kalubalen da ke gaban dan takara
Sau da yawa idan aka yi maganar siyasa a Nijeriya, ana maganar kudi ne kawai! Yayin da hakan ke sauyawa zuwa ga bin akida ko ra’ayi duk da cewa dabi’ar zarcewa ta dasu a zukatan ‘yan siyasar domin kowane kansila na son zama dan majalisar jiha, haka caymomi na da burin zama kwamishinoni, ko ‘yan […]
Sau da yawa idan aka yi maganar siyasa a Nijeriya, ana maganar kudi ne kawai! Yayin da hakan ke sauyawa zuwa ga bin akida ko ra’ayi duk da cewa dabi’ar zarcewa ta dasu a zukatan ‘yan siyasar domin kowane kansila na son zama dan majalisar jiha, haka caymomi na da burin zama kwamishinoni, ko ‘yan majalisar tarayya, yayin da ‘yan majalisar tarayya da sanatoci na da burin zama gwamnoni haka gwamnonin da yawa na da burin zama shugaban kasa!
Hakan ke nuna bukatar kudin ta fi yawa ga wanda ya hau kan kujerar, inda zai tara abin da zai sayi gida a a Abuja, idan dan Arewa ne ya kara da wani a Kaduna ko Kano sannan a kauyensu, kuma zai yi tanadin
abin da zai rika rabawa da Azumi ko atamfofin salla ga raguna da sauransu. Idan dan Kudu ne shi ma sai ya tanadin gida a Legas ko Fatakwal sannan akwai kudin sallamar ‘yan banga, kulla da makwafta kuma ga kyatutukan Kirismati!
daya daga cikin dabi’un ‘yan siyasa shi ne su rika tara mutane a gaban gidajensu ko idan sun zo gari a rika binsu! A haka idan siyasa kasuwanci ce, riba ke gaba dan takararka kallonku yake kamar wani jari da zai zuba ya sami riba!
Kusan duk ‘yan siyasar Nijeriya su suke bayana bukatarsu ta tsayawa takara, ba wai ba mutane suke fito da su ba, illa kalilan! Yayin da tun a tashin farko suke sakin jiki ku dauka daya kuke ko ba su kyamarku,
amma da mutum ya dare kujerar sai a sauya salo!
Akan fara da sukar wadanda suke kan karagar mulki, musamman ‘yan adawa, yayin da suka sami dama sai su nuna ba bambanci tsakaninsu da wadanda suke mulki a wasu wurare ma kullun gara jiya da yau!
Matakin farko jam’iyya tare da kamun kafar iyayen jam’iyya da neman goyon bayan mutane ta hanyar kwadaitasu ta yadda zasu yi sha’awar dan takarar. A nan akan dauki ‘yan jam’iyya daya a matsayin makusanta ko da akwai bambancin addini da al’ada, inda ake kulla zumunci.
Neman malamai da ‘yan tsubbu, a nan za a gaya masa ko talaka basu zabe shi ba zai ci! kudi kawai zai biya a masa tsafin da yake bukata da kuri’ar talakan! Daga karshe zai wulakanta inda kaikayi zai koma kan mashekiya.
Siyasa a Najeriya ba ilimi ba ce shi yasa sai ka iske wani jahilci wanda bai san komai ba ya jagoranci jama’a, sannan ba a aiki da ilimi wajen warware matsalolin mutanen! Ko ka iske masu ilimin suna jahiltar
abin da suka koya a makaranta a sunan mahukunta!
A mayar da jari hujjanci jigon ci gaba, duk wanda ya fika samu ya fi ka karbuwa, yayin da malaman na addini da na zamani suke da wannan tsarin hatta sarakuna, inda suke nada sarautu ga wadanda suka ba su ba wai wadanda suka kawo ci gaba a garin ba! Su ma na addinin maimakon su guji haram sai ka ga suna girmamam wani azzalumi, ku ga jami’a na karrama shi duk da magudin da ya bayana da irin babakeren ya tafka a kira shi da Dakta!
Idan an hau, an rantsar da gwamna ko dan majalisa, mutane kan yi yawa! A nan ne ake sauya alkawalin da aka yi, musamman idan muka kalli yawan mabukata, kuma shi kansa yana son ya gina kansa, inda giyar mulki kan kai wakilin da yin wulakanci.
Bayan ya dawo gida ya kan rage tasiri a bisa rashin ba sabbin shugabannin shawara cikin hikima, halartar tarruruka, tsokaci a jaridu ko gidajen radiyo, rashin taimakon ‘ya’yan jam’iyya da mutanen gari.
Wasu kan zama ‘yan kasuwa ko su sayi gidaje a Abuja su zuba ‘yan haya ko su sayi wasu hanayen jari su kwanta a gefe a manta dasu. Idan ya guji mutane a ce ci-ka-tsere, idan bai tara ba a ce matsayaci!
Duk da haka a watan farko ko bayan ‘yan watanni sai ya bayana karara dan siyasa ya ja baya, domin zai ci abin da ya tara kawai, sai ya sauya salon almubazzranci da dukiyar hukuma zuwa Umra ko Hajji har ya biya wasu ya kau! sai ka ga ya yi shekaru bai hau jirgi ba.
Bugu da kari addu’o’in wadanda aka zalunta a zamaninsa za su addabe shi, inda wasu za su gaya masa magana a bainar jama’a, sannan wasu ba zasu hakura ba, har iyalensa da danginsa sai abin ya shafa.
Ya kamata dan siyasa ko bayan ya bar mukaminsa ya ci gaba da hidimta wa mutane ta hanyar mu’amala da kokarin kyautata zamantakewa da harkokin rayuwarsu, a san ra’ayinsa, ya fito fili ya goyi bayan wasu ‘yan takara ko ma ya tsaida shugaban karamar hukuma ko kansiloli a yankinsa. Ya ba jam’iyyarsa saiti.
Babban kaluballe babu dimokuradiyyar cikin gida, sannan komai ya dogara ga shugabancin masu zartarwa, sune masu wuka da nama! A haka yana da wuya mutum ya yi tasirin a zo a gani sai da kamun kafa ko kalubalantar wanda suke sama. Hakan kan sa su daga ma kafa, a dama da kai! Suna jan masu sukarsu jiki!
A halin yanzu an fara faran-faran da talakawa, yana yawan zuwa garinsu, don ya saba da ‘yan karamar hukuma, ‘yan uwa a karkara domin ana shekarar jajiberin zabe, kafin a yi sa’a a sauya fuska ko a dawo gida cikinmu talakawa nan ido zai raina fata!
Buhari Daure
Muryar Talaka
[email protected]
+2347035986444