Kalubalen da ke gaban sabon kocin Barcelona Xavi
Ana ganin Xavi zai dawo da tsarin taka ledar kungiyar na ‘Tiki-Taka’.
A ranar Litinin ce aka gabatar da tsohon dan wasan Barcelona, Xavi Hernandes a matsayin sabon kocin kungiyar.
Xavi ya maye gurbin Ronald Koeman, wanda kungiyar ta raba gari da shi saboda rashin katabus.
- Kungiyoyin agaji sun horar da ’yan sa-kai 50 a Gombe
- ‘Zan iya makure wuyan Solskjaer saboda sanya Fred a wasanni’
A ranar 19 ga Agustan 2020 ce aka ba Koeman aikin horar da Barcelona bayan kungiyar ta yi hannun riga da Quique Setien bayan kungiyar Bayern Munich ta lallasa kungiyar da ci 8 da 2 a Gasar Zakarun Turai ta 2020.
Tun bayan zuwansa, sai kungiyar ta fara tatata, musamman bayan tafiyar Lionel Messi da Luis Suarez da Antoinne Griezman kusan a lokaci daya.
A wasa 67 da ya jagoranci kungiyar, ya samu nasara da kashi 59.7 inda ya ci wasa 39, ya yi kunnen doki 12, sannan aka doke shi a wasa 16.
Xavi a Al Sadd
A kakar 2015-2016 ce ya koma kungiyar Al Sadd a matsayin dan wasa, sannan a kakar 2019 ya zama mai horar da kungiyar, inda daga Mayun 2019 zuwa yanzu da ya bar kungiyar domin fara horar da ’yan wasan Barcelona ya jagoranci kungiyar ta Al Sadd buga wasa 102.
A tsawon wannan lokaci ya samu nasara a wasa 67, ya yi kunnen doki a wasa 17, sannan aka doke kungiyar a wasa 18.
Haka kuma a shekarun da ya yi a Qatar, ya jagoranci kungiyar lashe kofuna guda bakwai.
Xavi zai iya magance matsalar?
Magoya bayan kungiyar da dama suna cewa ba matsalar koci ba ce kungiyar Barcelona ke fama da ita, inda suke bayyana rashin kwararrun ’yan wasa a matsayin matsalar.
Xavi, mai shekara 41 ya lashe kofuna da dama, ciki har da La Liga guda takwas da Gasar Zakarun Turai guda hudu da sauransu.
Sannan ya lashe Kofin Duniya da Kofin Nahiyar Turai a kasarsa ta Spain.
A kungiyar Al Sadd ta birnin Doha da ke Qatar ce ya fara horar da ’yan wasa.
Sai dai ana ganin Al Sadd daban, Barcelona daban, musamman a wannan lokacin da Barcelona din take cikin matsala.
A farkon kakar bana ce kungiyar ta rasa zaratan ’yan wasanta, ciki kuwa har da Lionel Messi, wanda da dadewa kwazonsa a filin tamola ya kasance tamkar shi ne yake jan ragamar kungiyar.
Kasancewar babu Messi kuma babu Suarez, sai aka yi tunanin Griezman ne zai dauki ragamar jan kungiyar, sai kwatsam shi ma ya koma Atletico Madrid inda ya baro.
A nan kungiyar ta mayar da hankali kan Dembele da Ansu Fati, wanda shi aka ba lambar Messi, wato lamba 10 da tunanin zai maye gurbinsa.
Sai dai har yanzu Ansu Fati bai warware ba, inda yake fama da raunuka da dama.
Kwanan nan Ansu Fati ya dawo daga jinyar kusan wata 8, sannan yanzu haka akwai rade-radin ya sake jin wani raunin.
Shi kuma Dembele dama raunukan ne matsalarsa. Kwanan nan ya dawo daga jinya, inda magoya bayan kungiyar suke ta fatan ya dade yana buga wasanni.
Haka kuma kungiyar na fama da matsalar rashin kudi, wanda matsalar ce ma ta sa suka saki Messi ya tafi, suka saki Griezman, sannan suka kasa sayo wasu ’yan wasan, duk da suna da bukata.
Tun bayan annobar Covid-19, kungiyar ta shiga matsanancin rashin kudi, wanda har yanzu ba ta farfado ba.
Baya ga rashin ’yan wasa, ga rashin kudin da za a sayo sabbin ’yan wasa kwararru.
Da yake jawabi bayan karbar ragamar kungiyar, Xavi ya ce wa manema labarai cewa, “yanzu babu Messi babu Eto’o kuma babu Ronaldinho. Messi abokina, ya aiko min da sakon fatan alheri.
“Na yi matukar farin cikin dawowa kungiyar nan, domin gida na dawo. Muna cikin matsala na rashin kudi, amma mu Barcelona ne, kuma nan ne babbar kungiyar kwallon kafa a duniya.
“Za mu yi aiki tukuru domin dawo da martabar kungiyar nan.”
Sai dai magoya bayan kungiyar, har da wasu da a kwanakin baya suka bar goyon bayanta sun fara dawowa, inda suka ce suna tunanin Xavi zai dawo da martabarta, musamman kasancewar a cewarsu ya san kan kungiyar da salonta.
Sannan wasu na cewa ko ba komai, Xavi zai dawo da tsarin taka ledar kungiyar na ‘Tiki-Taka’.
Sai a ranar 20 ga Nuwamban ne kungiyar za ta fara wasa a karkashin jagorancin Xavi, inda za ta karbi bakuncin Espanyol, kafin ta karbi bakuncin kungiyar Benfica a wasan Zakarun Turai: Wasan da suke matukar bukatar ganin sun yi nasara.