Kalaman tunzuri yayin wa’azi na haddasa kiyayya — Izala

Kungiyar Izala ta jihar ta ja hankali malaman kan amfani da mumbarin wa’azi wajen yada kalaman tunzuri.

Kalaman tunzuri yayin wa’azi na haddasa kiyayya — Izala

Shugaban Kungiyar Izala na Jihar Gombe, Ininiya Salisu Muhammad Gombe, ya gargadi malamai kan amfani da kalaman tunzuri a lokacin tafsirin watan azumi da ke tafe.

Ya ce da yawan wasu da ba darika daya suke da malaman ba, ba lallai su fahimci inda suka dosa ba.

Ya bayyana hakan ne a lokacin taron bita da aka shirya wa malaman kungiyar sanin makamar wa’azi da za su gabatar da tafisiri a watan Ramadan.

“Ku gane munbarin tafsiri ba dandalin fade-fade ko na mayar da martini ba ne, waje ne na wa’azi da jama’a ke halarta domin jin sakonnin da Alkur’ani mai tsarki da hadisan Manzon Allah suke koyarwa,” in ji shi.

Ya ja hankalin malaman da su gane cewar su wakilai ne na Manzon Allah a lokacin da suke kan munbarin wa’azi.

A nasa jawabi,ataimakin shugaban kungiyar, Shielk Usman Isah Taliyawa, cewa ya yi shirya irin wannan taro yana da muhimmanci domin sanin makama saboda a kullum ana son mai wa’azi da mai sauraro ana tafiya tare.

A yayin taron, gwamnan jihar Muhammad Inuwa Yahaya, jan hankalin jama’a ya yi da su guji shiga zanga-zanga saboda tsadar rayuwa.

Gwamnan ya ce zanga-zanga ba mafita ba ce a halin da ake ci, face jajircewa da addu’a domin neman mafita daga Allah.

Gwamnan da ya samu wakilcin sakataren hukumar jin dadin Alhazai na jihar, Sa’adu Hassan, wanda ya yaba wa kungiyar kan hada taron irin wannan.

Sama da malamai 600 ne, suka halarci taron daga kananan hukumomi 11 na jihar.

Tinubu zai halarci taron ƙasashen Larabawa da Musulunci a Saudiyya

Obaseki ya rushe dukkanin muƙarraban gwamnatinsa

HOTUNA: Mayaƙan Lakurawa sun kashe mutum 17 a Kebbi

Mutum 20 sun tsere daga Cibiyar Horar da Nakasassu ta Abuja