Kama jirgin Oritsejafor makare da kudi: Lauya Festus Keyamo ya nuna shakku kan hujjar gwamnati

Lauya mai zaman kansa, Festus Keyamo ya bayyana shakkunsa dangane da hujjojin da Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayar game da kama ’yan Najeriya da aka yi da Dala miliyan 9.3 a Afirka ta kudu za su sayo makamai, inda ya fitar da wata takarda mai dauke da tambayoyi goma sha daya kamar haka:1-Shin wace hanya […]

Kama jirgin Oritsejafor makare da kudi: Lauya Festus Keyamo ya nuna shakku kan hujjar gwamnati

Lauya mai zaman kansa, Festus Keyamo ya bayyana shakkunsa dangane da hujjojin da Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayar game da kama ’yan Najeriya da aka yi da Dala miliyan 9.3 a Afirka ta kudu za su sayo makamai, inda ya fitar da wata takarda mai dauke da tambayoyi goma sha daya kamar haka:
1-Shin wace hanya ce ta fi sauri da saukin gudanar da cinikayyar da ta shafi kasa da kasa? Ta hanyar daukar makudan kudi ko kuwa ta hanyar sakon kar-ta-kwana, wanda zai iya isa cikin mintoci ko awoyi kadan?
2-Idan har al’amarin nan ya danganci tsaron kasa kamar sayo makamai ga kasa kamar Najeriya, me ya sanya ba a sanar da Gwamnatin Afirika Ta Kudu ba tun da farko? Ta yaya Gwamnatin Afirika Ta Kudu za ta samu tabbacin cewa makaman an sawo su ne bisa ka’ida don amfanin Gwamnatin Najeriya, ba don ’yan ta’adda ba, tun da ba a sanar da ita haka ba tun da farko?
3-Idan har masu kera wadannan makamai suna da masaniyar za su amshi wadannan kudi masu yawa haka a hannu, me ya sa ba su yi shiri na musamman suka sanar da hukumomin Afirika Ta Kudu ba a lokacin da mutanen suka sauka kasar?
4-Me ya sanya za a yi amfani da jirgi mai zaman kansa kuma da mutanen da ba ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ba wajen daukar makudan kudi da nufin safarar makamai? Kuma me ya sanya ba a hada mutanen tare da wasu ’yan rakiya daga jami’an tsaro na farin kaya ko kuma na Ofishin NSA, kamar yadda tsarin aiki ya tanada ba?
5-Me ya sanya gwamnatin da ta fito da tsarin amfani da bankuna wajen mu’amalar kudi masu yawa amma kuma ta zama babbar mai karya dokar tsarin da kanta, ta bari aka fitar da makudan kudi haka?
6-Idan har wannan harka ta gaskiya ce daga Gwamnatin Tarayya, me ya sanya ba a sanya jami’an Ofishin Jakadancin Najeriya a Afirika Ta Kudu, domin su shiga batun, don sama wa mutanen saukin tafiyar da al’amarin ba?
7-Kasancewar Gwamnatin Afirika Ta Kudu ta ce adadin kudin sun zarce abin da dokar kasarta ta amince a shiga da su, me ya sa gwamnatin babbar kasa kamar Najeriya ba ta san da wannan dokar ba, duk kuwa da cewa aminai ne kuma suna dasawa da juna, da har za ta bari aka kai irin wadannan adadin kudi zuwa kasar?
8-Me ya sanya Gwamnatin Najeriya za ta yi amfani da hanyar fasa-kwauri wajen shigar da kudi zuwa wata kasa, idan dai da gaske harkar ta halal ce?
9-Daga ina Gwamnatin Tarayya ta samo wadannan adadin kudi a Najeriya? Daga Babban Bankin Najeriya ne ko kuwa daga kasuwar bayan fage? ’Yan Najeriya na neman hujja.
10-Shin yaya aka yi ma har aka yi amfani da jirgin abokin Shugaban kasa, wato Fasto Ayo Oritsejafor wajen fasa-kwairin kudin?
11-Idan da a ce wani kamfani ne mai zaman kansa aka ba kwangilar nan, kuma ya yi amfani da kudi-hannu wajen tafiyar da ita, shin ba za a kama shi da laifin safarar kudi ba, kasancewar ba a tafiyar da kwangilar ta hanyar hukumomin kula da al’amuran kudi ba?

‘Kudin makaman gwamnati ne ‘
A ta bangaren gwamnati kuwa, a Talatar da ta gabata ce aka samu bayanin da ke tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya ta fitar da bayanin da ke nuna cewa da saninta ne aka fitar da wannan adadin kudi da nufin sawo mata makamai.
Kamar yadda majiyar PRNigeria ta sanar, ta ruwaito wani babban jami’in gwamnatin Najeriya, wanda ya ce ya zuwa yanzu gwamnatocin Najeriya Da Afirika Ta Kudu suna musayar bayanai da nufin warware al’amarin cikin difilomasiyya. Ya bayyana cewa matsalar ta faru ne, inda Gwamnatin Afirika Ta Kudu ta tuhumi ‘kin bayyana kudin’ da jami’an Najeriya suka yi a matsayin laifi.
“Ya zuwa yanzu, Najeriya da Afirika Ta Kudu suna gab da warware matsalar da ta faru a tsakaninsu dangane da kudi Dala miliyan tara da digo uku. kasashen biyu sun shiga tattaunawa kan al’amarin.” Kamar yadda kafar dillancin labarai ta PRNigeria ta ruwaito wani jami’in gwamnatin Najeriya.
Bayanin PRNigeria ya ce: “Gwamnatin Najeriya ta aika da cikakkun takardu dangane da al’amarin zuwa Afirika Ta Kudu kuma wannan harka tana kan ka’ida, ba haramtacciya ba ce. Gwamnatin kuma ta kara hasken cewa kudin nan kuma ba haramtattu ba ne, don haka ba fasa-kwaurinsu aka yi ba da nufin yin wani abu marar kyau. Babu wani dan tu’ammali da haramtacciyar dukiya da ya isa ya bugi gaba ya ce zai dauki shatar jirgi dauke da dukiya mai yawa haka, ya ce zai shiga wata kasa.”
Wani hafsan soja kuma ya bayyana wa Premium Times cewa dole ce ta sa gwamnati bin barauniyar hanya domin sayo makamai saboda kasar Amurka tana ta yi wa kasar nan makarkashiya a duk lokacin da take kokarin sayo makamai. A ganinsa Amurka tana yin haka ne domin cimma burinta na ganin kasar nan ta wargaje, kamar yadda ta yi hasashe.

Jirgina ne aka kama makare da kudi a Afririka Ta Kudu  – Oritsejafor
 Shugaban kungiyar Kiristoci Ta Najeriya (CAN), Fasto Ayo Oritsejafor ya barranta kansa daga badakalar nan da ta faru a Afririka Ta Kudu, inda aka kama wasu ’yan Najeriya biyu tare da wani dan kasar Isra’ila dauke da kudi, Dala miliyan tara da dubu dari uku da nufin sawo makamai, amma ya amince cewa jirgin da aka kama nasa ne
Mutanen uku dai sun shiga Afirika Ta Kudu ne a ranar 5 ga Satumba, inda aka same su dauke da kudin da suka kai kimanin Naira bilyan daya da rabi a jakarsu. Hukumomin kasar sun kwace kudin ne saboda ba su gabatar da su ga hukuma ba, sannan kuma adadinsu ya ketare abin da doka ta amince da shi a ka’ida, kamar yadda hukumomin Afirika Ta Kudu suka bayyana.
A Talatar da ta gabata ce Cocin Oritsejafor ya fitar da bayanin cewa lallai Shugaban CAN yana da hannun jari a kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Eagle Air, mai mallakra jirgin da aka kama a Afirika Ta Kudu da makudan kudi, amma dai ba ya da hannu cikin al’amarin da ya shafi kudin, domin kuwa an bayar da hayar jirgin ne ga wani kamfani na daban.
“Cocin The Word of Bible Church ya samu labarin da kafafen watsa labarai ke watsawa dangane da jingin sama (Bombardier Challenger 600, mai lamba N808HG), mallakar kamfanin Eagle Air, inda fastonmu, Fasto Ayo Oritsejafor yake da hannun jari.” Inji sanarwar da Bayo Adewoye ya sanya wa hannu.
“A madadin Fasto Oritsejafor, muna tabbatar da cewa duk da cewa yana da hannun jari a kamfanin Eagle Air amma shi wannan jirgin ba Fasto Oritsejafor ne ke amfani da shi ba. Shi wannan jirgi, tun daga ranar 2 ga Agustan bana aka ba da hayarsa ga kamfanin Green Coast Produce Limited. Kuma wannan bai saba wa ka’idar harkar zirga-zirgar jiragen sama ba ta duniya. Duk wani bayani na yau da kullum game da jirgin ana jingina shi ne ga hukumar gudanarwar kamfanin Green Coast Produce Limited. Za mu yi farin ciki mu taimaka wa hukumomi da dukkan bayanin da suke nema.”
A nasa bangaren, shi ma kamfanin Green Coast Produce Company Limited ya fitar da nasa bayanin na daban a Talatar da ta gabata, inda ya bayyana cewa ya bayar da hayar jirgin ne ga wani mutum mai suna John Ishyaku, kuma ba su da masaniyar kayan da ya yi safara da shi.
“Mu kamfanin Green Coast Produce Company Limited, mun amshi hayar jirgin sama, Bombardier Challenger 600, mai lambar rijista N808HG, a ranar 2 ga Agusta da ya gabata. Tun daga wannan rana muke amfani da jirgin wajen zirga-zirga, kamar yadda dokar harkar sufuri ta duniya ta tanadar.” Inji sanarwar, wacce Dokta Shima Adun ya sanya wa hannu.
“A ranar 5 ga watan Satumba da muke ciki, John Ishyaku ya amshi hayar jirgin bisa wadannan rubutattun sharudda: (a) Zai tashi daga Abuja zuwa Johanessburg a ranar 5 ga Satumba na bana. (b) Zai dawo Abuja a ranar 6 ga Satumba na bana. (c) Zai jira har ya samu fasinjoji, ya dawo da su. Wadannan sharudda kuma suna kan hanya kamar yadda harkar sufurin jirgi ta amince. Kamar yadda ake tafiyar da kowane kamfanin sufurin jirgi, kayan da aka dauka a cikin jirgin ya ta’allaka ne da bayanin da John Ishyaku ya ba mu. Duk wani kaya a jirgi, za su kasance ne tare da mai su, wanda shi zai iya ba da bayaninsu.  Ba za mu kasance masu laifi ko mu yi tarayya da kayan da ake zargi ba a cikin jirgin, ko a Najeriya ko kuma Afirika Ta Kudu. Abin da muka sani kawai shi ne sharuddan da muka kulla na bayar da hayar jirgin.
“Da zarar mun bayar da haya, jirgi ya bar hannunmu, ba mu da alhaki kuma ba za mu iya zama tare da abin da ake zargi na laifi ba, ko dai a nan Najeriya ko kuma Afirika Ta Kudu ba.”