ka’idojin mu’amala da “Password” (4)
Yadda Muke Zaban Password Bayan bayani kan dalilan da ke sa mutane su mallaki “Password” da mai karatu ya karanta a baya, zai dace mu ga irin yadda muke zabar “Password” a halin yanzu. Wato, a matsayinmu na masu mu’amala da hanyoyi da kayayyakin sadarwa na zamani masu bukatar “Password”, ta yaya muke zabar “Password”? […]
Yadda Muke Zaban Password
Bayan bayani kan dalilan da ke sa mutane su mallaki “Password” da mai karatu ya karanta a baya, zai dace mu ga irin yadda muke zabar “Password” a halin yanzu. Wato, a matsayinmu na masu mu’amala da hanyoyi da kayayyakin sadarwa na zamani masu bukatar “Password”, ta yaya muke zabar “Password”? Wannan tambaya tana da mahimmanci musamman idan muka yi la’akari da yawaita da kuma maimaituwar mu’amala da muke yi da wadannan na’urori. Kadan ne cikin masu mu’amala da su wadanda za a iya kebancewa da ba su mallaki “Password” ba. Amma kashi 90 cikin 100 za ka samu sun mallaka, musamman wadanda ke amfani da wayar salula wajen shiga shafukansu da ke dandalin abota irin su: Facebook da Twitter da Youtube da sauransu.
Kasancewar “Password” wani abu ne da dole sai ka shigar kafin a ba ka damar aiwatar da abin da kake son aiwatarwa, ya sa dole ga mai shi ya haddace shi. Tun da kuwa ya shafi hardacewa ne, ba kowa ke iya hararo abin da ya haddace lokaci guda ba, musamman idan ba yawan ta’ammali yake yi da shi ba. Misali, mutumin da ba ya amfani da “Password” dinsa sai sau daya a mako, zai fi saurin mancewa idan aka hada shi da wanda a kullum sai ya shigar da “Password” dinsa a shafi don samun shiga. A bangare na biyu kuma, akwai dalilan mantuwa. Wasu duk gajartan “Password” dinsu suna iya mancewa, a yayin da wasu kuma duk tsawonsa, zai yi wahala ka ga sun mance. Wadannan dalilai ne guda biyu da ke taimaka wa masu ta’ammali da “Password” wajen zabarsa; mai tsawo ne ko gajere, mai saukin haddacewa ne ko mai tsauri.
Galibin masu zabar “Password” sun fi yin amfani da sunaye. Ko dai sunansu, ko na mahaifansu, ko ‘ya’yansu, ko wasu daga cikin danginsu. Wadannan su ne kaso mafi yawa daga cikin masu amfani da sunaye a matsayin “Password”. Mata: ‘yan mata, da matan aure, da zawarawa musamman a Arewacin Najeriya, na cikin wannan rukuni. Masu kokari daga cikinsu ne ke kara lamba ko lambobi a gaban sunayensu don mayar da shi “Password”. Misali, kana iya ganin “Password” kamar haka: “jummai1” ko “hadiza21” ko “hajiya” ko “jummala” ko “talatu” ko “ibrahim00” ko “baballe” ko “ainau1” ko “zariya” ko “kanondabo” ko “katsina” ko “birninshehu”, duk a matsayin “Password.” Bahaushe dan Dandatsa (Hacker) ba zai sha wahala ba wajen sace ire-iren wadannan “Password” din, saboda saukinsu da zamansu “gama-gari.”
Wasu kuma su kan yi amfani da lambobi ne zalla. Misali, kwanan watan haihuwarsu, ko lambar wayarsu, ko lambar gidansu, ko lambar motarsu, ko su jirkita lambar wayarsu daga karshe zuwa farko, ko su cire lambobi uku na farkon lambarsu su bar sauran, da dai sauran dabaru, duk a matsayin “Password.” A wasu lokuta kuma su kan yi amfani da lamba daya zuwa goma (1 – 10) a matsayin “Password.” Wasu kuma su yi amfani da lamba daya zuwa shida ko bakwai ko takwas, duk dai a matsayin “Password.”
Idan muka koma bangaren harkokin rayuwa ma mutane kan yi amfani da bayanan da suka dangancesu ko suke sha’awa ko so, don mayar da su “Password.” Misali, a addinance, galibin daliban ilimin addini musamman, da mata, da matasa kan yi amfani da kalmomi irin su: “yaasalaam” da “assalamualaikum” da “yaaAllah” da “subhaanallah” ko “alhamdulillah” ko wata kalma makamanciyar wadannan. A wani bangaren kuma wasu kan yi amfani da sunayen gwarazansu a rayuwa, kamar a fagen addini ko fina-finai. Ba abin mamaki ba ne ka ga matashi ko matashiya ta sa “Password” mai suna “alinuhu” ko “sanidanja” ko “safiyamusa” ko ma sunan fim na musamman, kamar: “karni2” ko “masoyanzamani” ko “katanga” ko wani suna makamancin hakan.
Wasu kuma kan yi amfani da kalmomin turanci da suka shafi muradansu a matsayin “Password.” Wannan ya fi shahara a bangaren ‘yan mata da ke soyayya da samarinsu. Bai sayi wuri ba ka ga “Password” din mace a matsayin: “myheart” ko “mylobe” ko “ineedyou” ko “iwantyou” ko kuma, a mafi yawancin lokuta, kana iya cin karo da mafin girman suna: “sweetheart” ko “sweetapples” ko “mycutie” da dai sauransu. Babban abin dariya, wasu kalmomin “Password” din ma’anarsu sai wanda ya sa su. Kana iya cin karo da “Password” din matashi kamar su: “londonguy” ko “followme” ko “jirginmasoya” ko kuma “fezbuk”, duk akwai su. Wani lamarin sai ya ba ka dariya. daya daga cikin kalmomin da aka fi amfani da su a baya a duniya baki daya ita ce kalmar: “password” ita kanta.
Daga bayanan da suka gabata, za mu ga cewa galibin mutane suna zabar “Password” ne ba tare da la’akari da tsaro ba, ko mahimmancin samun “Password” mai tsauri ba. Babban dalili shi ne, tun da dole ne sai da “Password” ake shiga shafi ko samun riskar nau’in bayanan da ake so, shi ya sa mutane ke kaffa-kaffa wajen zabar abin da yake mai sauki a gare su. Nan gaba za mu fahimci hadari ko kuskuren da ke tattare da hakan, amma kafin nan, ga bayani kan ka’idojin da ke dauke da siffofin “Password” musamman a cikin wannan zamani da muke ciki.
Ka’idoji da Siffofin “Password”
Saboda matsaloli da aka yi ta samu a baya, tun bayyanar tsarin “Password” zuwa yau, duniyar fannin sadarwa ta yi wa kanta kiyamullaili, inda ta fara neman hanyar kariya daga sake aukuwar abubuwan da suka auku a baya. Nan gaba mai karatu zai ga irin badakalar da ta uyi ta faruwa a baya, a sashen da zan kira: “Tarihin Sace-sacen “Password” a Duniya.” A takaice dai, a halin yanzu an bullo da wasu ka’idoji da dukkan hukumomi da kamfanoni a duniya ke bi wajen tsarawa da kintsa bayanansu, daga ciki har da ka’idojin zabar Imel da Password. Wannan ka’ida ita ake kira: “Password Policy,” wanda ka’ida ce da ke karkashin “Email Policy.”
Dukkan kamfanonin sadarwa na duniya da ke baiwa mutane damar bude shafi ta hanyar Suna (username) da Kalmar izinin shiga (“Password”) a yau suna da ka’idoji na musamman da suke amfani da su wajen yin hakan. Wasu ka’idojin suna da tsauri, wasu kuma masu sauki ne. Wadannan ka’idoji, wadanda ke karkashin tsarin “Email Policy” ne, wato ka’idojin tsarawa, da bayarwa, da adanawa da kuma lura da bayanan da suka shafi harkar Imel na kamfanin kenan. Wadannan tsare-tsare suna taimaka wa kamfanin ne wajen tantance jama’ar da yake hulda da su. Idan hukuma ce ta gwamnati ko masu zaman kansu, hakan na ba ta damar tsara harkar suna da kalmomin izinin shiga da za ta ko take baiwa ma’aikatanta ne. Wannan ke sa dukkan ma’aikatan kamfanin su mallaki tsarin suna da kalmar izinishin shiga mai siffa iri daya.
Wadannan ka’idoji na Imel suna dauke ne da ka’idojin “Password” a daya bangaren. Ba komai wadannan ka’idoji suka kunsa ba illa siffofin da ake so kowane “Password” ya mallaka. Wadannan siffofi kuwa su ne:
Tsawo (Length)
Wannan shi ne iya karancin haruffa ko lambobin da ake so ka sa a matsayin “Password” dinka. Ma’ana, daga haruffan da adadinsu ya kai kaza, misali. A zamanin baya farkon bayyanar Imel, kamfanoni irin su Yahoo da Hotmail da Edcite da American Online sun kayyade tsawon “Password” din da dukkan mai son bude Imel da su zai kayyade ne. A lokacin nan, dole ne tsawon “Password” ya kai haruffa ko lambobi ko hadakar haruffa da lambobi guda shida (6). A haka lamarin yaci gaba har zuwa shekarar 2004 ko 2005, lokacin da kamfanin Google ya samar da manhajar Imel dinsa mai suna: Gmail. A takaice dai, wannan tsari na ka’idojin “Password” ne ke sa kamfani ya kayyade yawan haruffa ko lambobin da za a yi amfani da su a matsayin “Password.”
Hadaka (Combinations)
Abu na biyu cikin ka’idoji da siffofin “Password” shi ne Hadaka; me da me ake so ka hada don samar da “Password” dinka. A baya kamfanonin Imel da sadarwa a duniya ba su damu da wannan ba, kamar yadda ba su damu da yawan haruffa ba sosai. Amma a karkashin wannan ka’ida ta “Password Policy,” kamfanoni kan sa ka’idoji kan nau’ukan haruffan da suke so a yi amfani da su a matsayin “Password.”
Longebity (Tsawon rayuwa)
Rayuwar “Password” wani maudu’i ne mai zaman kansa na bincike a fannin kimiyya da fasahar sadarwa, musamman wajen kariyar bayanai. Abin da wannan ke nufi shi ne, daga lokacin da ka zabi “Password” dinka, kwamfutar da ta karbi “Password” din nan take za ta fara kirga kwanakin wannan kalma da ka shigar. A karkashin wannan ka’ida, dole ne ya zama kowane “Password” yana da iya adadin kwanaki (makonni, ko wata, ko shekara, ko shekaru, misali) da aka deba masa. Da zarar ya rage ‘yan kwanaki (kamar kwanaki 10 misali) lokacinsa ya kare, sai kwamfutar ta fara sanar da kai cewa ka canza “Password” din.
Sai dai wannan ka’ida galibi a kamfanonin hukumomin gwamnati ne ko kamfanoni masu zaman kansu. Amma kamfanonin sadarwa na Imel ba su tilasta wannan ka’ida, sai dai su shawarceka, musamman idan suka fahimci wani na yunkurin sace maka “Password” dinka.
Yanayi (Nature)
Wannan shi ake kira “Nature”, wato yanayin da ake so kowane “Password” ya kasance a ciki. Abin da wannan ke nufi shi ne: nau’ukan abin da kowane “Password” ya kunsa – haruffa, da lambobi, da alamomin rubutu da dai sauransu. Misali, a wasu daga cikin hukumomin gwamnati, ka’ida ce idan ka zo zabar “Password” dole ne ya hada da babban harafi (capital letter), da lamba, da alamomi ko isharorin rubuta na musamman (special characters). Kana iya ganin “Password” haka: “Jamilu@2013” ko “Idris12**” ko “Abdul00%%”, misali. Ba su kadai ba, hatta kamfanonin sadarwa masu bayar da Imel a duniya yanzu sun fara amfani da wannan ka’ida. Babbar hikimar da ke karkashin yin haka shi ne don tsaurara matakai tare da dakile yunkurin masu sace wa mutane “Password” karfi da yaji. Sai dai kuma, wannan tsari yana da nasa matsalar, kamar yadda mai karatu zai gani nan gaba.
Haramtattun alamomi (Prohibited Elements)
Wadannan su ne nau’ukan haruffa ko lambobi ko alamomin rubutu da aka haramta amfani da su a matsayin “Password” ko a cikin “Password.” Wannan ka’ida ce da kowane kamfani ko hukuma take da nata tsari a kai. Misali, a wasu ma’aikatun, haramun ne karkkshin wannan ka’ida “Password” dnka ya kunshi kalmar “password”, ko alamar “@”, misali. A wasu ma’aikatun kuma haramun ne yin amfan da kalmomin turanci da ke cikin kamus, wato: “Dictionary Words,” misali.
Wadannan, a takaice, su ne wasu daga cikin ka’idojin “Password” da ake amfani da su a halin yanzu a duniya.