kalubalen da ke gaban Gwamna Lalong
Da farko Jihar Filato tana daya daga jihohin da suke fama da matsaloli marasa misaltuwa, kadan daga cikinsu: Na farko rashin biyan Malaman firamare da sakandare albashin su, wasu tsawon wata 19. Na biyu matsalar da ta ki ci, ta ki cinyewa, ta fadace-fadacen kabilanci da addini. Na uku muna fama da rashin kyawun hanyoyi, […]
Da farko Jihar Filato tana daya daga jihohin da suke fama da matsaloli marasa misaltuwa, kadan daga cikinsu: Na farko rashin biyan Malaman firamare da sakandare albashin su, wasu tsawon wata 19. Na biyu matsalar da ta ki ci, ta ki cinyewa, ta fadace-fadacen kabilanci da addini. Na uku muna fama da rashin kyawun hanyoyi, musamman a birnin Jos da kewaye. Na hudu muna fama da rashin aikin yi da ruwan sha. Na biyar muna bukatar a gyara mana kasuwar nan mai dimbin albarka, wato Terminus da ke birnin Jos. Wadannan kadan ne daga cikin matsalolin da muke fuskanta a Jihar Filato. Kuma duk wadannan matsalolin Mai girma Gwamna Lalong ya yi mana alkawarin magance su, amma har yanzu kimanin wata shida ke nan da hawansa karagar mulki shiru muke ji. Da fatan Mai girma Gwamna zai farka daga dogon barcin da yake yi.