Kalaman Bayyana Soyayya

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Ina mana marhabin da sake haduwa cikin wannan fili. A wannan makon za mu karasa bayani kan yadda siffofin kalaman soyayya suke. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga masu bukatarsa, ya kuma amfanar da su, amin.3. Kalaman goyon baya da karfafa gwiwa: Irin wadannan kalamai, […]

Kalaman Bayyana Soyayya
Kalaman Bayyana Soyayya

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Ina mana marhabin da sake haduwa cikin wannan fili. A wannan makon za mu karasa bayani kan yadda siffofin kalaman soyayya suke. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga masu bukatarsa, ya kuma amfanar da su, amin.
3. Kalaman goyon baya da karfafa gwiwa: Irin wadannan kalamai, lokaci da kuma yanayin zamantakewa ke kawo su, don haka sai a kiyaye lokacin da ake bukatar furta irin wadannan kalaman, kamar lokacin da ake fuskantar wani muhimmin abu a rayuwa, mutum na bukatar kalaman karfafa gwiwa a irin wannan lokacin. Misalin haka shi ne, farkon lokacin da aka fara saukar da wahayi ga Manzon Allah SAW, da ya dawo gida a firgice, a nazarci irin kalaman da matarsa Uwar Muminai ta furta masa don kwantar masa da hankali da kara karfafa masa gwiwa: “Allah ba Zai kaskantar da kai ba, domin kai mai sada zumunci ne, kuma kana taimakon miskinai da marasa galihu, sannan kana kyautata wa bakinka, kuma kana taimakon mabukacin taimakon.” Sannan ta bi bayan wannan kalaman karfafawar da aikin sadaukarwa, don kara karfafa masa gwiwa a wannan lokacin mai matukar muhimmanci a rayuwarsa SAW.
4. Kalaman Godiya: Yawan yi wa juna godiya tsakanin ma’aurata na kara kusantar da kuma inganta auratayyarsu. Don haka yana da matukar alfanu ma’aurata su rika bayyana wa juna godiyarsu; a kalamance da kuma a aikace. Kuskure ne mai girma ya kasance ma’aurata su rika kin gode wa junansu kan abubuwan da suke yi wa juna da suka zama al’ada a gare su. Duk wani aiki na sadukarwa yana bukatar nuna godiya daga wanda aka yi wa aikin nan, kasancewarsa aiki na al’ada ba ya hana a rika nuna godiyarsa; don haka ita ma godiyar sai a mayar da ita al’ada, kamar yadda aikinta yake al’ada. Maigidan da ya dawo gida ya iske shi a gyare tas, ya kamata a take ya bayyanar da godiyarsa ga matarsa, domin wata kila saboda shi kawai ta gyara gidan domin ba ta so ya dawo ya same shi kaca-kaca: “Amma dai wance kin sha aiki yau, na gode da gyara gidan nan da kika yi, Allah  Ya saka miki da alheri.” Gobe ma in ya zo ya iske shi tas ya kara nuna godiyarsa, jibi da gata ma haka, da haka har godiyar ta zamar masa al’ada.
Ya kamata duk lokacin da maigida ya sayo wani abu ya kawo gida, komai kankantarsa to ya kamata uwargida ta gode masa, kuma ta rika gode masa duk lokacin da ya yi mata wata hidima. Hatta in ta tambaye shi zuwa unguwa kuma ya amince mata, to ya kamata ta gode masa, ta nuna jin dadinta sosai. Haka kuma bayan kammala gabatarwa ibadar aure, ya kamata ma’aurata su rika gode wa junansu.
Ga ma’auratan da kalami shi ne yaren soyayyarsu, kalmomin godiya ta al’ada da aka sani ba ya isa wajen bayyana godiya gare su, dole sai an hada da wasu zakakan kalmomi da suka dace da lokaci da kuma yanayin godiyar. Misali: “Kai! Amma wance kin iya gyaran gida wallahi, kullum sai in ga kamar kina canza masa samfuri ne, na gode, Allah Ya bar mini ke matata!”
“Gaskiya maigida ni kullum kara burge ni kake yi saboda ka iya cefane! Komai naka daban ne Wallahi. Na gode kwarai da kyakkyawar kulawarka, Allah Ya kara maka lafiya da arziki masu amfani, amin.”
5. Kalaman Sha’awa: Kalaman zakulo sha’awar juna da kalaman tsunduma juna cikin sha’awa na da matukar muhimmanci wajen inganta lafiyar sha’awar ma’aurata da zakaka dandanon ibadar aure. Ma’aurata za su amfana sosai da yawan koda wasu siffofin jikin junansu, wato kodawa irin ta sha’awa, misali, maigida na iya koda uwargidansa da wannan kalamin: “Siffa da kirar jikinki na dauke mini hankali, suna tsunduma ni cikin wani yanayi na tsananin sha’awa kodayaushe na kalle ki!”
Uwargida kuma na iya yaba wa maigidanta da: “Ina son Idanunka ya maigidana, ba kamar idan na kalli kwayar cikinsu, sukan dimautar da ni cikin kauna da sha’awa.” da sauran dadadan kalamai.
Haka kuma sai su rika yawan yaba iyawa da kwarewar junansu wajen ibadar aure, musamman bayan kammaluwar ibadar aurensu, lokacin ne ya kamata su koda junansu irin wannan kodawa, hadi da karin godiya, ko da kuwa waninsu bai samu yadda yake so wajen ibadar auren ba, kyakkyawan zancensa zai tafiyar da damuwarsa, kuma yawan dadadan kalamai a wannan lokacin wani lakani ne da zai kawo warakar wannan damuwa cikin kankanen lokaci.
Sarrafa murya da garwayata da shau’ukan sha’awa na da matukar muhimmanci wajen kalaman sha’awa, haka sai an hada da sarrafa jiki ya zama cikin yanayin sha’awa da lullube fuska cikin shimfidar sha’awa da kawata launin sha’awa.
6. Kalaman Nishadi: Su ne kalaman zaurance da yawan tsokanar juna da maganganun wasa da dariya, da saka juna cikin nishadi da jin dadin zuciya. Wadannan suna matukar dadada zamantakewar auratayya, kuma suna kore zaman tsami da jin haushin juna. Amma sai a kula kada a rika tonon mutum da munanan kalaman a kan siffa ko dabi’arsa, ko kalaman da ya nuna ba ya son su: kamar maigida ya ce da matarsa ‘ke bukekiyar nan!’ Daga ji cikin sigar wasa ya yi maganar amma kalmar da ya sa ba lallai ba ne ta yi ma uwargida dadi. Amma inda ya ce ‘Ke tsaleliyar nan!’ To ko da ita ba tsaleliyar ba ce wannan kalmar za ta yi mata dadi a rai.
Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.