kalubalen da Buhari ke fuskanta kan yaki da almundahana

Ko shakka babu har yanzu akwai aiki ja a gaban Shugaba Muhammadu Buhari wajen yaki da cin hanci da rashawa. Hakika duk wani dan kasa nagari mai kishi cike yake da burin ganin kasarsa ta zamo abar tinkaho, kuma ta zarce tsara cikin jerin kasashe masu fada-a-ji.  Mafi yawan masu rike da madafun iko a […]

kalubalen da Buhari ke fuskanta kan yaki da almundahana
kalubalen da Buhari ke fuskanta kan yaki da almundahana

Ko shakka babu har yanzu akwai aiki ja a gaban Shugaba Muhammadu Buhari wajen yaki da cin hanci da rashawa.

Hakika duk wani dan kasa nagari mai kishi cike yake da burin ganin kasarsa ta zamo abar tinkaho, kuma ta zarce tsara cikin jerin kasashe masu fada-a-ji. 

Mafi yawan masu rike da madafun iko a kasarmu Najeriya suna da tabon cin hacci da rashawa.  Kazalika mafi yawan masu fada-a-ji a  kasarmu suna da wannan laifi.

Duk da kasancewar Shugaba Buhari yana da manufofi na kwarai ga ’yan kasarsa, amma wadansu masu hana ruwa- gudu  sun yi babakere a cikin gwamnatinsa, wannan ne ya sa ba su ba shi cikakken hadin kai wajen yin wannan aiki domin ciyar da kasa gaba.

In ko haka ne babu yadda za a yi wannan kasa ta samu ta kai ga inda ake so. Mafi yawa  daga cikin kasashen da suka ci gaba a duniya, ci gaban ya samo asali ne daga yaki da cin hanci da rashawa hadi  da jan dukan al’umma waje daya, domin haduwa a yi aiki tare,

Kasancewar har yanzu Najeriya tana da kima da kwarjini a idon duniya, ya kamata Shugaba Buhari ya dubi yiwuwar samo masana harkar yakar cin hanci da rashawa, hadi da samo shawarwarin kasashen da suka kubuta da wannan cutar, kamar kasar China da Indiya da Japan da Faransa da sauran kasashen waje, haka da daukar matakin ba sani ba sabo da duk wanda aka kama da wannan aika-aikar, a cire bambancin ra’ayi ko siyasa ko kabilanci ko addini, insha Allahu in aka yi haka za a samu abin da ake son samu wajen cin nasarar kan wannan lamari.

A gefe guda su ma matasa akwai rawar da suke iya takawa wajen kawar da cin hanci da rashawa, ta hanyar bayar da bayanan sirri, hadi da aiki tukuru. Idan cin hacci ya kau, zaman lafiya da kaunar juna za su samu a cikin al’umma, arzikin kasa zai yalwatu. A karshe sai Allah Ya kawo mana zaman lafiya da kaunar juna a yankin Arewa da kasa baki daya.

 Nura Muhammad Mai Apple Gusau

Mai fafutukar kare hakkin dan Adam a Najeriya 

Za a iya samunsa a 08133376020