Kakar Obama ta isa Saudiyya don yin Umara

A shekaranjiya Laraba ne kakar Shugaban kasar Amurka Barack Obama ta isa birinin Makkah na kasar Saudiyya domin gabatar da aikin Umara, cikin wadanda suka ruba mata baya har da kawun shugaban da kuma dan uwansa. Lokacin da take ganawa da manema labarai, Kakar tasa mai suna, Sara Umar ta kara jaddada muhimmanci Manzon Allah […]

Kakar Obama ta isa Saudiyya don yin Umara
Kakar Obama ta isa Saudiyya don yin Umara

A shekaranjiya Laraba ne kakar Shugaban kasar Amurka Barack Obama ta isa birinin Makkah na kasar Saudiyya domin gabatar da aikin Umara, cikin wadanda suka ruba mata baya har da kawun shugaban da kuma dan uwansa.

Lokacin da take ganawa da manema labarai, Kakar tasa mai suna, Sara Umar ta kara jaddada muhimmanci Manzon Allah (SAW), inda ta ce rayuwarsa tana koyar da hakuri da juya da kuma kaucewa tsahe-tashen hankula.
Sara tana ziyarar ne tare da danta Saeed Obama kawun Shugaba Obama da kuma wani jikanta mai suna, Mousa Obama. Har ila yau, ta yaba wa gwamnatin kasar saboda aikin fadada Masallatan da ake ci gaba da yi.
Daga nan ta ziyarci wurare masu alfarma da ke gundumar Naseem da ke birnin Makkah, inda ta yi sa’o’i biyu a nan. Ta ce: “Ina matukar farin ciki da ziyarta wannan wuri, wannan wuri yana nuni da yadda addinin Musulunci ke ci gaba a zamanance da kwararen hujjoji a kimiyyance.