Kalubale ga matasan Najeriya
Salam, don Allah ku ba ni dama in ja kunnen ’yan uwana matasa. Tabbas dole ne mu matasa mu tsaya mu yi karatun ta natsu tare da yi wa kanmu fada kuma mu amsa wa kanmu wadannan tambayoyi 1. Shin idan ’yan siyasa suka ba mu makamai da kayan shaye-shaye mu sha da zimmar kai […]
Salam, don Allah ku ba ni dama in ja kunnen ’yan uwana matasa. Tabbas dole ne mu matasa mu tsaya mu yi karatun ta natsu tare da yi wa kanmu fada kuma mu amsa wa kanmu wadannan tambayoyi 1. Shin idan ’yan siyasa suka ba mu makamai da kayan shaye-shaye mu sha da zimmar kai wa abokan adawarsu hari shin ina nasu ’ya’yan ne da ba su hada mu mu je tare da su ba?
- Shin idan mu ma muka je makaranta wata rana ba za mu samu zama a kujerun da suke ba ko mun fi son su mulke mu ne kuma a karshe ’ya’yansu su mulke mu, ke nan mun zama bayinsu? Don haka akwai kalubale gare mu mu matasa cewa dole sai mun tashi tsaye wajen wayar wa ’yan uwanmu matasa kai cewa kada su yarda a rika amfani da su wajen tada zaune-tsaye a duk lokacin da aka buga gangar siyasa, ko a yi amfani da su wajen tada rikicin bayan zabe. Su kuma iyaye ya kamata su tashi tsaye domin ganin sun raba ’ya’yansu da bangar siyasa malamai kuma su rika wayar wa al’umma kansu daga illar tada zaune-tsaye a mahangar addini.
Da fatan matasa za mu natsu ba za mu bari a yi amfani da mu ba wajen tayar da zaune-tsaye a lokacin wannan zabe da za a fara gobe. Ina rokon Allah Ya sa a yi zabe lafiya Ya ba mu shugabanni nagari masu son ci gaban Najeriya da al’ummar Najeriya.
Daga Naziru Abubakar Sabo Gusau 07033565999.