Kaidin mata
Wani mutum ya yi tafiya don ya gano kaidin mata. A kanHanyarsa sai ya yi kicibus da wata mata a gefen wata rijiya. Ya karasa gare ta sai ya ga tana dari-dari da shi. Ya gaishe ta sannan ya ce: “Ina da tambaya ne game da kaidin mata.” Ba ta ce masa komai ba kawai […]
Wani mutum ya yi tafiya don ya gano kaidin mata. A kan
Hanyarsa sai ya yi kicibus da wata mata a gefen wata rijiya. Ya karasa gare ta sai ya ga tana dari-dari da shi. Ya gaishe ta sannan ya ce: “Ina da tambaya ne game da kaidin mata.” Ba ta ce masa komai ba kawai sai ta fashe da kuka, daga nan kuma sai ta kama kururuwa da karfi yadda mutane za su ji. A firgice ya ce mata: “Yaya haka?” Sai ta ce: “Don mutanen gari su zo su kashe ka.” Sai ya ce mata: “To ai ni kuma ban zo nan da niyyar in cutar da ke ba, sai don in tambaye ki, don na gan ki kyakkyawa.” Da ta ji haka sai ta debi ruwa ta watsa wa kanta. Mamaki ya kama shi, ya tambaye ta cewa: “Ke kuwa me ya sa kuma kika yi haka?” Yana cikin maganar ne mutane suka karaso suka tambaye ta abin da ke faruwa. Ta ce: “Wannan mutumin shi ya fito da ni da na fada rijiya.” Nan da nan kuwa mutanen suka kama gode masa, suna yi masa maraba. Da aka natsu sai ya tambaye ta cewa: “Ke kuwa mene hikimar haka?” Ta ce: “To wannan shi ne kadan daga cikin kaidin mata. Da na so, da yanzu an kashe ka. Da ban so ba kuwa ga shi ana ta yi maka godiya mai yawa.”
Daga Muhammed Jungudo, 07034924275