kalubalen da ke gaban Jam’iyyar PDP
Tabbas zaben 2015 tsakanin jam’iyyu biyu za a yi shi watau tsakanin mai mulki PDP da kuma jam’iyyar adawa APC, wadda ta zama wata gagarumar hadakar jam’iyyun hamayya ganin yadda aka yi sama da shekaru 14 PDP na mulki, amma an gaza tabuka abin a zo a gani! PDP ta fara fuskantar matsaloli tun lokacin […]
Tabbas zaben 2015 tsakanin jam’iyyu biyu za a yi shi watau tsakanin mai mulki PDP da kuma jam’iyyar adawa APC, wadda ta zama wata gagarumar hadakar jam’iyyun hamayya ganin yadda aka yi sama da shekaru 14 PDP na mulki, amma an gaza tabuka abin a zo a gani! PDP ta fara fuskantar matsaloli tun lokacin da marigayi Umaru Musa ‘Yar aduwa ya kamu da rashin lafiya, bayan cewa shi kansa dora shi aka yi, kuma ya amince da kansa cewa zaben da ya kai shi kan karagar mulki cike yake da kura-kurai, wanda ya ce zai gyara a zabe idan hali ya yi, amma rai ya riga mu!
Zabo sabon shugaban PDP ko neman a kori Bamanga Tukur ba zai sauya komai ba, kamar yadda wasu ke ganin haka mataki ne na kwarai. Barin Bamanga ba shi ba ne gyara, musamman ganin ‘yan Arewa sun fi so a sauya shi.
Gudun hijira da ake yi daga jam’iyyar PDP ita ce babbar barazanar da jam’iyyar ta fuskanta tun da aka kafa ta, yayin da a yau kullun sai ka ji mutane suna kaura, wasu ma sun zama bakin haure a jam’iyyar, wani lokacin ma sai a ji dubunnai su bar PDP a rana daya rak! Idan ‘yan majalisa suka dawo hutu suka bukaci a sake sabon zabe a majalisar, ya ke nan? Dole dan jam’iyyar adawa zai jagorance su idan sun fi yawa, to wai idan shugaban majalisar ya koma APC fa?, kuma ra’ayin APC ya koma kan ganin sai an tsige Shugaba Jonathan da wasu gwamnonin da suke zagon kasa a jihohinsu!
Duk da cewa ita kanta APC tana da nata matsalolin, musamman na cikin gida wanda ke neman raba jam’iyyar gida biyu, babbar matsala ce, da za ta iya raunana jam’iyyar kafin ta ma kafa gwamnatin. Tun kafin a fara rajista, an raba gari tsakanin magoya bayan Buhari na asali, watau ‘yan ANPP/CPC/APC da ANPP/APC sannan ga sababbi, wadanda suka shigo yanzu kamar ‘yan PDP din nan.
A jihohi ana fafatawa tsakanin magoya ‘yan asalin jam’iyyar da sababbin shiga, musamman gwamnonin ‘yan PDP da suka yi kaura. Watau Jihohin Kano da Sakkwato da Adamawa. Duk da cewa bakin sun yi suna a kamawa da karyawa, amma an tsarkake su, sun shahara da magudi da yankan baya, wasu ma akan haka suka ginu, kuma wai su za su jagoranci ‘yan adawa ga nasara!
Sannan akwai matsalar cewa kowane tsahon Gwamnan PDP yana da mataimakin da ya yi wa alkawari, tare da dan lele, sannan a APC akwai gwanin da ake ganin ya fi dacewa; wannan ma wata matsala ce da ya kamata a duba kafin a je ko’ina. Gara a dunkule a zama daya a yi magana da murya guda.
Addini zai taka rawar ganin wajen karkata ra’ayoyin talakawa a zabe mai zuwa, domin idan Jonathan ya tsaya takara Kiristocin Arewa da Kudu duk shi za su zaba, haka sai ya samu wasu Musulmi mabiya! A haka ya rage ga ‘yan Arewa su hada kai, su san wanda za su tsayar, kuma a tabbata an ba shi goyon baya.
A nan hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) tana da rawar da za ta taka wajen ceto jam’iyyun kasar daga halin da suke neman fadawa, musamman wajen fidda gwani a jam’iyyu, yayin da akwai wanda ya fara fitowa, akwai mai jama’a, akwai wanda ya fi kudi da wanda ya fi kamun kafa wajen iyayen gida. Duk da ana sa’a a samu wanda ya fara fitowa, mutumin mutane, kuma ya fi abokan takararsa kudi, kuma ya rike ubangida.
Amma a gyara musamman don rage kaifin ubangidanci tsakanin iyayen jam’iyyu da ‘yan takara, tare da ba matasa damar taka rawar gani, domin talakawa sun san nasu, dadin dadawa lokaci ya yi da za a yi wa siyasar kasar nan allurar sabon jini.
Buhari Daure ya rubuto daga Muryar Talaka +2347035986444 [email protected]