Kalaman da wasu ke yadawa yana ketare iyaka-Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna takaicinsa dangane da kalaman  da wasu ’yan Najeriya ke yadawa a kafofin sada zumunta inda ya ce suna ketare iya. Buhari ya bayyana takaicinsa ne yayin da yake yi wa ’yan Najeriya jawabi a yau da safe bayan dawowarsa daga jinya daga kasar Birtaniya. “A zaman jinyar da na yi […]

Kalaman da wasu ke yadawa yana ketare iyaka-Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna takaicinsa dangane da kalaman  da wasu ’yan Najeriya ke yadawa a kafofin sada zumunta inda ya ce suna ketare iya.
Buhari ya bayyana takaicinsa ne yayin da yake yi wa ’yan Najeriya jawabi a yau da safe bayan dawowarsa daga jinya daga kasar Birtaniya.
“A zaman jinyar da na yi a birnin Landan, ina bibiyar abubuwan da ke faruwa a gida Najeriya. ’Yan Najeriya mutane ne da ke da karfin halin tattauna lamuransu amma kuma abin damuwar shi ne yadda na lura cewa wadansu kalaman da ake yadawa a kafofin sada zumunta suna ketare iyaka inda suke sanya alamar tambaya ga hadin kan kasarmu. Wannan mataki ne da ya kai mutuka”. Inji shi.
Ya ci gaba da cewa “A shekarar 2003 bayan na shiga siyasa, marigayi Chif Emeka Ojukwu ya zo gidana da ke cikin garin Daura a matsayin bakona na musamman inda muka shafe kwanaki biyu muna tattauna batutuwan da suka shafi kasar nan. Har tsakiyar dare muka rika kai wa muna tattaunawa, daga karshe muka cimma matsaya cewa dole kasar nan ta ci gaba da kasancewa tsintsiya madaurinki daya”.
Shugaban kasar wanda ya jaddada muhimmancin kasar ya yi kira ga ’yan Najeriya kada su bar makiyan kasar su tayar da tarzoma a kasar.
Ya bayyana cewa kowane dan Najeriya yana da ’yancin ya zauna tare da gudanar da kasuwancinsa a duk inda yake so a kasar ba tare da takura ba.
Buhari ya yi kira ga jami’an tsaro kada su bari ci gaban da kasar ta samu a cikin watanni 18 ya zama ya tafi a banza.
Ya bayyana cewa dole kasar ta ci gaba da yakar ta’addanci da masu aikata laifi don mutanen kasar su ci gaba da zama lafiya.