kalubalen da ke fuskantar matasa Musulmi a yau

Alkur’ani Mai girma yana cewa: “Allah (Shi ne) Ya halicce ku cikin rauni, sannan Ya ba ku karfi, sannan Ya maida karfin rauni…” Don haka, malaman Musulunci suke cewa matashi shi ne wanda rayuwarsa ke tsakanin rayuwar yara kanana daga shekara 1 zuwa 15 ko 18, ba su kuma shiga shekarun tsufa ba, wato daga […]

kalubalen da ke fuskantar matasa Musulmi a yau
kalubalen da ke fuskantar matasa Musulmi a yau

Alkur’ani Mai girma yana cewa: “Allah (Shi ne) Ya halicce ku cikin rauni, sannan Ya ba ku karfi, sannan Ya maida karfin rauni…” Don haka, malaman Musulunci suke cewa matashi shi ne wanda rayuwarsa ke tsakanin rayuwar yara kanana daga shekara 1 zuwa 15 ko 18, ba su kuma shiga shekarun tsufa ba, wato daga shekara 45 zuwa abin da ya yi sama. Ma’ana tun daga shekara 15 har zuwa shekara 40, karfinsa yana karuwa, hankalinsa yana saituwa, tunaninsa yana fadaduwa, aikinsa yana kyautatuwa. Shi ya sa muke ganin Allah Madaukakin Sarki Yana aiko Manzanni ne idan sun kai wadannan shekara (mafi yawa, 40).
Matasa: Don haka za mu iya cewa matasa su ne wadanda ba su tsufa ba, amma sun wuce matakin yarinta; Majalisar dinkin Duniya da Bankin Duniya sun ce matasa su ne ’yan shekara 15 zuwa 24; Shirin Matsa na kasashe Rainon Ingila ya ce: ’yan 15 zuwa 29; ga wasu kasashen kuwa, ’yan 13 zuwa 25; Shirin Matasa na Najeriya (National Youth Policy of Nigeria) ya tanadi shekara 18 zuwa 30.
Ana daukar su (matasa) manyan gobe; jarin da ya fi kowane; garkuwa ga al’umma; gatan kowace al’umma; amma suna fuskantar kalubale mai yawa, musamman a wannan zamani.
kalubale: kalubale lafazin Alkur’ani ne: kalmomi biyu ne “kalu da bala” – a kira’ar Hafsu; ko “kalu  da bale” – a kira’ar Warshu; Allah Yana bada labarin cewa, a Lahira, za a tambayi kafirai (game da abin da suke karyatawa a duniya): “Shin wannan (abinda kuke gani na hisabi) ba gaskiya ba ne?” “kalu – Suka ce:  “bale – haka ne, gaskiya ne.”
Sai Hausawa suka hade Kalmar suka kira ta “kalubale” a matsayin wata kalma ta fuskantar barazana da matsaloli da gwagwarmaya da fafatawa. Don haka kalubalen matasa yana kaddara wata tambaya gabanin haka. Misali:
i. Ashe ba ku ya kamata a ce ku ne kashin bayan tafiyar kowace al’umma ba? – “kalu-bale” – Suka ce haka ne!
ii. Ba ku ake amfani da ku a tura mota, idan ta tashi a bade ku da kura ko hayaki ba? – “kalu-bale” – Suka ce haka ne!
iii. Shin ba ku aka fi gani ’yan kadan a sahun gaba a masallaci da makaranta da wuraren lacca, kanku babu hula ba, amma kun fi yawa a wuraren wasa da gidajen kallo ba?  “kalu-bale” – Suka ce mu ne!
ib. Shin ba a cikinku ake ba wasu kudi da kayan maye, su yi banga da daba ba? – “kalu-bale” – Suka ce haka ne!
b. Shin ba ku ake sa rai ku zama manyan gobe ba?  “kalu-bale” – Suka ce haka ne!
Don haka matasa suna fuskantar kalubale ko barazana ko matsaloli masu tarin yawa; wasu daga ciki sun shafi duk matasa, Musulmi da wadanda ba Musulmi ba; wasu kuma sun kebanta ga matasa Musulmi;
Za mu yi tsokaci game da kowane, insha Allahu, sai mu ba da ’yan shawarwari, daga nan mu rufe da addu’a mu tashi; Allah Ta’ala Ya agaza mana.

kalubalen matasa a ko’ina:
Duk duniya matasa suna fuskantar kalubale mai yawa. Ga kadan daga ciki:
i. Matsalar tarbiyya: ko’ina a duniya ana fama da matsalar tarbiyyar matasa; babban abin da ya damu kowa shi ne yawaitar kayan maye a tsakanin matasa; yana hana su karatu, ya hana su aiki, ya hana su sana’a, ya hana su aure, ya saka su fasikanci, ya saka su tashe-tashen hankula da kashe-kashe da sace-sace da sauran abubuwan da ke kawo matsala a cikin al’umma. kokarin Majalisar dinkin Duniya na cusa wa kowa hanyar tarbiyya irin ta Turawa, yana kara wa kasashe masu tasowa matsaloli, musamman ma na Musulmi; Misali: halatta auren jinsi da kokarin halatta wasu nau’o’in kayan maye da yunkurin soke hukuncin kisa da makamantansu.
ii. kalubalen jahilci: Wajibi na farko a kan kowane matashi shi ne neman ilimi; matasan farko sun yi fice a kan haka. Misali: Ibnu Sina (Abu Ali al-Husayn Ibn Abdallah) ya haddace Alkur’ani yana da shekara goma, ya gama karance ilimin zamaninsa yana da shekara 18; Imam Abdullahi bin Abu Zaidin Alkairawani ya rubuta littafin Risala yana dan shekara 13 ko 14; amma mafi yawan matasa a yau ba sa son karatu; ko’ina a duniya ana fama da matasa don su je makaranta, amma su sun fi son a bar su su yi wasa, musamman kwallon kafa; kari a kan haka gwamnatocin kasashe masu tasowa ba sa son kashe kudi a kan harkar ilimi, don haka da matasan ma za su maida hankalin wajen zuwa makaranta, to, babu isassun makarantun, babu kwararrun malamai, babu wadatar kayan koyarwa; sannan a kasar Hausa, iyaye ba safai suke nuna damuwarsu game da ilimin ’ya’yansu ba; don haka babban kalubalen da yake fuskantar matasa a yau shi ne su farga su yi wa kansu da kansu gata wajen neman ilimi.
iii. Rashin Sana’a: Da zarar matashi ya kammala karatun da ya dace, kalubale na gaba shi ne samun aikin da ya dace. Wannan ma matsala ce a ko’ina a yanzu a duniya, shi ya sa ake ta samun karuwar zanga-zanga da tashin hankali a ko’ina; bugu da kari kasashe masu tasowa ba su nuna alamar daukar hanyar da ta dace don sama wa matasa aiki. Misali, maimakon a ware kaso mai tsoka na kasafin kudi don inganta harkar ilimi ko noma ko kiwo ko kasuwanci ko kananan san’o’in hannu, ko inganta manyan masana’antu, gwamnatocin kasashe masu tasowa sun gwammace su ware kudi masu yawa a harkar tsaro, don saya wa ’yan sanda motoci a rika bin su a guje da jiniya da sunan tsaronsu, ko a rika zagayawa neman inda matasa suke ko za su aikata laifi a kame su. Sannan a kasar Hausa, an fi karancin taimakekeniya da rainon matasa wajen sana’a da ’yantar da su idan sun kai wani zango na koyo; don haka babban kalubalen matasa shi ne su gane hakan su yi wa kansu gata wajen neman sana’a da jurewa a kanta.
ib. Matsalolin soyayya da aure: Bayan samun aiki sai aure. Mafi yawan tattaunawar matasa, maza da mata ko a fili ko a waya, game da soyayya ce da aure. Harkar tana yi musu barazana da ban tsoro. Ga shi malamai sun taskance bayanin yadda soyayya za ta yi sauki da dadi, amma matasa ba sa karantanwa. Don haka kullum suke a wahale da fargaba. A kasashe masu tasowa akwai karancin bita ga matasa game da rayuwar aure da soyayya. Matsalar ta fi tsamari a kasar Hausa. Babu abin da zai taimaka wa matasa game da wannan kalubalen kamar su yi karatu sosai.
kalubalen Matasa Musulmi: Tun daga zuwan Annabin Rahama (SAW) tarihin duniya ya zamo na gwagwarmaya tsakanin Musulunci da kafirci. Wannan ya gadar wa matasa Musulmi kalubale mai yawa:

 Yada sakon Musulunci:
Allah Ya ce Ya aiko da ManzonSa da shiriya da addini na kwarai don ya sha gaban duk wata hanya ta rayuwa, koda kuwa mushrikai ba su so ba, (kuma matasa ake sa ran su yi aikin). Sannan Ya ce su mushirikai, ba za su kauce daga yakarku ba har sai sun gotar da ku daga tafarkin addininku matukar suka samu iko (don haka matasa Musulmi za su fuskanci kalubale daga mushirikai). Ya kuma ce Yahudu da Nasara ba za su taba amince muku ba har sai kun bi tafarkinsu (kamar yadda za mu gani a misalai masu zuwa); haka kuma Ya ce idan kuka yi sakaci a wannan gwagwarmayar Allah zai maye gurbinku da wasu wadanda ba za su yi sakaci irin naku ba.