Kamale: Miloniyan da ’yan Boko Haram suka mayar dan tallar jarida
Rayuwar Solomon Dali Kamale, rayuwa ce mai daga hankali da ban takaici. Solomon Kamale wani miloniya ne mai harkar man fetur da yake da jarin fiye da Naira miliyan 24 da gida na a gani-a-fada a birnin Maiduguri da sito-sito hudu da motocin kasaita guda hudu. Sai dai abin ban tausayi yanzu ya koma tallar […]

Rayuwar Solomon Dali Kamale, rayuwa ce mai daga hankali da ban takaici. Solomon Kamale wani miloniya ne mai harkar man fetur da yake da jarin fiye da Naira miliyan 24 da gida na a gani-a-fada a birnin Maiduguri da sito-sito hudu da motocin kasaita guda hudu. Sai dai abin ban tausayi yanzu ya koma tallar jaridu da rayuwarsa ta fi dogara da isowar jaridar Daily Trust don sayarwa ya samu abin da zai ci shi da iyalinsa da kuma kula da iyalinsa mai ’ya’ya tara.
Kamale, tare da matarsa da danginsa 18 da suke karkashinsa a yanzu suna sansanin ’yan gudun hijira da ke Kamfanin kusa a Maiduguri suna gudanar da rayuwa da taimakon da suke samu daga sansanin.
“Matsalata ta faro ne a wata rana a shekarar 2012 lokacin da aka kawo min man fetur tireliya uku daga daffon Kamfanin NNPC na Maiduguri. Mun sayar da kusan dukkan man a ranar. Ban mallaki gidan mai ba, ina haya ne a gidan man Alhaji Ibrahim Maikore da ke hanyar Baga a birnin Maiduguri. Muna sayar wa masu motoci da kuma ’yan kasuwar bayan-fage da suke saya a durom-durom. Kuma ina da yara da dama a karkashina,” inji Kamale.
Ya kara da cewa: “Akwai wadansu yaran da suke aiki a karkashina da mutane suka rika cewa ’yan Boko Haram ne. Sai dai ba ni da shaida a kan haka duk da cewa an ci gaba da yi wannan zargi. Domin a wancan lokaci da ’yan Boko Haram suke Maiduguri da wuya ka iya gane su wane ne da wane ne. To mun sayar da fiye da man fiye da tirela biyu muna da miliyoyin Naira sannan yamma ta yi ba za mu iya zuwa banki ba. Sai na kira manajana wanda yake aiki da yayansa a gidan man na ce masa ya boye kudin a cikin wuraren ajiye kaya na tirelolin da na motocin da suka lalace da kuma cikin ofis mu bar gidan man.”
Kamale ya ci gaba da cewa: “Na shawarce shi cewa kada ya kwana a gidansa a wannan rana. Ya je ya nemi wani wuri ya kwana amma sai yayansa ya yi dariya ya ce na cika tsoro. Ya ce su tafi gida babu abin da zai faru. Sai suka boye kudin suka tafi da kusan Naira miliyan daya.”
Solomon Kamale ya kara da cewa: “Da daddare da misalin karfe daya, sai matata ta tashe ni ta ce wadansu mutane suna kokarin balle kofarmu. Kwatsam, sai na ji murya na cewa idan ba ku bude kofa ba, in muka balle muka shigo za mu kashe ku. Sai na matsa kusa da kofar na ce musu mai gidan ba ya nan. Sai biyu da suke bakin kofar suka tambaye ni, ni wane ne? Sai na shaida musu cewa ni maigadi ne, matata tana jin mu daga cikin daki. Sai maharan suka umarce ni cewa in bar gidan jim kadan bayan sun shigo ciki.”
“Sai na fita cikin gaggawa zuwa daya gidana da ’yan haya ke ciki na shaida musu cewa akwai mahara a daya gidan nawa don haka duk su gudu. Cikin mintoci kadan sai ’yan Boko Haram din suka zo suka same ni a can, sai daya daga cikinsu ya ce, ‘ba kai ne muka kora daga wancan gidan ba?’ Me kake yi a nan kuma? Na shaida musu cewa ni nake gadin gidajen biyu. Domin dukkansu na mutum daya ne. Nan ma suka ce in bar wurin nan take na gudu,” inji shi.
Kamale ya ce a dai wannan dare ne wadansu ’yan Boko Haram suka fada gidan manajansa suka nemi kudi, “An gaya min cewa manajan ya ba su Naira miliyan daya da yake tare da su, amma ’yan Boko Haram din suka ce ba wannan kudi suke so ba, ya san kudin da suke so. Mutanen gidansu da suka ga yadda lamarin ya faru a daren sun ce maharan sun san manajana da dan uwansa domin da sunansu suke kiransu,” inji Kamale.
Ya ce: “An kuma shaida min sun kashe yayan a nan wurin take, sannan suka tafi da manajan zuwa gidan man inda suka tilasta shi ya fito da dukkan kudin ya ba su kafin su kashe shi. Ina zargin wadansu daga cikin yaran da suke gidan man nawa wadanda daga baya aka kashe wandasu daga cikinsu a wasu rikice-rikicen Boko Haram suna daga cikin wadanda suka kai hari tare da kashe manajan nawa.”
Kamale wanda ya ce ya fara harkar sayar da man fetur ne a jarkoki ta hanyar amfani da jakuna a iyakan Najeriya da Kamaru ya ce ya rasa dukkan dukiyarsa ga maharan inda hakan ya tilasta shi daina harkar man fetur.
“Bayan kwana uku da aukuwar lamarin daya daga cikin yaran da suke aiki a gidan man nawa da nake zargin dan Boko Haram ne an kashe shi a Damaturu da ke Jihar Yobe lokacin da Boko Haram suka kai hari. Yaron ya kira ni a waya ya ce in bar Maiduguri a ranar da karfe biyar na yamma. Ya gargade ni cewa akwai shirin kai min hari don kashe ni a wannan rana. Don haka na tattara suturana na bar Maiduguri a wancan rana na tafi Askira Uba ta hanyar Damaturu. A ranar an kira ni ta waya da daddare cewa ’yan Boko Haram sun mamaye gidana kuma sun banka wa gidajena biyu da motocina uku wuta sun tafi.”
Sai ya karkare da cewa: “Komai ya zama tarihi. Amma hakan ba yana nufin na fitar da rai ba ne, kuma tuni na sauya rayuwata zuwa sabon kalubalen da na samu kaina a ciki.”