Kalli yadda aka yi bikin yayen sojojin Najeriya a COVID-19

A karon farko rundunar sojin kasa ta Najeriya na bikin yayen kananan sojojin kasa a cikin yanayi na COVID-19 wanda ke bukatar sanya takunkumi da kuma bayar da tazara. Ga hotunan da Aminiya ta dauko a yayin bikin wanda shi ne karo na 79 ke gudana a Makarantar Horas da Kananan Sojojin Kasa (DEPOT) da […]

Kalli yadda aka yi bikin yayen sojojin Najeriya a COVID-19

A karon farko rundunar sojin kasa ta Najeriya na bikin yayen kananan sojojin kasa a cikin yanayi na COVID-19 wanda ke bukatar sanya takunkumi da kuma bayar da tazara.

Ga hotunan da Aminiya ta dauko a yayin bikin wanda shi ne karo na 79 ke gudana a Makarantar Horas da Kananan Sojojin Kasa (DEPOT) da ke Zariya, a ranar Asabar 27 ga watan Yuni:

Laftanar Janar Lamidi Adeosun, Babban Jami’i Mai Kula da Tsara Manufofi a Hedkwatar Rundunar Sojin Kasa (a nan ya sara). Shi ne ya wakilci babban bako a taron kuma Babban Hafsan Rundunar Sojojin Kasa ta Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai a wurin bikin.
Sanya takunkumi bai hana ‘yan tawagar ‘yan adujalan kuratan sojojin da ake yayewa cashewa a lokacin faretin ba
Laftanar Janar Lamidi Adeosun a kan mimbari yana karɓar gaisuwa daga kuratan sojojin da ke faretin ban kwana
Wakilin Mai Martaba Sarkin Zazzau, Fagacin Zazzau Alhaji Umaru Muhammad, tare da babban bako Laftanar Janar Lamidi Adeosun
Kuratan sojojin da ake yayewa suna mika gaisuwa yayin faretin ban kwana
Kwamandan faretin yana mika wa bataliyar da ta fi kwazo tuta
Laftanar Janar Adeosun, tare da Kwamandan Barikin Sojoji na Depot da ke Zariya, Manjo Janar Muhammad Sani, a lokacin duba Faritin kuratan sojojin
Laftanar Janar Lamidi Adeosun yana gaisawa da Darakta Janar na Ma’aikatar Kera Motocin Soji Manjo Janar Victor Nzegu
Nan ma Laftanar Janar Lamidi Adeosun da Manjo Janar Muhammad Sani ne suke duba faretin

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50