kalubalen bayan gama rajistar masu zabe – Tafida Mafindi

A karshen watan Agusta ne Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta kammala rajistar masu zabe. Aminiya ta zanta da wani masaniin siyasa kuma jigo a Jam’iyyar APC a yanzu Alhaji Isa Tafida Mafindi idan ya yi bayani a kan babban kalubale da ke tafe. Ya kuma yi bayani a kan sauya sheka da rikicin shugabanci […]

kalubalen bayan gama rajistar masu zabe – Tafida Mafindi
kalubalen bayan gama rajistar masu zabe – Tafida Mafindi

A karshen watan Agusta ne Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta kammala rajistar masu zabe. Aminiya ta zanta da wani masaniin siyasa kuma jigo a Jam’iyyar APC a yanzu Alhaji Isa Tafida Mafindi idan ya yi bayani a kan babban kalubale da ke tafe. Ya kuma yi bayani a kan sauya sheka da rikicin shugabanci a Majalisar Dattawa:

 

Kusan kallo ya koma Jam’iyyar PDP a yanzu bayan wasu jiga-jigan siyasa sun koma jam’iyyar daga APC, wane tasiri kake ganin hakan zai yi ga zaben 2019?

Ai dama siyasa ita ce babban tsarin raba-gardama idan dai har za a bi ka’ida. Komawarsu PDP abu ne mai kyau ga jam’iyyar da masu yin zabe da ma kasa baki daya. Sai dai fa abu ne mawuyaci hakan a samu yadda ake so saboda wadanda suka sauya shekar sun tarar da wadansu na rike da ragamar jam’iyyar wadanda kuma wadansu ne suka ajiye su a wurin, ka ga ke nan dole ne su bi su a hakan duk da dai su ne su ka fi tasiri a siyance. To wannan ita ce matsalar, mu dai za mu zuba ido mu gani.

Shugaban Jam’iyyar APC Adams Oshimole na ta cewa mambobin jam’iyyar a Majalisar Dattaw za su tsige shugabansu matukar bai sauka daga mukamin ba. Shin akwai wata hanya ta daban ban da ta biyu bisa uku da doka ta ce sai an bi a yi haka?

Idan ka ji makaho yana cewa a yi wasan jifa to ka tabbata ya taka dutse, saboda haka akwai hanyoyi da dama da za a bi a tsige shugaban majalisa ba lallai sai an bi biyu bisa ukun nan ba da jama’a suke tunani. Biyu bisa ukun da ake nufi ba wai na zababbun mambobi a majalisar ba ne gaba daya, ana nufin biyu bisa ukun da suka halarci majalisa ne a lokacin da za a yi zaman Kuma dama a ka’idar zaman majalisa idan mambobi suka kai adadin jam’i wanda aka fi sani da suna “kuorum” wato mambobi 33 a Majalsar Dattawa, ai shi ke nan suna iya aiwatar da haka, kuma wannan shi ne tsarin da aka bi a baya aka zabi shugaban majalisar.

Me ya sa ’yan siyasa ke yin rajistar sababbin jam’iyyu a kullum duk da rashin tasirinsu?

Buri ne da nuna kasaita, saboda duk wanda ya kafa jam’iyya yana ganin ya kai wani matsayi a siyasa kuma ya shiga tarihi. Jam’iyya ba a kafa ta sai an samu sa hannun wadansu da bude ofishi a kowace jiha da adadin mambbobi, ga kuma kudin da za a biya hukumar zabe. Sannan batun tallafi da hukumar zabe take ba su a baya a yanzu an janye. Haka duk wani zabe da za a yi, jam’iyyar ce za ta dauki nauyin wanda zai wakilice ta wajen sa ido. To wane alfanu ne za a samu a kafa jam’iyya idan dai ba neman nuna kasaita da isa ba?

 Ganin an kare rajistar masu zabe, wane kira gare ka ga masu yin zabe da hukumar zaben?

Kirana ga masu yin zabe shi ne su guji sayar da kuri’arsu ko ba da shi ga wadansu dillalan siyasa. Su tabbata sun adana katin zabensu har zuwa lokacin yin zabe don zaben mutane nagari. Miyagun ’yan siyasa suna da hanyoyi da yawa da suke bi wajen ganin sun lalata wa al’umma katin zabensu idan dai har ba za su zabe su ba. Akwai zargin cewa wadansu daga cikin rigingimu da aka yi ta fama da su a baya an jawo su ne don kawai a hana al’ummar yankunan da lamarin ya shafa samun damar yin rajistar zabe. Kirana ga hukumar zabe kuma shi ne ta hana shiga wajen kada kuri’a da wayar hannu inda wadansu ke daukar hoto bayan dangwala kuri’a, sannan idan suka fito sai su nuna wa jami’in jam’iyya abin da suka zaba a hoton da suka dauka don ya ba su kudi. Haka hukumar zabe ta sirranta wajen kada kuri’a ta yadda ba wanda zai iya ganin abin da aka zaba bare ma ya biya ka bayan ka kada kuri’ar.H

Hukumar zaben tana fama da rashin amincewa da karin kasafin kudinta da ta mika ga majalisa?

Ai ba wata matsala a wannan. Babban kasafi da ta yi wanda yana cikin kasafin kudi na 2018 inda ta nemi Naira biliyan 149, tuni an riga an amince da shi a majalisa har Shugaban kasa ya sa masa hannu. Wannan wata sabuwar bukata ce da ta aike tana neman Naira biliyan 49. Su kuma jagororin majalisar musamman bangaren dattawa suna tsoron sake dawo da zaman majalisarsu a yanzu don gudun abin da ka iya faruwa na rigimarsu ta siyasa, ina tunanin irin wannan shi ne ya kawo jinkirin.