kalubalantar Indiya Hausa ba daidai ba ne – Illiya mai kaset
Alhaji Sa’idu Iliya dan kasuwa mai sana’ar sayar da fina-finan Hausa a Kalaba, ya kalubalanci masu shirya fina-finan da cewa su yi hakuri ‘mai laya ya kiyayi mai zamani’, domin kyashi da hassada da suke nuna wa fina-finan indiyan Hausa da ake fassara su da harshen Hausa a yanzu sun karbu kuma kasuwarsu take ja […]
Alhaji Sa’idu Iliya dan kasuwa mai sana’ar sayar da fina-finan Hausa a Kalaba, ya kalubalanci masu shirya fina-finan da cewa su yi hakuri ‘mai laya ya kiyayi mai zamani’, domin kyashi da hassada da suke nuna wa fina-finan indiyan Hausa da ake fassara su da harshen Hausa a yanzu sun karbu kuma kasuwarsu take ja ko ina a fadin kasar nan, domin kuwa kamar yadda suka yunkuro a zamanin su suka danne wasu daga cikin shahararrun mawakakan Hausa suka yi hakuri ,to kamata ya yi su ma su dangana.
dan kasuwar ya furta haka ne a hirar su da Aminiya. Ya ce: “Masu fina-fina Hausa suna sukar masu fina-finan Indiya da ake fassarasu da harshen Hausa, ana sayarwa kasuwar su ke ja, su tunafa su ma sun danne sauran mawakan Hausa idan suka tuna a lokacin akwai su marigayi Sani dan indo da Alhaji danmaraya Jos da Marigayi Haruna Uji Hadeja da kuma Musa Gumel , duk suka danne su, kuma suka hakura. Da yake lokacin su ne duk wannan an bar shi, an bar wannan bangaren an dawo nasu, to su ma yanzu lokaci ne nasu ya kare.”
“ Adawa da Indiyan Hausa da suke yi, su dawo su daina wanna ba layin su ba ne. Idan gaskiya suke so, su tafi Legas kasuwar duniya ta Alaba, su je su kama Inyamurai [kabilar ibo] masu buga faya-fayen dbd, wanna ya kamata su yi shi ne suke da hujja, amma wancan su ce za su yi hassada akan Indiyan Hausa wannan ba layin su ba ne,”inji shi.
Da aka tambaye shi hujja ko mai yasa shi yin korafi ganin cewa shi sana’arsa sayarwa ce ta dukan bangarorin fina-finan biyu, sai ya kara da cewa: “Ba hujja ba ce da suke cewa wai fina-finan Indiya na kashemusu kasuwa, su hakura komai da lokacin sa; su tuna fa su ma sun zo sun danne wadanda su ne suka hakura . Don haka su ma suyi hakuri.”
A cewarsa, ba daidai ba ne kalubalantar da ’yan fim ke yi wa masu fim din Indiyan Hausa,indaa karshe ya shawarci bangarorin biyu masu fim na Hausa da kuma Indiyan Hausa kowa ya ci gaba da yin nasa, ba tare da kyarrar juna ba.