Kagame na Rwanda ya yiwa manyan sojojin kasar 83 ritayar dole
Sa’o’i kalilan bayan juyin mulkin soji a Gabon, shugaba Paul Kagame na Rwanda ya tilasta ritaya ga wasu manyan hafsoshin sojin kasarsa.
Sa’o’i kalilan bayan juyin mulkin soji a Gabon, shugaba Paul Kagame ya sanar da garambawul ga Ma’aikatar Tsaron Kasar wanda ya kai ga tilasta ritaya ga wasu manyan jami’ai.
Sanarwar da rundunar tsaron Rwanda ta wallafa a shafinta na X da aka fi sani da Twitter ta ce, ritayar dolen ta shafi manyan jami’an soji 83.
- Gabon: Janar Brice Nguema zai karɓi rantsuwa a Kotun Koli
- Paul Biya ya sauya jami’an tsaron fadar shi bayan juyin mulkin Gabon
Sanarwar ta ce, tuni shugaban ya sahale karin girma ga wasu kananan jami’ai don maye gurbin wadanda aka yi wa ritayar dolen.
Shugaba Paul Kagame mai shekaru 65 da ya hau mulkin kasar tun a shekarar 2000, a shekarar 2015 ya yi wani gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin kasar da ya sahale masa ci gaba da mulki har zuwa shekarar 2034.