Ka’idojin rubutun Hausa (1): Gabatarwa
Amincin Allah ya tabbata gare mu. Hakika mutane da dama za su ji mamaki a ce suna Hausawa za a tsaya ana koyar da su ka’idojin rubutun Hausa alhali harshensu ne da suka gada iyaye da kankanni! Sai dai ba a nan gizo ke sakar ba, domin Harshen Hausa kamar sauran manyan harsunan duniya yana […]
Amincin Allah ya tabbata gare mu. Hakika mutane da dama za su ji mamaki a ce suna Hausawa za a tsaya ana koyar da su ka’idojin rubutun Hausa alhali harshensu ne da suka gada iyaye da kankanni!
Sai dai ba a nan gizo ke sakar ba, domin Harshen Hausa kamar sauran manyan harsunan duniya yana daga cikin harsunan Allah Ya tarfa wa garinsu nono, ya samu masana suka tsara masa ka’idojin rubutu.
Kuma abin sha’awar wadannan ka’idoji ba sun tsaya ne kawai a kan rubutun haruffan boko ba, hatta akwai su a rubutun Ajami tun kafin jihadin Shehu Usman Dan Fodiyo.
Wani babban abin takaici shi ne Hausawa da yawa sukan dauka rashin basira ko kwazo ne ke sa mutum ya dauki darasin Hausa a makaranta balle a ce ya yi diploma ko digiri balle a kai ga digirin digirgir a kai.
Da wannan ya sa hatta a makarantun firamare da sakandare dalibai Hausawa ba su cika mayar da hankali su koyi harshen Hausa ba.
Wannan sakaci ya rika tafiya har ta kai a yanzu an kai matsayin da hatta Hausawa wadanda suka yi karatu a manyan cibiyoyin ilimi da jami’o’i, kai har da wadansu malaman jami’o’in da suka karanta Hausar idan suka yi maka rubutu da Hausar sai su ba ka kunya.
Abin da ya sa shi ne tun asali ba su tsaya sun yi wa darasin karatun sha’awa da jin dadi ba, sun dauki darasin ne kawai saboda babu yadda suka iya.
Shi ya sa a yau za ka ga ga littattafai nan na ilimi da adabi da na addini masu kyau da inganci, amma fa wajen kiyaye ka’idojin rubutun Hausa sai su ba ka kunya da takaici.
Hausa ce da ta yi hannun riga da ka’idojin harshen, ta kakkarya Nahawun Hausawa, ta kuma ci zarafin Balaga da Mandakin Harshen Hausa.
Lamarin bai tsaya a nan ba, hatta kafafen watsa labarai na Hausa cike suke da kwamacala da rashin bin ka’idar rubutu.
Gidajen rediyo da talabijin kam ba a ma maganarsu, domin idan mutum ya leka dakunan labaransu ya dauki takardun labaran da suka karanta ya duba, sai ya rantse da Allah wadanda suka rubuta labaran kila ko firamare ba su je ba.
Wannan ya sa ayyukan bunkasa Harshen Hausa da rubutun boko da Turawan Mulkin Mallaka suka faro kusan shekara 80 da suka gabata suke ci gaba da rugujewa.
’Yan ka’idojin da masana suka tsara a zamaninsu ana yi musu karan-tsaye, kowa ya tashi yin rubutu da Hausa sai ya yi rubutun Hausar yadda ya ga dama kai ka ce ba ta da ka’idoji.
Irin wadannan ka’idoji da ake kakkaryawa a yayin rubutun Hausa da a ce Harshen Ingilishi ake yi wa haka, za ka ga mutane suna ta caccakar marubucin suna yayata shi a shafukan sada zumunta suna nuna bai iya Ingilishi ba.
Amma Hausa da yake marainiya ce ba ta da uwa, ba ta da uba, sai kowa ya yi mata hawan kawara ya rubuta ta yadda ya ga dama babu mai damuwa saboda ai Hausa ce!
Matsalolin da ake fuskanta wajen karya ka’idojin rubutun Hausar sun hada da rashin dacewar abin mallaka da mamallaki da rashin daidaiton adadi lamiri.
Misali sai ka ga mutum ya rubuta ‘Shafukan sada zumunta ya cika da sako,’ maimakon ‘Shafukan sada sun cika da sako.’
Sauran wuraren da ake karya ka’idojin rubutun sun hada da wuraren da suka kamata a rarraba kalmomi sai ka ga an hade su, inda kuma ya kamata a hade su sai ka ga an rarraba su.
Akwai kuma rashin yin amfani da manyan bakake a wuraren da suka wajaba.
Kai babu mamaki ka ga wakilin jarida ya rubuta farkon sunansa da karamin baki, haka sunan garin da yake aiki ko sunan wata sananniyar makaranta ko hukuma ko unguwa da makamantansu.
Yadda lamarin yake shafar ayyukan watsa labarai tare da dora nauyin mafiya yawan ayyukan a kan ma’aikatan da ke hedkwatocin gidajen jaridun ya sa jaridu da a baya-bayan nan ake dogaro da su wajen samun Daidaitacciyar Hausa sun fara komawa kamar littattafan Adabin Kasuwar Kano (a gafarce ni Farfesa Ibrahim Malumfashi), inda kowa ke rubuta abin da ya ga dama.
Wannan hali ya sa muka yi ta yunkurin fara gabatar da darasi kan ka’idojin rubutun Hausa a wannan jarida.
Fatarmu wannan fili ya sake zaburar da malamai da masana Hausa su motsa su dora daga inda magabata suka tsaya wajen gyara da tabbatar da ana aiki da ka’idojin rubutun Hausa.
Za mu karbi gyara kan duk inda wani ya ga mun yi kuskure, kuma muna maraba da gudunmawar da wani ko wadansu za su gabatar mana don amfani makaranta.
Daga Salihu Makera – [email protected]