Kalaman kishin Indiya sun jawo wa dan Pakistan hukuncin cin amanar kasa
Wani matashi dan kasar Pakistan da ya rubuta ‘Hindustan Zindabad’ a bangon gidansa da ke Lardin Khyber- Pakhtunkhwa an yanke masa hukuncin amanar kasa, a cewar kafafen yada labaran kasar. Matashin ya rubuta kalaman taken kishin kasar Indiya, wato ‘Hindustan Zindabad,’ don haka aka yanke masa hukuncin cin amanar kasa, kamar yadda kafofin yada labarai […]
Wani matashi dan kasar Pakistan da ya rubuta ‘Hindustan Zindabad’ a bangon gidansa da ke Lardin Khyber- Pakhtunkhwa an yanke masa hukuncin amanar kasa, a cewar kafafen yada labaran kasar.
Matashin ya rubuta kalaman taken kishin kasar Indiya, wato ‘Hindustan Zindabad,’ don haka aka yanke masa hukuncin cin amanar kasa, kamar yadda kafofin yada labarai suka ruwaito.
Sajid Shah ya rubuta kalaman ‘Hindustan Zindabad’ a bangon kofar gidansa da ke yankin Nara Amazi, kamar yadda jaridar Daily Edpresss ta ruwaito daga bakin ’yan sanda.
Wasu mutane suka dauki hoton bangon gidansa a wayoyinsu na alfarma, suka aike da sakon i-mail ga manyan jami’an ’yan sanda, a cewar ’yan sandan.
Kwannan dai aka yanke masa hukuncin cin amanar kasa, a cewarsu.
Wasu mutane a yankin nasu sun ce masa ya goge taken kishin kasar daga bangon don yana cutar da kasarsu, a cewar ’yan sanda.
“Mun kuma yanke matsayar kaddamar masa da hukuncin bisa umarnin da muka samu daga sama, “ inji Jami’in ’yan sanda.