kalubalen da ke gaban Janar Buhari

Da farko zan fara da taya mai girma shugaban kasa mai jiran gado murnar samun nasarar wannan zabe mai cike da dimbin tarihi, sannan ina taya shi murnar kasancewa mutum na farko a Nijeriya kuma na bakwai a duk fadin Afirka wanda ya samu nasarar kayar da shugaban kasa mai ci. Duk da cewar Janar […]

kalubalen da ke gaban Janar Buhari
kalubalen da ke gaban Janar Buhari

Da farko zan fara da taya mai girma shugaban kasa mai jiran gado murnar samun nasarar wannan zabe mai cike da dimbin tarihi, sannan ina taya shi murnar kasancewa mutum na farko a Nijeriya kuma na bakwai a duk fadin Afirka wanda ya samu nasarar kayar da shugaban kasa mai ci.

Duk da cewar Janar Muhammadu Buhari mutum ne mai gaskiya da rikon amana da hangen nesa, to, amma ya kamata ya sani cewa Nijeriyar yau ta sha bamban da Nijeriyar 31, ga watan Disambar 1983 zuwa Agustan 1985.Domin a wannan lokacin ya tarar da kasar a lokacin da take fama da matsanancin kabilanci, da nuna bambancin addini ko yanki, ta yadda za ka kasa gane shin jami’an tsaron kasar nan suna wakiltar kasar ne ko kuma a’a suna wakiltar bangaren da suka fito ne? Wannan yanayin da wadansu marasa kishin kasa suka jefa mu ya sanya aikin gyaran yake da matukar sarkakiya ta yadda lallai Janar yana bukatar kara nutsuwa domin fuskantar kalubalen da yake gabansa.
Babban kalubalen kuma wanda ya fi kowane muhimmanci shi ne hadin kan kasa. Sanin kowa ne cewa Nijeriya ba ta taba samun kanta a cikin mawuyacin hali na rashin amintar juna irin wannan karon ba. wannan kuwa zai fito fili ne idan mutum ya yi duba na tsanaki irin yadda aka kada kuri’ar shugaban kasa a inda mafi yawan ’yan Arewa suka zabi dan yankinsu watau Janar Muhammadu Buhari mai ritaya, su kuma Yarbawa suka zabi na su dan watau Farfesa Yemi Osinbajo (a matsayin mataimakin shugaban kasa).Su kuwa ‘yan kabilar Igbo da sauran kanan kabilun Kudu maso Kudu suka zabi dansu watau Dr. Goodluck Ebele Jonathan. To, a nan shawarata ga Buhari ita ce lallai ya kamata ya nuna misali ta hanyar yin adalci ga kowane bangare, ba tare da la’akari da cewa sun zabe shi ko ba su zabe shi ba, domin yanzu shi shugaban Nijeriya ne ba na wani yanki ko addini ba. Yin haka zai sa ‘yan Arewa su yi masa kallon magajin Sardauna, Yarbawa su rika yi masa kallon Cif Obafemi Awolowo, a yayin da Inyamurai za su rika cewa Zik ya tafi, Zik ya dawo! Su kuwa ‘yan Kudu maso Kudu su ce ‘Sai Buari’. Hakan zai yi matukar kara wa Janar Buhari mutunci a idon duniya.
kalubale na biyu kuwa shi ne rashin tsaro, a nan zan tunasar da Janar abin da ya riga ya sani ne, dole ne ya zama kowanne bangare ko addini yana da wakilci, sannan a samar wa da jami’an tsaro kayan aiki na zamani.Amma abin bakin ciki ne ainun irin yadda jami’an tsaronmu suke nema su zama jami’an tsoro!
Na uku shi ne matsalar tattalin arziki, a nan lallai Janar yana bukatar mutane masu kaifin hankali da hangen nesa da kishin kasa, mutanen da za su bai wa Gwamnati shawarwari da hanyoyin samun kudin shiga ta yadda ba sai mun raja’a a kan man fetur ba. A nan kasancewar shugaban kasa ya fito ne daga yankin Arewa, ba na bukatar sanar da shi cewa akwai dimbin albarkatun kasa a yankin Arewa, to, lallai ya kamata a fito da su domin kara bunkasa tattalin arizikin kasa.
Wani abu mai matukar muhimmanci shi ne, ya kamata shugaban kasa mai jiran gado ya sani cewa yankin Neja-Delta yana bukatar kulawa ta musamman.Musamman idan aka yi la’akari da cewa kusan manyan garin su ne suke handame kaso mafi tsoka na kudaden da ake warewa domin su. A nan ya kamata ka lura da dukkanin aiyukan ma’aikatar Neja-Delta ta yadda kudaden da ake warewa ya zama suna amfanar talakan yankin kai-tsaye.
Daga karshe ina rokon Allah da sunayensa mafi girma da daukaka ya dafa wa sabon Shugaban kasa, ya zaba masa abokan aiki na gari, wadanda za su taya shi sauke wannan nauyi da Allah ya dora masa.

Muhammad Sa’id Ibrahim
karamar Hukumar Fagge, Kano.
[email protected]
0803 810 3306