Kama Dokta Nazif Yunus: Za a iya fakewa da Boko Haram a kama kowane Musulmi – Al-Mannar

Sheikh Muhammad Adam Tukur Al-Mannar babban Limamin Masallacin Al-Mannar da ke Unguwar Rimi Kaduna, aminin Dokta Nazif Yunus ne da jami’an tsaro suka gabatar a makon jiya cewa dan Boko Haram ne. Malam Tukur ya ce kama shi wata manuniya ce ta za a iya kama kowane Musulmi da sunan Boko Haram:   Aminiya: Me […]

Kama Dokta Nazif Yunus: Za a iya fakewa da Boko Haram a kama kowane Musulmi – Al-Mannar

Sheikh Muhammad Adam Tukur Al-Mannar babban Limamin Masallacin Al-Mannar da ke Unguwar Rimi Kaduna, aminin Dokta Nazif Yunus ne da jami’an tsaro suka gabatar a makon jiya cewa dan Boko Haram ne. Malam Tukur ya ce kama shi wata manuniya ce ta za a iya kama kowane Musulmi da sunan Boko Haram:

 

Aminiya: Me Malam zai ce dangane da salon da jami’an tsaro suka dauka a yanzu na kama mutane da sunan ’yan Boko Haram ne?
Al-Mannar: Kama mutum ko a gayyace shi domin ya je a yi bincike ya amsa wasu tambayoyi ba laifi ba ne. Shi ya sa aka kira su jami’an tsaro domin su kare duk wani al’amari da ka iya tasowa. Wani ya je ya yi laifi sai ya ce da Malam Tukur a ciki ka ga ba zai hana a zo a tambaya ba, ko na san shi kuma a ina na san shi? Domin ga abin da suka yi suka ce da ni a ciki. Don an nemi in je in amsa tambayoyi babu laifi a ciki. Saboda ana kiran mutum ‘Almuhtammu’ wanda ake tuhuma. Sai dai salon kamawar ya zama akwai girmamawa. Kamawar ta zamanto kamawa ce ta mutunci. Wane mu je ana bukatarka ko ana gayyatarka ko kwamishina ko DPO na gayyatarka wannan a duk duniya babu laifi a ciki. Amma a zo da daddare an fasa kofa kuma a buga maka ankwa a hannu da kafa ana jan ka a gaban iyalanka a ganina irin wannan kamu bai yi ba. Amma kamun yawanci akwai tozartawa da wulakanci da cin mutunci a ciki. Abu na gaba shi ne idan bincike ne na adalci da za a yi sai a bincika a tsare mutum a tabbatar ya yi ko bai yi ba, bisa hujjoji da adalci wannan duk babu laifi a kasa da kuma a hukumance. Amma a rike mutum a yi ta wulakanta shi tun ba a tabbatar da ya aikata laifin ba wannan ya saba wa mutuntaka da ’yancin dan Adam. Sannan kafin a kama mutum jami’an tsaron nan akwai SSS da ’yan sanda da sauransu wadanda ko tashar motar ka je za ka same su. Ko filayen kwallo ka je suna nan ballantana masallatai da wuraren wa’azi ko tarurruka ko lacca. Duk jami’an tsaro suna nan.
In mutum ma an ce a maganarsa ne ya fadi kaza ko ya furta kaza. Su jami’an tsaron babu lacca ko wa’azi da za a yi a samu ba sa nan. Saboda haka tun farko idan wanda ake kamanta shi da wannan laifi ne sun fi kowa sanin tarihinsa. In kuma ba wanda ake kamantawa ba ne sun fi kowa sani. Saboda haka mutum ba sai ya dade a hannunsu ba. Akwai wanda za a fada musu sunansa da sun ji za su ce a’a wane ba irin wadannan mutane ba ne a iya saninmu. Daga wannan lokaci ne ya kamata su ce karya ne su kuma sake mutum. Sannan a ce yana ba da makudan kudi ina bankin mutumin nan inda yake ajiye kudi. Malami ne na makaranta ko wanda ake biyansa albashi. A cikin makarantun duk mun san cewa akwai wadanda suke zuwa makarantu a matsayin dalibai alhalin kuma jami’an tsaro ne.
Aminiya: Me za ka ce game da kama Malam Muhammad Nazifi Yunus da jami’an tsaron SSS suka yi kwanan nan?
Al-Mannar: Malam Nazifi mun yi karatu da shi a Jami’ar Madina yau kusan shekara 23 da suka wuce. Ya karanci fannin Alkur’ani da Addinin Musulunci. Shi da marigayi Sheikh Ja’afar Adam sashinsu daya, Malam Ja’afar na gabansa da shekara daya.  Ni kuma shekara daya muka shiga jami’a amma ina sashin karantar shari’a ne. Na kuma san malam Nazifi sosai domin abokina ne a jami’a har muka kammala karatunmu. Bayan mun dawo Najeriya sai ya je ya kara digirinsa na biyu a Jami’ar Jos ya kara digiri na uku wato P.hd a Jami’ar Jihar Kogi.  Ka ga duk wannan karatu da ya yi ai na boko ne, idan kuma yana adawa da bokon ba zai yi su ba. Sannan Malam Nazifi limami ne na Juma’a an san hudubobinsa da wa’azozinsa. Haka Malam Nazifi Shugaba ne na Kwalejin Al-Bayan da ke Jos. An kona makarantar har sau hudu zuwa sau biyar. An kona ta a lokacin tana hanyar Bauchi zuwa Zariya, an kuma kona masu gadinta. Haka an kona ta a Goron Dutse, an kuma sa dalibanta yara a cikin mota da ma’ajiyar ruwa an kona su. Babu wanda ya kama wadanda suka aikata wannan laifi a matsayin ’yan ta’adda. Bayan haka Malam Nazifi ya kamata a sani cewa a nan yake da iyalansa da ’ya’yansa, a nan garin ya yi aure kuma nan yake neman abincinsa. Saboda haka babu wani mai hankali da zai janyo bala’i a marayarsa. Ya janyo bala’i da masifa a inda yake rayuwa inda kuma matansa da ’ya’yansa ke rayuwa.
Saboda haka irin karatun da ya yi ko muka yi ba karatu ne na ta da hankali ba, domin mun fi kowa sanin tarihi da yadda duniya take kafin Manzon Allah (SAW) da yadda aka aiko shi da yadda ya kawo kwanciyar hankali da zaman lafiya. Da yadda Manzon Allah (SAW) ya zauna da Yahudawa da Kiristoci da kafirai da maguzawan Larubawa masu bauta wa gumaka ya kuma zauna da manafukai sannan ya kuma zauna da masoya da kuma makiya, ya kuma zauna da ’yan birni da ’yan kauye.
Yadda ake kama mutane ban ce laifi ba ne amma babban abin da ake kallo shi ne adalci da yanayin da za a kama da kuma yanayin da za a yi ta gallaza maka kafin a tabbatar haka ne ko ba haka ba ne. Idan an tabbatar mutum ba ya da lafi sai a sako shi ya koma cikin iyalinsa kuma a fito a bayyana a rediyo da jaridu cewa an wanke shi daga wannan zargi.
Yanzu salon da abin ke dauka shi ne watakila mutum makiyinka ne watakila kuma ba Musulmi ba ne ya zo ya manna maka abu kuma a shirya shaidu. Ka duba kamar Manjo Al-Mustapha yadda wani ya je ya ba da shaidar karya da daga baya ya fito ya fadi irin gidaje da abubuwan da ya ce an yi masa alkawari za a ba shi idan ya ba da shaidar cewa Al-Mustapha ne ya kashe Kudirat.
Idan har masu bincike ko gwamnati da jami’an tsaro za su zamanto haka kawai don a bata sunan mutum saboda malamin Musulunci ne su jingina masa Boko Haram. Haka kawai domin yana da’awar addinin Musulunci ko wa’azin da bai yi musu ba, saboda ba sa son gaskiya wannan tsabar zalunci ne. Kuma ko ba jima ko ba dade wannan zalunci Allah zai magance masu yi. Yadda Allah Ya ba ka matsayin jami’in tsaro ko a matsayinka na Gwamna ko Shugaban kasa, Allah Yana sama da kai.
Kiran da muke yi shi ne su wadanda ake daukowa a matsayin shaidun karya su sani cewa wannan abu ba mai sauki ba ne, domin Allah zai kama su. Wannan zamani ne na jarrabawa, ba mu da abin da za mu ce sai addu’a da fada wa Allah da kira a rika yin adalci ba mu da karfin da za mu fito mu fuskanci hukuma ko ta hanyar yin zanga-zanga ko kone-kone, sai dai muna kira ga hukuma ta rika sara tana duban bakin gatari. In dai haka za ta rika yi haka siddan a bisa zalunci a kama mutum to, akwai ranar da Allah zai damke ta.
Aminiya: A tsawon lokacin da ka san Malam Nazif ko yaya za ka kwatanta halayensa?
Al-Mannar: Muhammad Nazifi yana da mata biyu kuma shugaba ne na Kwalejin Al -Bayan kuma ya yi shekaru 20 yana rike da wannan wuri. Malami ne a Jami’ar Jihar Kogi. Mutum ne mai kawo zaman lafiya a cikin hudubobinsa, yana da kyawawan halaye yana da tsantseni. Mutum ne ban san shi da alfasha ko fasikanci ko mu’ala da kudin haram ba, mutum ne hafizi na Alkur’ani, mutum ne da ya amfani al’umma kwarai da gaske kuma al’umma sun amfana daga gare shi, daga ’yan boko da masu karatun addini, akwai wadanda suka haddace Alkur’ani da yawa a tare da shi. ’Yarsa Summayya ma ta haddace Alkur’ani. Kuma Nazifi yana daya daga cikin masu yaki da duk wani abu da zai kawo rashin zaman lafiya ko kwanciyar hankali. Malam Nazifi ya sha zuwa gidan talabijin na NTA Jos da PRTb Jos duk a kan tattaunawa kan yadda za a kawo zaman lafiya a Jos. An kuma sha zama da shi a kan yadda za a samu zaman lafiya a tsakanin Kiristoci da Musulmi. Sannan ya yi NYSC kuma ya zamanto Amir na MCAN a nan Jos.
Kamar yadda nake fada maka su jami’an tsaron na SSS idan ba son zuciya ba, sun fi sanin take-taken kowa. In kuma ba su sani ba ya nuna ke nan ba su san aikinsu ba. Shi ya sa nake mamaki har suke barin abu ya yi girma har ta kai da an zubar da jini. Saboda haka kiran da muke yi shi ne a yi adalci, duk wanda yake ji da karfin soja ko mulki da karfin jami’an tsaro zai ci mutuncin Musulmi da zaluntarsu, musamman malamai mahaddata Alkur’ani to, ina ganin bai kai rabin Fir’auna ba. Kuma Allahn da ya gama da Fir’auna Ya tserar da Annabi Musa da mabiyansa Rayayye ne ba Ya mutuwa. Saboda haka muna kira da a rika yin adalci a kuma kula da makiyan mutum.
Aminiya: Yaya ka ji lokacin da ka samu labarin an kama shi?
Al-Mannar: A lokacin da aka kama shi na tafi aikin Hajji, amma da na dawo na samu cikakken bayani, gaskiya ban yi barci ba. Kuma ban yi mamaki ba, saboda tunda aka fito da zancen Boko Haram din nan kowa ake son kamawa in dai shi Musulmi ne za su iya yin amfani da abin domin a kama shi. Ina lillahi wa inna ilaihi raji’um kawai na yi, na kuma mayar da al’amarina zuwa ga Allah.