kalubalen da ke gaban mata marubuta

Marubuta mata muna da baban kalubale, wajen sauya manhajar karatu, don kyautar tarbiyar al’umma da walawala zamantakewa da tatalin arziki. Hakika sanin kowa ne maruibuta mata sun bayar da gudunmuwa wajen bunkasa adabi a wannan kasa, musamman in an yi la’akari da littattafan Farfesa Zainab Alkali a fannin adabin Turancin Ingilishi; sai kuma Hajiya Hafsat […]

kalubalen da ke gaban mata marubuta
kalubalen da ke gaban mata marubuta

Marubuta mata muna da baban kalubale, wajen sauya manhajar karatu, don kyautar tarbiyar al’umma da walawala zamantakewa da tatalin arziki. Hakika sanin kowa ne maruibuta mata sun bayar da gudunmuwa wajen bunkasa adabi a wannan kasa, musamman in an yi la’akari da littattafan Farfesa Zainab Alkali a fannin adabin Turancin Ingilishi; sai kuma Hajiya Hafsat AbdulWaheed, wadda ta rubuta ‘So aljannar Duniya, wadannn su ne a sahun manyan marubuta. Mu d amuke bin su a baya, wacce turbha muka dauka don inganta rayuwar al’umma?
daukacin rubuce-rubucen mata sun fi ta’allaka ne kan yadda za a warware matsalolin zamantakewar aure, kodayake wadanda suka waye a zamani, sun fadada tunaninsu kan al’amuran da suka shafi ’yancin mata, har ma wadanda suka wuce gona da iri, na ganin lokaci ya yi da za su yi kafa-da-kafada da maza a kowane fanni na rayuwa. Musulmi dai da daukacin mabiya addinai ba lallai ne su ga wata fa’ida a atattare da gasa tsakanin maza da mata ba, illa dai su zamanto abokan zaman jinsi, masu kokkarin tabbatar da daidaito wajen tabbatar da adalci ga juna.
A irin tawa fahimtar ina ganin marubuta mata suna da babban kalubale a gabansu, musamman ganin cewa uwa ita ce makarantar farko ga yaro ko yarinya. Uwa mai tsafta da kula da iyali, akwai yiwuwar ’ya’yan da ta haifa su yi koyi da ita; mhaifiyar ’ya’yan da ke yin sana’a, akwai yiwuwar ‘’ya’yanta ba za su shiga cikin gungun zauna gari banza. Sannan uwar da ta iya girki, babu ko wata tantama duk wanda ya yi aure daga zuri’arta ya auro girkin abinci mai gina jiki. daukacin kyawawan dabi’u da uwa ta siffantu da su, su ake sa ran ’ya’yanta su tashi das u; sana’o’in da uwa ta tashi tana yi, don tallafa wa iyali, ko tantama babu sasi an samu wanda zai yi koyi da ita a cikin zuri’arta. Kowa ya san akwai jikar Barni mai coke da ke waka. Nana Asma’u diyar shehu Usmanu Mujadaddi dan Fodiyo, ta yi wa ilimin adddini hidima, kuma a cikin jikokinta, an samu wadanda suka gajeta.
Babban al’amari dai, shi ne yadda Malam Bahaushe ke cewa, “Kamar Kumbo, kamar katanta,” a wani bagiren ma har tambaya ya kanyi, “wai shin barewa ta yi gudu, danta ya yi rarrafe.” Idan kuwa aka samu sabani, a tsakanin dabi’un uwa ko ma na iyaye da ’ya’yansu, Malam Bahaushe kan furta cewa, “albasa ba ta yi halin ruwa ba.”
kalubalen da ke garemu, shi ne na bunkasa sana’o’i da sauyawa ko ingant amanhajar karatun da ake koyar da ’ya’yanmu, a makarantun Boko da Islamiya. Ina ganin zai yi matukar fa’ida idan aka ce kowace yarinya ko yaro da zai shekara biyar zuwa 10 yana halartar makarantun addini, wajibi ne a hada masa da ilimin sana’a, ta yadda kafin ya kamala ya samu alkiblar rayuwa, don gudun kada ya shiga cikin jerin zauna gari banza. Ita kanta ’ya mace idan ta iya sana’ar da za ta talalfa wa rayuwarta, ko da a gidan miji ta zauna babu wadda za ta zo ta kawo mata gulamace-guolmace da za su haifar wa aurenta tangarta. Kuma ita kanta za ta samu natsuwa wajen kula da iyali; ko da maigidanta wajen neman abinci ya samu matsalar a kasuwancinsa, ko ba a biya albashi ba, uwargida za ta iya bayar da tata gudunmuwar.
Ina da tabbacin cewa duk wanda ya karanta littafina mai taken “tantabara,’ watakila ya fahimci yadda ma’aurata za su zama masu cika alkawura ga juna. Kai a cikin marubuta mata akwai wadanda suka yi rubutu kan sarakuna da malamai da attajirai. Don na san Hajiya Rabi’a Tallae Maifata ta rubuta wani littafi, mai taken “Awa 24 a gidan Dabo,” wanda ya fito wa al’umma yadda ake tarbiyyantar da ’ya’yan gidan sarauta. Muhimmin al’amari game da wannan littafi shi ne yadda  Mai Martaba San Kano ke gudanar harkokin rayuwarsa a kowace rana, musamman abin da ya shafi tarbiyyar iyali. Kai marubuciyar, ta ma bayyana cewa, “sarki ya fi talawakawansa samun lokacin ganawa da iyalansa.” Kuma marubuciyar tana da sauran littattafai, wadanda suka hada da sirrin rayuwa. Akwai marubuta mata da ke da irin wannan fasahar, amma kash, sai dai mafi yawanmu mun takure tunaninmu kana bin da ya shafi soyayya, har ma wasu na zarginmu da fassara fina-finan Indiya, har al’adunsu suka yi tasiri a kanmu.
Bisa la’akari da misalan da na jero, ya kamata marubuta mata su sauya akalar rubutunsu kan muhimmancin koyon sana’a da tarbiyyar yara, ta hanyar fifita kyawawan al’adu  da tanade-tanaden addinin Musulunci. Kuma tunda ana samun malaman makaranta mata, to a nusar da su yadda za su gane cewa, wadanda suke koyarwa tamkar ’ya’yansu ne na ciki. Marubuta mata su himmata wajen yin kira ga gwamnati, tare da kulla dangantaka da kungiyoyin raya ci gaban al’umma, don kyautata zamantakewa da tattalin arziki da samar da shugabanci nagari. Wajibi a daukacin tarurrukan da marubuta mata ke halarta, don kara wa juna sani, su rika tattaunawa kan manhajar karatun da ake koya wa yara, kuma su rika rubuta labarai da ke kunshe da dabarun yadda za a bunkasa fannonin ilimi yadda ’ya’yanmu za su ci gajiyarsu. Matukar marubuta mata suka dauki tafarkin inganta manhaja karatu, da cusa fa’idojin da ke tattare da koyon sana’a a kagaggun labaransu, yin haka zai sanya mu warware kusan rabin matsalolin da al’umma ke fama da su.
Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo, ma’aikaciya ce a ma’aikatar yada labarai ta Jihar Kano.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno