Kalubale da nasarorin da aka samu a AFCON 2021
A ranar Lahadin da ta gabata aka kammala Gasar Cin Kofin Afirka ta 2021, inda kasar Senegal ta doke kasar Masar a wasan karshe a bugun fanareti da ci hudu da biyu. Wannan shi ne karo na farko da kasar Senegal ta lashe gasar a tarihinta, duk da cewa shekaru biyu da rabi da ska […]
A ranar Lahadin da ta gabata aka kammala Gasar Cin Kofin Afirka ta 2021, inda kasar Senegal ta doke kasar Masar a wasan karshe a bugun fanareti da ci hudu da biyu.
Wannan shi ne karo na farko da kasar Senegal ta lashe gasar a tarihinta, duk da cewa shekaru biyu da rabi da ska wuce ta kai wasan karshe, inda Aljeriya ta doke ta.
- Murnar AFCON 2021: Gwamnatin Senegal ta ba da hutun aiki
- AFCON2021: A karon farko, Senegal ta daga Kofin Afirka
Sadio Mane ne ya lashe kyautar Gwarzon Dan Wasa na gasar, inda takwararsa Edourd Mendy ya lashe Gwarzon Gola, sannan Vincent Abubakar ya fi zura kwallaye da kwallo 8.
Sai dai kamar yadda yake a duk wata gasa da ake bugawa a duniya ta kasashe da kungiyoyi, ba a rasa nasarori da kalubale.
A gasar ta AFCON,wadda ya kamata a yi a 2021 amma annobar COVID-19 ta hana, duk da cewa ba a rasa matsaloli da aka fuskanta daga farkonta zuwa karshe, an samu nasarori da dama.
Aminiya ta zanta da fitaccen mai sharhi kan wasanni, Mohammed Abdu, wanda aka fi sani da Mamman Skipper, wanda ya samu damar halartar gasar a Kamaru, inda ya yi cikakken bayani kan nasarorin da aka samu da sauransu.
Ko Senegal ta nuna alamar lashe gasar?
Da yake bayani kan alamun nasara, Mamman Skipper cewa ya yi, “Wasa ya yi kyau matuka, an taka leda sosai.
“Da ma kasar Senegal ce ta daya a Afirka kuma ta 20 a duniya, ita kuma Masar ita ce ta shida a Afirka, ta 44 a duniya a iya taka leda.
“Tun kafin a kai ga bugun fanaretin, ’yar manuniya ta nuna cewa Senegal za ta yi nasara, ganin Sadio Mane ya barar da fanareti tun a farko.”
Ya kara da cewa, “Wannan abin alfahari ne ga Senegal a karon farko ta lashe gasar – sau 16 da ta buga gasar, kuma sau uku tana zuwa wasan karshe, kuma karo na biyu a jere.”
Sai dai Skipper ya ce bai yi tunanin Senegal za ta iya lashe gasar ba, inda ya ce, “Gaskiya ban ba Senegal kofin ba a farko ganin yadda suka fara da tafiyar hawainiya.
“Duk da cewa su suka ja rukunin, amma da kyar suka doke Zimbabwe da daya mai ban haushi a wasan farko, sannan suka yi canjaras Guinea, sannan Malawai, inda suka ja rukunin da maki biyar.
“A zagaye na biyu, sun ci Cape Verde da biyu babu sannan a wasan dab da na kusa da karshe suka ci Equatorial Guinea da ci uku da daya, sai a na kusa da karshe suka doke Burkina Faso. Sai daga baya ne nasarar ta riko dawo wajensu.
“Kafin nan ma sun rika shan suka akan cewa ba sa kokari. Shi kansa kocinsu Aliou Cisse ya sha suka. Sun kai wasan karshe a 2019, ba su samu nasara ba, shi ya sa aka rika ganin wannan ma ba za ta canja zani ba. Sai kuma suka bayar da mamaki, amma gaskiya ban ba su nasara ba.”
Masu horar da ’yan wasan kasashen Afirka daga Afirka
Wani abin da ya dauki hankalin masu kallo shi ne yadda kasashe da dama suka zo da masu horar da ’yan wasa ’yan gida, inda daya daga cikinsu, Aliou Cisse ya jagoranci kasar Senegal wajen samun nasara a gasar.
A game da wannan, Mamman Skipper cewa ya yi, “Ai kasashe 15 a cikin kasashen 24 da suka zo da koci ’yan gida suka zo. Misali Najeria, da Senegal da Comoros da Guinea-Bissau da Cave Verda da Aljeriya da Saliyo da Equatorial Guinea da Mali da Burkina Faso da Tunisa da Malawai da Habasha.
“Ka ga a ce an samu koci 15 cikin 24 duk ’yan gida ne alama ce da ke nuna cewa kasashen Afirka sun yarda cewa na gidan za su iya, kuma ga alama nan Aliou Cisse ya kawo musu nasara a karon farko ganin an yi hakuri an yi juiriya bayan gasar 16 da suka buga.
“Wanna ke nuna idan aka yi amanna da masu horarwar na gidan aka ba su abin da ake bukata, lallai za a kai ga gaci.”
Matsaloli da aka fuskanta a gasar
A game da kalubale da aka fuskanta a gasar, Mammam Skipper cewa ya yi, “Gaskiya an samu matsaloli, amma kasancewar wasa ne na guje-guje, dole a rika samun kura-kurai. Ko a Turai ana samun haka.
“Na san akwai alkalin wasa da ya hura tashi lokaci bai yi ba. Akwai kuma inda aka rika samun yawan duba na’urar VAR.
“Sai dai duk da haka akwai alkalin da ya kafa tarihi dan kasar Gambiya Bakary Papa Gassama da ya hura wasa minti 120 ba tare da duba na’urar VAR ba, kuma ba a same shi da kuskure ba.”
Abubuwan da za su dade ba a manta ba
Gasar ta zo da ba-zata da dama, inda da Aminiya ta tambayi masanin wasannin ko me zai ce, sai ya ce, “Ka ga kamar kasashen nan guda biyu: Comoros da Gambiya sun yi kokari duk da cewa wannan ne karon farkon da suka zo gasar, amma sun tsallake zuwa zagaye na biyu.
“Ita Gambiya ma har wasan dab da na kusa da karshe ta kai. Gambiya ta fito ne a rukuni na shida, inda ba a ma yi zaton za ta iya fitowa ba, amma ta bayar da mamaki da samun maki 7.
“Haka kuma ta buga wasa hudu ba a doke ta ba. Ta doke Guinea a wasan farko na zagaye na biyu, sai Kamaru ta doke ta a wasan dab da na kusa da karshe.
“Ita ma Comoros haka ta yi, doke Ghana da ta yi ne ya kori Ghana daga gasar, inda ta tsallake zagaye na biyu.
“Sai ta samu kalubale na annobar Corona, inda dan wasa ne ma ya kama mata wasa, kuma suka samu jan kati, amma duka da haka da kyar, Kamaru ta doke ta a wasan farko na zagaye na biyu.”
Skipper ya kara da cewa, “Sai Aljeriya da take rike da kofin, ta kuma shiga gasar a matsayin kasar ta buga was 34 ba a doke ta ba, amma aka yi waje da ita. Ita ma Gahana ta kasa tsallake zagayen farko, ita kuma Najeriya ta samu maki 9, amma ta tasa zuwa da gaba.
“Sai akwai wai abin kunya da aka yi a wajen buga taken kasa a farkon wasa, inda aka samu a wasan Mauritaniya da Gambiya aka sa musu takensu na da har sau uku ana sakawa, daga baya sai kawai suka yi da kansu.
“Haka kuma mutumuwar mutum 8 da jikkatar kusan mutum 50. Wadannan suna cikin abubuwan da za su dade ana tunawa game da gasar ta bana.”
Shin Turawa suna girmama gasar AFCON?
A wani batu da aka rika tattaunawa tun farkon fara gasar ta bana, shi ne batun ko Turawa suna girmama gasar, ballantana ma su rika kallo.
A game da wannan Mamman Skipper ya ce, “Akwai wannan, amma ai dole Turawan suna dogara da ’yan wasan Afirka, kuma AFCON tana cikin gasannin da ke fitar da zakakuran ’yan wasa.
“Ana samun matsala misali a Firimiyar Ingila wasanni sun fi zafi a tsakanin Disamba da Janairu, kuma sai a dauke musu manyan ’yan wasansu ka ga akwai matsala.
“Sun yi ta kokarin ganin an daidaita lokacin da na Turai, amma idan aka hada a lokaci daya, wa zai kalla na Afirka kuma ina za ka tallata dan wasanka. Ina za a samu kudin shiga?”
Amma da Aminiya ta tambaye shi ko su ’yan wasan suna raina gasarsu da kansu, sai ya ce, “Wasu za su iya cewa haka. Misali kai ne kana min aiki ka ce za ka je gida na ce ba za ka je, yaya za ka yi? Kasarka ce amma alawus za ta ba ka, sannan za ka kara daraja, amma kungiyar kuma aikinka ne abincinka ne. Idan tana tunanin tafiyarka za su samu tangarda ai akwai matsala. Wasu na kokarin ganin sun zo, amma ba zai yiwowu ba.
“Kuma FIFA ta bayar da lokacin gayyata da sakin ’yan sana idan kuma ba a saka ba kasa za ta iya kai karar kungiyar ga FIFA har ana iya cire mata maki.
“Wasu kasashen kuma suna gayyatar ’yan wasa kurarren lokaci ne. Wadannan suna cikin ababen da suke kawo matsala. Amma ganin yadda ake taka gasar nan, babu dan wasan da zai ce ba ya so ya zo.”
Nasarori da kalubale
A bangaren nasarori da kalubale, Mamman Skipper ya ce an samu nasarori da dama, sannan an samu kalubale.
A cewarsa, idan aka yi wasu gyare-gyare, nan da dan lokaci Afirka za ta gagari duniya a harkar kwallon kafa, sannan ya ce, “muna fata a daura akan nasarar da aka samu a wannan gasar a gasar ta gaba da kasar Ivory Coast za ta dauki nauyi a 2023.”
Hakanan ya bayyana fara amfani da na’urar VAR tun daga farkon gasar, maimakon na wancan karon da sai a wasannin dab da na kusa da karshe da aka fara amfani da na’urar.
Haka kuma an samu karin kudin nasarar gasar, inda daga kasashen da suka kai wasannin dab da na kusa da karshe duk suka samun karin daloli.
Sai ya ce daga cikin kalubalen da aka samu akwai annobar covid-19 da ya tsayar da komai, da matsalar tsaro a yankin Ambazonia na kasar Kamaru da aka rika fargabar hare-hare.”
A karshe Mamman Skipper ya yi kira ga kasashen Afirka da su yi duk ababen da suka kamata kama daga gyara filiyen wasanni da samar da ababen bukata na cigaban wasanni ba sai lokacin da ake bukatarsu ba.