Kainuwa
BASHIR YAHUZA MALUMFASHI (08065576011) ya gabatar da wannan waka a ranar Alhamis 24-06-1438BH = 23-03-2017, a yayin gudanar da wani taro da aka shirya wa ’yan jaridar Shoshal-Midiya domin tantance ayyukan da Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya gudanar a cikin shekara biyu da hawansa mulki: Gwamnanmu Masari, Aikinka nazari, Ba ka garari, […]
BASHIR YAHUZA MALUMFASHI (08065576011) ya gabatar da wannan waka a ranar Alhamis 24-06-1438BH = 23-03-2017, a yayin gudanar da wani taro da aka shirya wa ’yan jaridar Shoshal-Midiya domin tantance ayyukan da Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya gudanar a cikin shekara biyu da hawansa mulki:
Gwamnanmu Masari,
Aikinka nazari,
Ba ka garari,
Nasara ka zam damkewa.
*
Dankama har Damari,
Ba ka kurari,
Ba ka nasari,
Aikinka kake makawa.
*
Rika riko mai tsauri,
Ka doke tsirari,
Ba su yin tasiri,
Kai ne mai Katsinawa.
*
Masu adawa kuri,
Sun yo tsiriri
Su ne ’yan miriri,
Kai ne mai Daurawa.
*
Dallatu uban taurari,
Ka fi gaban jariri,
A daji akwai mariri,
Aminu mai Katsinawa.
*
Matawallen Hausa kirari,
Ka fi gaban kanari,
Ba ka aikin kari,
Amanar mai Daurawa.
*
Amanar Baba Buhari
Zuciya fara sukari
Ba ka alfahari,
Allah kake rokawa.
*
Farin ruwa mai tsari,
Kana kashe kissa tari,
Ga magabta sanya mari,
Adalci kake aikawa.
*
kyale wancan mai sauri,
Maciji bar shi da sari,
Sullutu o’e Bagwari,
Ka wuce wulakantawa.
*
Zaman lafiya ne jari,
Katsi gidanmu a fari,
Daura gandun alheri,
Sawaba muke nemawa.
*
Mulkinka Aminu Masari
Ka aika ba wadari
Allah ne wutiri.
Jagora Yake badawa!