Kamal Alkali ya bukaci ’yan fim su guji kalaman batanci
Shahararren Daraktan Fina-Finan Hausa, Kamal Sani Alkali ya bukaci ’yan fim su guji kalaman batanci a kafafen sadarwa da suka hada da facebook da twitter da kuma Instagram. Daraktan ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Instagram a ranar Lahadin da ta gabata. Idan ba a manta ba dai […]

Shahararren Daraktan Fina-Finan Hausa, Kamal Sani Alkali ya bukaci ’yan fim su guji kalaman batanci a kafafen sadarwa da suka hada da facebook da twitter da kuma Instagram.
Daraktan ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Instagram a ranar Lahadin da ta gabata.
Idan ba a manta ba dai a kwanakin baya magoya bayan fitattun jaruman fina-finan Hausa, Ali Nuhu da kuma Adam Abdullahi Zango sun yi yakin cacar baki a kafafen sadarwa na zamani, inda har hakan ya taba dangantakar da ke tsakanin jarumin, kafin a kai ga yi musu sulhu.
Sai dai duk da an yi sulhun magoya bayansu da kuma yaransu sun ci gaba da yin musayar yawu, al’amarin da ya sanya Darakta Kamal ya yi kiran ke nan.
Ya ce, ya kamata abokan sana’arsa ta Kannywood su daina kalaman tsanar juna a kafar Instagram, domin ba hakan ba ne abin da mabiyansu suke jiran gani a wajensu ba.
Ya ce, “Ina amfanin rura wutar gaba ta hanyar post, duniyar ma nawa take? Ba mu san ranar mutuwarmu ba. In ka aibata wani ka yi masa gugar zana da cin fuska a shafinka, sannan jimawa kadan ka mutu, kana jin zai yi maka fatan alheri?”
Daraktan ya bukaci ’yan uwansa su rika hakuri da nuna dattaku da kuma yafiya da afuwa idan wani ya yi musu laifi.
“Mu daina dauka ba za a bata mana ba, mu zama cikin zaton za a yi mana laifi za mu yi. Idan halin mutum bai yi maka ba, ka kauce masa duniya da fadi. Na yi tir da mummunan post, ba na yi. Nasiha ce a kara hakuri,” inji shi.