Kafin Shugaba Buhari ya dawo! (2)
Shin an kawar da gwamnatin APC daga mulki ne ko kuwa Mukaddashin Shugaba, Osinbajo ba gwamnatin canji ce yake jagoranta ba? Me ya sa ba za mu canza ba har kafin Shugaba Buhari ya dawo daga Landan? Tabbas ba a kawar da gwamnatin APC ba, kuma manufofin da aka kafa gwamnatin bisa kan su, suna […]
Shin an kawar da gwamnatin APC daga mulki ne ko kuwa Mukaddashin Shugaba, Osinbajo ba gwamnatin canji ce yake jagoranta ba? Me ya sa ba za mu canza ba har kafin Shugaba Buhari ya dawo daga Landan?
Tabbas ba a kawar da gwamnatin APC ba, kuma manufofin da aka kafa gwamnatin bisa kan su, suna nan har yanzu. Amanna da gwamnatin kuma ba ta kau ba, domin zabarta aka yi, an kuma san ta gaskiya ce. Haka kuma shi ma Osinbajo da ke rikon kwaryar gwamnati kafin Shugaba Buhari ya warke sumul, ya kuma dawo fagen daga, ya aminta da Buhari da tsarinsa. Da shi aka assasa gwamnatin; kuma manufofinta yake bi domin aiwatarwa. Kila inda gizo ke sakar shi ne yadda mutanen Najeriya suka kasa ko suka ki canzawa a cikin tsawon kwana sama da 100 da Buhari baya nan. Wannan shi ne ya kara tabbatar da cewa Buhari ne kaxai mai iya kawo canji, sauran mu ‘yan Najeriya, muna nan muna jira, sai Shugaba Buharin ya dawo, ya hau kan karagar mulki, sa’annan za mu canza halaye ko kyautata al’amurran da ke dakile kasar nan. Wannan ne ya sa na kara tabbatar da zancen da na sha yi na cewa, akwai masoya Buhari da kuma masoyan Buhari. Wani na iya cewa ai ba wani bambanci tsakanin waxannan al’umma biyu!
Akwai bambancin tsakanin irin waxannan mutane. A halin da muke ciki duk wanda ka ji yana ta tunanin ai canji ya kusa dawwama, tun da Buhari ya kusa dawowa daga Landan, to MASOYIN Buhari ne, amma ba masoyin kawo canji ba. Irin su ne ke biye da akida da ruhi da tunani na irin gwamnatin Buhari da irin aljannar da talaka zai shiga a lokacin da Buhari ya warke sarai, ya dawo kan mulki. Ma’ana, irin waxannan mutane ba sa ganin komi sai ci gaban da Buhari zai kawo wa Najeriya in ya dawo daga Landan, ba tare da dubi zuwa ga irin tasu gudunmuwar wajen kawo wa Najeriya canjin ba!
Irin waxannan mutane suna tare da Buhari a kowane irin fasali, amma sun bambanta da MASOYA Buhari. Ta yaya? Waxanda suke MASOYA Buhari, ba irin waxancan gungun da muka yi bayani a baya ba ne! Su MASOYA Buhari, su ne waxanda ke biye da akidojin Buhari da tunanin Buhari da tausayin Buhari da gaskiyar Buhari da kuma kima da xaukaka ta Buhari! Akwai su kuma da dama a cikin kasar nan, wasu ba ma ‘yan siyasar ba ne. Wasu ba kuma ‘yan jam’iyyar APC ba ne! Suna nan jibge! Irin waxannan MASOYA na Buhari ba su kallon Buhari a matsayin ma’asumi. Ba sa tsawwala wa jama’a idan sun kasance masu sayar da tumatir ko doya ko dankali ko shinkafa ko man gyaxa ko kuma in sun haye kan doron mulki! Irin waxannan MASOYA na Buhari za ka gan su cikin kamala da xa’a, ba wai haka nan sakayau ba, kamar dabbobi! MASOYA Buhari ba sa neman kazamar riba! Ba sa cin mutunci ‘yan uwa. Ba sa cin hanci da yin bocar iska a duk inda suke aikin gwamnati! Ba sa kuma yin algushu, idan an ba su kwangila! Ba sa gudun ganganci da kabu-kabu ko wani abin hawa, suna kashe da gurgunta mutane a bisa titi! Ba sa ajiye mota ba bisa ka’ida ba! Ba sa zunxe da gulma da zagin mutane! Ba sa yin dukkan wani abu da ba bisa ka’ida yake ba! Kai in gajarce maka, MASOYA Buhari ba sa nuna rashin xa’a a kodayaushe! MASOYA Buhari masu gaskiya da rikon amana ne, ko Buhari na nan ko ba ya nan!
A halin da muke ciki akwai rikici tattare da nawa tunanin game da MASOYAN Buhari domin kuwa ban sani ba, in MASOYAN Buhari su masu gaskiya da rikon amana ne kamar sa! Shin muna jin cewa za mu iya barin Buharin da muke so ko mu taimaka wa Buharin da muke so ya yi aikin ci gaban kasar da ya kuduri aniyar yi in ya dawo daga Landan xin ko kuwa za mu canza tun yanzu, mu shiga yin aiki tukuru domin kawar da duk wata tambaxa kafin Buhari ya dawo? Ni dai ban sani ba!
Abin da na sani shi ne MASOYA Buhari, ba MASOYAN Buhari ba, su ne za su riki kasar nan da kyau har canji ya samu; kama daga mace mai sayar da man gyaxa zuwa kansila ko minista ko gwamna. Da Buhari ko ba Buhari! Buharin na Landan ko yana Aso Rock ko Daura zaune a gidansa. Lokaci ya yi da za mu sake salon biyayya da }auna da muke nuna wa Buhari, mu gyara!
Mun Kammala