Kalaman Sarki Sanusi kan sace yara sun bar baya da kura

Takaddamar da ta kunno kai bayan da aka bayar da sanarwar gano wadansu yara da aka sace su daga Kano na ta ci gaba da ruruwa, bayan wasu kalamai da Mai martaba Sarki Malam Muhammadu Sanusi II ya furta na cewa laifin iyayen yaran da aka sace ne. Yayin wani jawabi da ya yi a […]

Kalaman Sarki Sanusi kan sace yara sun bar baya da kura

Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II

Takaddamar da ta kunno kai bayan da aka bayar da sanarwar gano wadansu yara da aka sace su daga Kano na ta ci gaba da ruruwa, bayan wasu kalamai da Mai martaba Sarki Malam Muhammadu Sanusi II ya furta na cewa laifin iyayen yaran da aka sace ne.

Yayin wani jawabi da ya yi a wajen wani taro a birnin Kano, Sarki Sanusi ya ce, “Duk yaran nan da ake cewa an sace, kuma ana cewa Sarki bai yi magana ba, mun riga mun yi bayani, tunda aka fara maganar yaran nan na Anacha, muka yi magana da Obi na Anacha, kuma muna sane da halin da ake ciki kuma da binciken da ake yi.”

Daga nan ne Sarkin ya bayyana cewa, “Amma kafin a zo kan wadanda aka ce sun sace mana yara, duk ana ta zage-zage, sun sace mana yara. Mun ji, sun yi laifi. Amma shin wanda ya saci yaron nan cikin gidanka ya shigo ya sace shi? Ko kai ne ka bar danka dan shekara uku ya fita yana yawo a kan titi ba ka ma san inda yake ba? Ni na fada, na san lokacin da aka kama wadansu aka kawo kara gaban Sarki a lokacin cewa na yi da ni nake da gwamnati da duk mahaifansu sai na daure su.”

Sarkin ya kara da cewa “Kuma har na ce a nemi Kwamishinan ’Yan sanda, a bincika shin ba mu da doka ce kan masu watsi da abin da ya zama dole su kula da shi da ake cewa laifin sakaci? Laifi a wajenmu yake, mu ne masu laifi.”

Sarkin ya yi wadannan kalaman ne bayan ce-ce-ku-cen da aka yi ta yi a Kano, game da rashin jin martaninsa kan batun sace yaran na Kano.

A karshen watan Oktoba ne Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta ceto wadansu yara tara wadanda ta ce wadansu mutanen Kudu ne suka sace suka sayar da su a Jihar Anambra, tare da sauya musu suna da kammani.

Kalaman Sarkin dai sun janyo ce-ce-ku-ce inda wadansu ke cewa abin da Sarkin ya fada gaskiya ne, yayin da wadansu ke cewa har cikin gida aka shiga aka dauki daya daga cikin yaran.

Hidaya Salisu Ahmad wata uwa a birnin Kano ta goyi bayan kalaman Sarkin inda ta ce, “Gaskiya wannan maganar ta yi daidai saboda za ka ga idan iyaye suna hayaniya sai a ce wa yaro je ka waje ka yi wasa kuma shekarunsu bai kai su fita su kadai ba,” kamar yadda ta shaida wa BBC.

“A tunanina, a ce wai wannan laifin iyaye ne, wannan kuskure ne saboda wani ya tura dansa makaranta amma an dauke shi,” in ji wani magidanci a Kano.

A bangaren gwamnati kuwa, a ranar 31 ga Oktoba Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da kwamitin bin bahasi kan sace yaran a karkashin jagorancin Mai shari’a Wada Umar Rano.

Tuni kwamitin ya fara zamansa a kotun da ke Miller Road, bayan kira ga iyayen yaran da masu ruwa-da-tsaki domin gabatar da bayanai.