ka’idojin mu’amala da “Password” (3)
Dalilan Amfani da “Password” Kamar yadda wuraren shigar da “Password” suka bambanta, haka ma manufofi da dalilan masu amfani da “Password” suka bambanta, suka nau’anta, sannan suka yawaita. Akwai mutum guda mai “Password” 20! Wani yana da 10! Wani “Password” dinsa duk ba su shige 5 ba, wani 3, wani 2, wani kuma, kamar fitilar […]
Dalilan Amfani da “Password”
Kamar yadda wuraren shigar da “Password” suka bambanta, haka ma manufofi da dalilan masu amfani da “Password” suka bambanta, suka nau’anta, sannan suka yawaita. Akwai mutum guda mai “Password” 20! Wani yana da 10! Wani “Password” dinsa duk ba su shige 5 ba, wani 3, wani 2, wani kuma, kamar fitilar mota, “Password” dinsa kwara daya ce rak. Me ya sa aka samu wannan bambanci? Hakan ya samo asali ne daga manufa da dalilan mai “Password” din. Wadannan dalilai dai masu bincike na kwakwaf a fannin kimiyya da fasahar sadarwa na zamani sun haddade su zuwa bangarori ne kamar haka:
Mu’amala da Imel
Masu amfani da “Password” suna yin hakan ne don samun isa zuwa ga sakonninsu da ke akwatin wasikar Imel dinsu. Wadannan su ne rukunan mutane da suka fi yawa cikin masu amfani da “Password” a duniya baki daya. Domin bincike ya tabbatar da cewa akwai mutane miliyan dubu biyu da dari biyar (wato biliyan biyu da rabi kenan), masu dauke da akwatin Imel ya zuwa karshen shekarar 2014! A duk shekara ana aikawa da sakonnin Imel da adadinsu ya kai biliyan dubu casa’in, wato tiriliyon casa’in kenan (90 trillion)! A duk dakkka guda ana aikawa da sakonnin Imel da adadinsu ya kai miliyan biyu da dubu dari takwas (2.8 million). Dukkan wannan adadi na masu Imel na nuna cewa lallai akwai “Password” na Imel kadai da ya kai wancan adadi na masu mallakar Imel kenan a duniya. Dankari! Wannan manufa na cikin manufofin mallakar “Password” da ya fi kowanne karfi da tasiri a duniya.
Mu’amala da Kwamfuta
Kusan dukkan masu mu’amala da kwamfuta a duniya suna shiga ne bayan sanya “Password” a kofar shiga. Kadan ne cikin mutane suke shiga cikin kwamfuta kai tsaye ba tare da “Password” ba. Dalili kuwa shi ne, a yanzu duniya ta fadaka kan abin da ya shafi kariyar bayanai a kwamfuta da sauran hanyoyi da na’urorin sadarwa. Duk wata kwamfuta da ke dauke da Gidan yanar sadarwa a matsayin Uwar Garke (Serber), tana da “Password” rubi biyu ko ma uku. Na farko wanda za a shigar idan aka zo shiga kwamfutar (Log In Password), na biyu wanda za a shigar idan aka zo shiga zangon sadarwar da kwamfutar ke baiwa bayanai (Network Log In Credentials), na uku kuma wanda za a shigar idan aka zo loda mata bayanai a shafukan yanar sadarwar da masu ziyara ke mu’amala da su. Wannan adadi ne mai yawa, domin a shekarar da ta gabata (2014) an kiyasta cewa akwai ire-iren wadannan kwamfutoci masu dauke da gidajen yanar sadarwa na Intanet kadai guda biliyan biyu.
Bayan wadannan kwamfutoci masu dauke da gidajen yanar sadarwa, akwai ire-irensu masu dauke da bayanai kadai, wadanda ba a jone suke da Giza-gizan sadarwa na duniya ba, wato: Network Serber. Wadannan su ne ire-iren kwamfutocin manyan kamfanonin duniya wadanda ke dauke da bayanai kan ayyukansu na cikin gida. Su wadannan Allah kadai ya san adadinsu. Domin kamfanin HP kadai, mai kera kwamfutoci a duniya, yana da kwamfutoci sama da 800, a kkyasin shekarar 2012! Kuma dole ne suna dauke da “Password” dinsu. A takaice dai, manufa ta biyu ita ce bukatar amfani da kwamfuta kai tsaye, don sarrafa bayanai ko wasu manufofin daban kuma.
Mu’amala da Manhajojin Kwamfuta
Akwai manhajojin mu’amala na yau da kullum wadanda kafin ka fara amfani da su dole sai ka shigar da “Password.” Ire-iren wadannan manhajoji sun kasu kashi biyu; akwai wadanda ke jone da Intanet zalla, don ba ka damar sadarwa da wasu da ke wata uwa duniya, akwai kuma wadanda ke girke a Gajeren Zangon Sadarwa (Local Area Network) da ke kamfanoni ko hukumomi. Wadanda suka shafi Intanet zalla sun hada da manhajar hira na Facebook (Facebook Messenger), da manhajar hira na Yahoo! (Yahoo Messenger), da manhajar Skype da dai sauransu. Wadannan manhajoji ne da ke sauke a kan kwamfutarka ko wayarka ta salula, amma ba za ka iya amfani da su ba sai ka jonu da Intanet, sannan ka shigar da suna da kalmar izinin shiga (“Username” and “Password”).
Kashi na biyu su ne waddnda ke Gajeren Zangon Sadarwa da ake amfani da su wajen ayyukan ma’aikata ko ofis, don tara bayanai na kwastoma ko kuma bincike da dai makamantansu. Ire-iren wadannan sun hada da manhajar Oracle, da manhajar Lync da ake amfani da ita wajen sadarwa tsakanin ma’aikata dake ma’aikata guda. Kamfanin Microsoft ne yake da wannan manhaja. Wannan ke nuna mana cewa ashe ba dukkan manhajojin kwamfuta ba ne kawai za ka yi alkafira ka fada ciki kuma ka kama amfani da ita ba, akwai wadanda sai ka shigar da “Password” kafin a ba ka damar yin hakan.
Mu’amala da Fasahar Intanet
Daga cikin dalilan da ke sa mutane su bukaci “Password” akwai bukatar mu’amala da fasahar Intanet don fa’idantuwa da wasu bayanai na musamman da ke wasu mahallai a giza-gizan sadarwa na duniya. A asali da kuma ka’ida, ba dole bane sai kana da “Password” kafin ka iya shiga da mu’amala da bayanan da ke Intanet. A takaice ma dai, kashi casa’in cikin dari na bayanan da ke Intanet ba sa bukatar “Password” kafin mai ziyara ya fara amfani da su. To amma akwai wasu wurare da mai ziyara zai ga bayanai masu gamsarwa, wadanda ba zai iya wuce su ba. Da zarar ya bukata za a ce masa: “Register,” ko “Log In”, ko kuma “Are you registered? If no, then sign up,” ko wani abu makamancin haka. Wannan zai tilasta masa yin rajista a wannan mahalli, da samun “Password” na musamman don wannan mahalli.
Bayan haka, akwai zaurukan hira da majalisun tattaunawa (Chatrooms and Usergroups) wadanda ke zankame da ilimi mai dimbin yawa ga wanda ya san abin da yake nema. Ire-iren wadannan mahallai dole sai ka yi rajista a shafin Gidan yanar kafin a ba ka izinin shiga. Kwanakin baya wani Farfesa ke sanar da mu cewa akwai wani zauren tattaunawa a Intanet, wanda ko kudi yana iya biya don kawai ya zama mamba, saboda fa’idar da ke cikin zauren. Ka ga wanda ya fadi zance irin wannan, don ka ce masa ya yi rajista kadai kafin ya samu shiga zauren, abu ne mai wahala a gare shi? Ko kadan. Don haka, wannan na daya daga cikin dalilan da ke sa a mallaki “Password” a dole.
Shiga Gajeren Zangon Sadarwa (LAN)
Galibin ofisoshi na hukuma da ma’aikatu da kamfanoni suna da Gajeren Zangon Sadarwa (Local Area Network – LAN) wanda dukkan kwamfutocin da ke ma’aikatar ke jone a jiki. A matsayinka na ma’aikaci a wannan ma’aikata ko hukuma, duk kwamfutar da ka ke amfani da ita tana jone ne da wata Uwar Garke (Serber) da ke girke. Wannan Uwar Garke na dauke ne da sunayen dukkan ma’aikatan ofishin, da adireshinsu na Imel wanda ma’aikatar ta ba su. Da zarar ka kunna kwamfutarka ta Ofis, nan take za a budo maka inda za ka shigar da “Password” dinka. Sai ka yi haka sannan ma za ka samu damar iya mu’amala da kwamfutar. Ba wannan kadai ba, hatta Intanet idan ka tashi shiga, sai ka yi amfani da Suna da Kalmar izinin shigarka (“Username” and “Password”) kafin ka iya riskuwa ga giza-gizan sadarwa na duniya. Kenan ashe mu’amala da sauran kwamfutocin da ke wani Gajeren Zangon Sadarwa dole yana bukatar “Password”. Idan a ma’aikata ce ko hukuma, su za su ba ka adireshin Imel sannan ka zabi “Password” din da kake bukata, idan ka tashi canza wanda suka ba ka kenan.
Saye da Sayarwa a Intanet
Daga cikin dalilan mallakar “Password” akwai bukatar cinikayya a Intanet. Idan ka je wani shafin kasuwanci don sayen wata haja, dole za a bukaci ka yi rajista a shafin. Yin rajistan shi zai samar maka da “Password” wanda da shi masu shafin za su rika tantanceka idan ka shigo don aiwatar da wani sha’ani. Haka idan kaine mai tallata hajojin, dole kana da suna da kalmar izinin shiga na Gidan yanar sadarwarka, da kuma kamfanin da ke maka dillancin karbar kudaden da masu sayan hajarka ke bayarwa don mallakar hajar. Wannan kam dole ne gare ka mallakar “Password,” kuma daya ne daga cikin dalilan da ke sa a mallaki “Password” a bisa tilas.
Mu’amala a Dandalin Abota
A zamanin yau babu abin da ke daukar hankulan mutane masu mu’amala da fasahar Intanet a duniya, musamman matasa, irin Dandalin Abota, wato: “Social Network,” ko “Social Media.” Wurare ne da samari da ‘yan mata da matasa da manya da dattawa maza da mata ke aiwatar da sadarwa don sanayya, ko kasuwanci, ko sadarwa, ko kuma abota irin ta yau da kullum. Wadannan dandamali na abota suna dauke ne a gidajen yanar sadarwa wadanda ke kan wasu madaukai na sadarwa a yanayin manhaja da tsarin sadarwar da tsarinsu ya sha karfin bayani a kasida daya. Shahararru daga ciki sun hada da Facebook, da Twitter, da MySpace, da Youtube, da bimeo, da sauran ire-irensu.
Alkaluman bayanai sun tabbatar da akwai mutane sama da biliyan daya masu amfani da wadannan wuraren shakatawa a duniya a yau. Kamar yadda bayani ya gabata, ganin wadannan wurare na dauke ne a kan gidajen yanar sadarwa, wadanda ke dogaro da wasu manhajoji na sadarwa, kuma sun shafi bayar da bayanan duk mai sha’awar shiga, wannan ke tilasta samar da hanyar tantance dukkan mambobin da ke da rajista a wadannan wurare. Don haka, ba zai taba yiwuwa ba ka ji wani ya ce maka yana da shafi a Dandalin Facebook amma kuma bai mallaki Suna (“Username”) da kalmar izinin shiga (“Password”) ba. Babu abin da yaf i zama tilas irin mallakar wadannan abubuwa guda biyu. In kuwa haka ne, ashe dalili ne babba ga duk wanda ke son shiga ko yin rajista a ire-iren wadannan wurare da ya mallaki “Password” don yin hakan.
A mako mai zuwa in Allah Ya kaimu, bayanai na nan tafe kan abin da ya shafi siffofi da dabi’u da kuma ka’idojin “Password”.