Kalubalen da ke gaban sabon kocin Juventus, Andrea Pirlo

A ranar Lahadi aka sanar da tsohon dan wasa Juventus Andrea Pirlo mai shekara 41 a matsayin sabon kocin kungiyar, sa’o’i kadan bayan kungiyar Lyon ta Faransa ta fitar da kungiyar daga gasar Zakarun Turai ta bana. A wasan wanda aka tashi Juventus ta doke Lyon da ci 2 – 1 a gidan Lyon, Juventus […]

Kalubalen da ke gaban sabon kocin Juventus, Andrea Pirlo

A ranar Lahadi aka sanar da tsohon dan wasa Juventus Andrea Pirlo mai shekara 41 a matsayin sabon kocin kungiyar, sa’o’i kadan bayan kungiyar Lyon ta Faransa ta fitar da kungiyar daga gasar Zakarun Turai ta bana.

A wasan wanda aka tashi Juventus ta doke Lyon da ci 2 – 1 a gidan Lyon, Juventus ta yi waje na kasancewar Lyon ta doke ta a Italiya da ci daya da nema.

Wannan ya sa jimilla ya kama biyu da biyu, amma kasancewar Lyon ta je har gida ta doke Juventus da ci 1 – 0 tun kafin annobar Covid-19 ta dakatar da komai sai ya zama an yi waje da Juventus.

Kungiyar Juventus ta sanar da Pirlo ne a matsayin sabon kocinta domin maye gurbin tsohon kocinta Maurizio Sarri wanda ta sallama jim kadan bayan fitar da ita daga gasar Zakarun Turai.

Shi dai Pirlo tsohon dan wasan tsakiya ne na Italiya da ya buga wa kungiyoyin Brescia da AC Milan da Inter Milan da Juventus, sannan ya karkare zamaninsa a kungiyar New York City ta Amurka.

An samu matasan masu horar da ‘yan wasa da suka shigo bangaren da kafar dama bayan sun yi ritaya daga kwallo kamar su Pep Guardiola da Zinedine Zidane da sauransu.

Matsalolin da Pirlo zai fuskanta a Juventus a matsayin koci

Rashin gogewa

A watan jiya ne kawai tsohon dan wasan ya fara horar da ’yan wasa, inda ya zama kocin ’yan wasan kungiyar Juventus ’yan kasa da shekara 23.

Bayan horar da ’yan wasan kasa da shekara 23 na Juventus da ya yi na wata daya, kuma bai ma taba jagorantar kungiyar zuwa wasa ko daya ba, ba shi da wata gogewa ta horar da ’yan wasa.

Ke nan za a iya cewa ba shi da gogewar da ake bukata domin jagorantar babbar kungiya irin ta Juventus, wadda ta lashe gasar Seria A sau takwas a jere.

Bukatar da Juventus ke da ita

Kasancewar kungiyar Juventus ta lashe gasar Seria A sau takwas a jere, kuma tana cin karenta ba babbaka a kasar, sai ya kasance kungiyar tana da bukata mai girma na fadada ikonta zuwa nahiyar Turai da ma duniya baki daya.

A yanzu Juventus ba gasar Seria A take bukata ba, Zakarun Turai take bukatar ta lashe, kuma akwai kalubale babba a gabansa wajen cimma bukatar kungiyar.

Hada kan ’yan wasa

Kasancewar kungiyar Juventus na da manyan ’yan wasa irinsu Cristiano Ronaldo da Paulo Dybala da Gonzalo Higuan da Buffon wanda ya girmi kocin a yanzu da shekara daya.

Wasu daga cikin magoya bayan Juventus sun zargi tsohon kocin kungiyar, Sarri da rashin iya amfani da tulin ’yan wasan kungiyar, inda a lokuta da dama ya gaza iya hada Ronaldo da Dybala da Higuan a lokaci daya, musamman idan ana kwallo ruwa a jallo.

Kasancewar ya buga kwallo da wasu daga cikin ’yan wasan, kuma dan wasa ne shi da duk da cewa kwararre ne da ya yi fice a duniya, amma ana masa kallon bai kai kamar su Zidane ba da suka lashe gasar Gwarzon Dan Wasa na duniya. Don haka ake ganin zai fuskanci kalubale daga manyan ’yan wasan kungiyar.

A lokacin da yake taya abokinsa murna, Gennaro Gattuso wanda yanzu yake horar da ‘yan wasan Napoli, ya ce duk da cewa Pirlo kwararren dan wasa ne, hakan ba ya nufin zai zama koci nagartacce.