Kama mutanenmu da ake yi yana damunmu -Sarkin Hausawa
Sarkin Hausawan unguwar Biktoriya Ailan da ke Jihar Legas, Alhaji Yakubu Bala ya ce, kamen ’yan Arewa da jami’an tsaro suke yi a yankinsa shi ne yake ci masa tuwo a kwarya.Alhaji Bala Yakubu ya yi furucin ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya a karshen makon da ya gabata.Ya ce ‘Mu ba mu da […]
Sarkin Hausawan unguwar Biktoriya Ailan da ke Jihar Legas, Alhaji Yakubu Bala ya ce, kamen ’yan Arewa da jami’an tsaro suke yi a yankinsa shi ne yake ci masa tuwo a kwarya.
Alhaji Bala Yakubu ya yi furucin ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya a karshen makon da ya gabata.
Ya ce ‘Mu ba mu da wata matsala a yankin Biktoriya Ailan muna zaune lafiya da mutanenmu da Yarabawa da sauran kabilu sai dai matsalar da ke damunmu ita ce yadda jami’an tsaro suke zuwa su kama mutanenmu. Za ka ga sun shigo cikin dare mutum yana barci a kama shi ba tare da ya aikata wani laifi ba. Mun yi korafe-korafe, amma ba su daina ba sai da a kwanakin baya aka kawo wani jami’in ’yan sanda shi ne muka samu saukin abin’.
Ya ci gaba da cewa ‘Muna so jami’an tsaro su sani babu yadda za mu yarda wani bata gari ya zo ya zauna a cikinmu. Duk wanda ya zo sai mun bincike shi mun yi masa binciken kwakwaf mun tabbatar mutumin kirki ne sannan mu yarda ya zauna a cikinmu. Abinda muka sani mutanenmu masu sana’a ne ba masu zaman banza ba kuma mutane ne masu bin doka da oda’.
Ya bayyana cewa matakin da gwamnatin jihar Legas ta dauka dangane da tsaro da hadin gwiwa da sarakunan Hausawa na jihar ya dace.
Sai dai ya ce ya kamata a rika taka –tsatsan don kada a rika musgunawa wadanda ba su ji ba ba su gani ba.
Alhaji Yakubu ya ce ya fi shekara 30 yana gudanar da sana’ar fawa a yankin Biktoriya Ailan.
Sai dai rundunar jihar Legas ta ce ba kowa take kamawa ba sai wanda take zargi da aikata laifuka.