cewa abin da muke yi ba daidai ba ne, muna dai jiran Buhari ya hau ne, sai mu gyara!
Ni a tawa gurguwar fahimtar sai na ga cewa, idan har muna rike da katin jefa kuri’a, muna jiran ranar 28 ga Maris ko 11 ga Afrilu domin mu kawo canji, sa’annan muna yin abin da muke yi na lalaci da barna da almundahana da sauran ayyukan assha, to da alama mun fara shiga motar canjin da matattar taya. Ba laifi ba ne, mu nemi a kawo canji a cikin kasa. Ba kuma laifi ba ne in mun zuba dukkan kwayayenmu a cikin kwarya guda, wato ta Buhari. Ba laifi ba ne in mun raya a zuciyarmu cewa nan da ’yan watanni za a yi ruwan saman canji a cikin kasar nan, saboda haka za mu ci gaba da halin batunci da barna har canji ko mai canjin ya zo! Idan har muna son canji na hakika ya tabbata idan Buhari ya hau, to, mu fara daga yau, mu zama mu ne sinadaran canjin; mu kasance canjin da Buhari zai zo da shi; ya iske mu bisa torokon da tsunamin Buhari zai taho da shi!
Me za mu iya yi domin ganin haka ya tabbata? Akwai abubuwa da dama. Bari na sanya su cikin harshen da wadancan mutanen na baya aka ce suna fada ‘kafin Buhari ya hau!’ Maimakon mu ji ’yan fashi na fadar “Ku ba mu rabonmu kafin Buhari ya hau,” mu ji suna cewa “Mun bar fashi da sata tun kafin Buhari ya hau!” Haka kuma masu tukin ganganci a bisa titi kamata ya yi mu ji suna fadar “Ba mu kara yin tukin ganganci daga yau har Buhari ya hau!” Shi ma direban bas da ke ajiye mota ba bisa ka’ida ba a kan titi, kamata ya yi mu ji yana cewa, “Daga yau ba zan kara ba, har lokacin da Buhari zai hau.” Ita ma karuwa mu ji daga gare ta, tana fadar, “Na bar wannan ta’asa ko kafin Buhari ya hau.” Kai kuwa ma’aikacin gwamnati abin da muke so mu ji daga wurinka shi ne, “Daga yau na bar jan kaya, kafin Buhari ya hau!”
Idan mun yi haka, ni da kai da ke da shi da ku, to, babu wata burga da canji zai yi mana balle a ce ya yi mana barazana. Jira kawai za mu yi Buhari ya hau, mu sha lagwada! Amma wai shin za mu iya?