Kama matashiya kan sukar Gwamnan Sakkwato ya tayar da ƙura

Kama matashiya Hamdiyya Sidi kan sukan Gwamnan Sakkwato Dakta Ahmad Aliyu ya bar baya da kura, musamman a kafofin sada zumunta, inda a wasu ke ganin gaskiya ce ta faɗa da ƙoƙarin janyo hankalin gwamnati kan matsalar tsaro da Ƙaramar Hukuma Wurno a Gabashin Sakkwato ke fuskanta. Hamdiya a wani bidiyo da ke yawo a […]

Kama matashiya kan sukar Gwamnan Sakkwato ya tayar da ƙura

Gwamnan Jihar Sakkwato Ahmad Aliyu

Kama matashiya Hamdiyya Sidi kan sukan Gwamnan Sakkwato Dakta Ahmad Aliyu ya bar baya da kura, musamman a kafofin sada zumunta, inda a wasu ke ganin gaskiya ce ta faɗa da ƙoƙarin janyo hankalin gwamnati kan matsalar tsaro da Ƙaramar Hukuma Wurno a Gabashin Sakkwato ke fuskanta.

Hamdiya a wani bidiyo da ke yawo a lokacin da ta je garin Sabon Birnin Daji a wata ziyara da ta kai a garin mahaifiyarta, ta ce “Ahmad Ali matsayinka na mai hankali mai ilimi, shugaba, uba kuma Musulmi, ka san gaskiya, namiji kake ya za ka ji a ce wani ya tsallako gidanka, ɗakinka wani ya kwanta da matarka ta sunna, kai ma da zuciya a kirjinka.

“Matsayinka na uba a ce wani namiji ya tsallako ya kwanta da ’yarka, shin ka taɓa kwatanta irin abin da waɗannan bayin Allah ke ji? Tun sanda waɗannan abubuwan ke faruwa wani naka bai taɓa zuwa ya yi masu jaje a Sabon Birnin Daji ba,” in ji Hamdiyya.

Bayan bayyanar bidiyon ne aka samu labarin ’yan sanda sun kama matashiyar kan zargin ta zagi gwamna, inda wasu mutane suka zargi gwamnan ne ya sa aka kama ta don ta soke shi kan matsalar tsaro
da ta addabi mutanen yankin.

Rundunar ’yan sandan Jihar Sakkwato ta fitar da wani bayani wanda kakakinta, ASP Ahmad Rufa’i ya ce “hankalin rundunar ’yan sandan ya karkato kan wata ƙarya da shaci faɗi da ake yaɗawa a kafofin sada zumunta da sauran kafafen yaɗa labarai cewa rundunar ’yan sandan Sakkwato a asirce ta kama wata mata saboda ta soki Gwamnan Sakkwato Alhaji Ahmad Aliyu.

Kawo mana ita aka yi —’Yan sanda

“Wannan ƙarya ne kuma shaci faɗi ne, yadda lamarin yake shi ne, a ranar 3 ga watan Nuwamban nan, Marafa Yakubu, Hakimin Sabon Birnin Daji a Ƙaramar Hukumar Wurno ya kawo bayani wurin ’yan sanda cewa wata mata da ake kira Hamdiyya Sidi wadda ita ‘yar Ƙauyen Munki ce duk a karamar hukumar, ta zo ƙauyensa ta yaudare shi inda ta gaya masa ita tana cikin ƙungiyoyin da ke tallafa wa al’umma, don haka ta zo nan don ta taimaki mata da matasa, tana son ta yi masu jawabi sannan a tallafa wa marasa karfi.”

Ya ce a lokacin da take yi masu jawabi ne ta yi kalaman fusata matan ga gwamnati hakan ya haifar da ruɗu a cikin jama’a, sai jami’an tsaron yankin suka kama ta suka mika ta hannun ’yan sanda.

An kai ta kotu

Jami’in hulɗa da jama’an ya ce wadda ake tuhumar a lokacin da take wurinsu ta amsa laifinta na haifar da ruɗu a cikin al’umma daga nan suka kaita kotu a cikin awa 24.

Ya ce dokar kasa ta ɗora masu alhakin bincikar ƙanana da manyan laifukka, don haka abin da ya shafi Hamdiyya ba zai fita daban ba.

Ya yi kira ga mutane su daina yaɗa karya domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin al’umma.

Ta sha dukan kawo-wuƙa

Aminiya a kokarinta na son magana da matashiyar ta tuntuɓi wani makusancinta don samun damar a yi magana da ita, amma ya ce ba zai yiwu ba.

“Abin da nake faɗa maka a yanzu Hamdiyya ba ta iya magana tana kwance ba ta da lafiya domin a satin da ya gabata ne wasu matasa suka ɗauke ta suka yi mata duka har ba ta san in da take ba sannan suka kyale ta, a haka wasu suka zo aka kai ta asibiti, in dai ta samu sauki za ka yi fira da ita.”

Shugaban Rundunar Adalci reshen Sakkwato, Bashir Altine Guyawa ya ce, “yarinyar ta yi kalamai kan halin da Gabashin Sakkwato yake ciki na taɓarɓarewar tsaro da cin zarafin da ake yi, ta jawo hankalin gwamnati da gwamnan Sakkwato ya yi abin da ya dace.

“Mu muna tare da kalamanta duk wanda zai tausaya wa mutanen Gabashin Sakkwato na kalaman alheri da jin kai, ba shakka muna tare da shi.

“Bayan ta yi kalaman ne aka kama ta a garin Acida bayan ta kwana a hannun ’yan sanda aka kai ta gaban alkali, ya karanta mata tuhumar da ake mata ya kuma bayar da ita beli ba, shakka ya tausaya.

“Da ta koma gida ne a garin Acida ta fito za ta kai waya caji wasu matasa suka kama ta da duka suka ɗaure ta hannu da kafa suka kawo ta hanyar shigowa birnin jiha (road block) suka jefar, a nan ne aka kai ta asibiti.

“A yanzu tana samun kulawa a wani wuri a ɓoye ganin yadda ake neman rayuwarta, tana shan magani. Mun nemi ƙungiyoyin agaji na duniya su shiga lamarinta.”

Rashin kunya ne —Gwamnati

Mataimaki na musamman ga gwamnan Sakkwato kan lamurran cikin gida, Faruku Labbo ya yi magana kan matashiyar ya ce “wannan ba ’yar Sakkwato ba ce ba Hausar Sakkwato take yi ba, kawai aiki ya kawo ta NGOs ta tafi wannan ƙauyen, ita kawai labari ta samu, maganar tsaro ba wata gwamnati a Nijeriya da ke ɗaga wa Gwamnatin Ahmad Aliyu hannu kan harkar tsaro,” in ji shi.

Ya ce “duk abin da ya kamata gwamna ya yi ya aiwatar da shi, wannan fitina ce ta duniya kowa ya sani, saboda haka bai kamata a sanya siyasa ciki ba, kowa ya taka tasa rawa.

“Maganarta gaba ɗaya babu biyayya a ciki, ba wata tsararta da za ta iya yin kalaman da ta yi a Sakkwato, gwamna bai sa a kama kowa ba, mutanen da ta yi magana a ƙauyensu mai garin shi ne ya sa a kama ta don za ta kawo masa tashin hankali a kasa, gwamna bai san an kama ta ba.”

Lucky Aiyedatiwa ya lashe zaɓen Gwamnan Ondo

Ba na yi wa Tinubu hassada — Atiku

Kama matashiya kan sukar Gwamnan Sakkwato ya tayar da ƙura

Babban Limamin Minna Sheikh Isa Fari ya rasu