kalubale: Shin kan marubuta zai hadu kuwa? (2)

Ga karin wasu ra’ayoyin daga marubuta inda suke ganin za a sami hadin kai, kuma sun bayyana wasu matsaloli su ma. Ga abin da Rahma A. Majeed (Mace Mutum) ta bayyana: “Kai zai hadu in an rage dokokin da aka kafa wa hadin kan. Tsarin dokokin ne suka hadu da rashin ilmin rayuwa da rashin […]

kalubale: Shin kan marubuta zai hadu kuwa? (2)
kalubale: Shin kan marubuta zai hadu kuwa? (2)

Ga karin wasu ra’ayoyin daga marubuta inda suke ganin za a sami hadin kai, kuma sun bayyana wasu matsaloli su ma.
Ga abin da Rahma A. Majeed (Mace Mutum) ta bayyana: “Kai zai hadu in an rage dokokin da aka kafa wa hadin kan. Tsarin dokokin ne suka hadu da rashin ilmin rayuwa da rashin aikin yi na wasunmu suka kawo rabuwar.”
Zaharaddin Ibrahim Kalla (After Long Silence) ya bayyana cewa: “Kan marubuta zai hadu mana, a tafiyar da ake yi a yanzu mafi yawancin marubuta na a tare. Abubuwan da ke kawo matsala kwadayin mulki da tunanin wasu ana samun kudi ko suna cikin kungiyoyi. Wasu na ganin rubutu yana yi da su amma ba sa cikin mulki, mafi girman matsalar marubuta ba su san mene ne kungiya ba. Magance wannan matsala sai manya sun nuna wa kanana inda ake a cikin rubutu ba tare da son rai ba.”
Kabir Assada (Duniya Marudiya) ya bayyana cewa: Dalilan da suka haifar da rashin hadin kai suna da yawa. Akwai jayayya da kishi da hassada da kyashi da jiyewa juna. Akwai kuma karancin ilimi tsakanin su kansu marubutan. Wata matsalar ita ce ta yaya za a dauko marubuci dan sakandare da Dokta ko Farfesa a saka su a kungiya daya? Akwai bukatar a bambance tsakanin su kansu marubutan.
Farfesa Yusuf M. Adamu (Idan So Cuta Ne…) ya bayyana cewa: “Kodayake maganar hadin kan marubuta da ake ta godo a kai bai kai yadda ake zuzuta shi ba. In har ana ganin akwai rashin hadin kai to babu abin da zai hana kan marubuta haduwa. In ma ka dubi ’yan fim ai ma iya cewa kan marubuta a hade yake. Kuma son zuciya ne na shugabanni da fitattun marubuta ne ya kawo rashin hadin kan in har akwai shi. Mafita ita ce kowa ya hakura da son zuciyarsa a fuskancin harkar rubutu.”
Talatu Wada Ahmad (Ruwan Raina) ta ce: “Hadin kai sai an cire son rai zai yiwu.”
Aminu Abubakar (ALA) ya bayyana nasa ra’ayin kamar haka: “Hadin kan marubuta zai samu ne ta hanyar sadaukar wa manya marubuta da jagororin masu rubutun. Girmama na gaba, ita ce babbar matsalar masu rubutu a wannan bangaren kasa. Jibintar lamura da sadaukarwa ita ce kasawar shugabanni da marubuta. Shugaban al’ummamai jibintar lamarinsu ne.”
Mahimmancin Hadin Kan Marubuta: Hada kai shi ne karfi. Al’ummar da take da hadin kai ba a cim ma ta ta kowace fuska, ta fuskar ci gaba ko dakushewa kuma lamuranta suna tafiya yadda ake so da bukata, za su yi nasara a duk al’amuran da suka durfafa kuma masu barazana ga ci gabansu ba za su yi nasara ba a kullum. Masu hadin kai suna samar da wadannan abubuwa:
Ci gaba ta fannin tattalin arziki.
Siyasa mai tsafta, zamantakewa da kuma tattali da ci gaban al’umma.
Wadanda ba su da hadin kai sunansu karshen baya, marasa makoma, marasa alkibla, wadanda ba za su tsinana komai ba sai tir da Allah wadai. Don haka yana da matukar mahimmanci a sami hadin kai a tsakanin marubuta don a gudu tare a tsira tare.
Kammalawa: In muka lura da bayanan wannan takarda, mun fahimci lallai akwai matsala a cikin hadin kan marubuta ke nan, kuma sai an yarda akwai matsalar sannan za a sami gyaran. Mu dauka ba matsalar ita ce babbar matsalarmu, sai mun yarda akwai matsalar sannan za a mu sami maganin larurar. Don haka ya zama wajibi a gare mu mu lura mu kuma yi karatun ta-na-tsu a kan kanmu don mu san hanyar bi da kuma madafa a lokutan da ake maganar marubuta da hadin kansu. Ya zama wajibi ko lallai a kanmu mu yarda da laifi ko kuskurenmu, mu gyara in muna son hadin kan ya amsa sunansa, ba mu yi ta fadin sa da ba ki ba, amma a aikace sai lokaci-lokaci in wani abu ya taso, na lahaula walakuwata.  
Gidan Dabino shi ne Shugaban Kamfanin Gidan Dabino International Nigeria Limited, Lamba 570, Sabon Titi dandago, P. O. BOd 1597, Jakara, KanoNigeria [email protected]

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan